Sashe 30
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ya shiga karanto min ƙauli da ba'adi, wa'azi na son zuciya, da hujjojin kare kai masu rauni, har jikina ya yi sanyi, na dinga kuka, ya ce"Assayyada kukan ya isa haka, yana da kyau ki nemi yafiyata, duk da dai ma idan ta ni ne na yafe miki, wallahi la ba'asa na yafe, to amma ya za ki yi da hakkin aure? Kin yi wa Allah laifi, ki nemi yafiyarsa, kuma dole sai ki nuna nadama shi ne kika tuba, bi ma'ana wato ainahin ki tabbatar da ainahin shi Annadamu ala ma fata, wato yin danasani a kan abin da ya wuce, to a nan sai ki yi tunani, ta ya za ki yi danasanin? A nan kuka ba shi da muhalli a lamarin danasaninki, ki miƙa wuya shi ne nadamarki, bi ma'ana ki yarda da ni mijinki kuma ki daina guduna a duk lokacin da na buƙace ki".
Haka na miƙa wuya ba ni da yadda zan yi, da irin wannan yake kashe min jiki ya yi ta cutata.
Wani lokacin sai na tsiri aiki na ƙi shigowa ɗakin, idan ya kira ni na ce aiki nake yi, nan ma da ya tisa ni a gaba da wa'azin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ko mace tana gasa gurasa ne mijinta ya neme ta ta katse ta ba shi hakkinsa, sai ya ɗora da faɗin idan kuma ban yarda ba ya yafe min sai na je na nemi yafiyar Allah don shi na yi wa laifi ba shi ba.
Na sha rufe masa ƙorafa na ce sai dai ya kwana a falo, amma kamar tsohon maye sai ya zo window ya dinga karanto min wa'azi mai razanarwa, da zabar wuta nau'i-nau'i, a dole nake buɗewa na yarda da shi, sai dai na yi ta gursheƙen kuka.
Da na ga abun yana neman wuce gona da iri, tun da gabana duk ya buɗe, na fara tusar gaba, abin da a baya ban taɓa yi ba, to yanzu na buɗe kuma tun da aka yi auren ban taɓa amfani da wani maganin matsi ba ko na ni'ima, ga shi kullum ƙafata a buɗe, don haka ban yi mamaki ba, kuma ba ni da niyyar neman maganin, saboda so nake ma ya ji rashin daɗi ko zai ɗaga min ƙafa, amma abu kamar ana ƙarawa zuma suga, sai na narke sosai na fara rashin lafiyar ƙarya, na kira Mama ina ta kuka na faɗa mata ba ni da lafiya sosai kamar zan mutu, sai ga ta a ranar ta zo gidan, da ta ga yadda na rame hankalinta ya tashi, dama duk sanda na je gida sai ta tambaye ni damuwata, sai na ce mata babu komai, duk don saboda kar ta ji halin da nake ciki ta faɗawa Baba, shi kuma ya yi zargin fitina ce kawai da rashin son zaman lafiya ya da na ce haka, to amma yanzu an kai magaryar tuƙewa, don haka na fashe da kuka ina faɗawa jikinta da faɗin"Mama don Allah ki tafi da ni, ba zan iya zaman auren nan ba mutuwa zan yi, zai kashe ni, rayuwata yake nema da ta ɗan cikina".
Hankalinta ya kara tashi, ta ce"Ban gane ba, me yake yi miki? Ciki ne da ke dama?"
Na nemi kunyata na rasa, na kwashe komai na faÉ—a mata, tuni ita ma ta fara kuka tana cewa"Sayyada ba ki da hankali za ki yi shiru ki zauna da miji irin wannan? Shikenan kin tashi daga aiki ya kashe ki, ya cuce ki".
Na ƙara ruɗewa na tsananta kukana.
Ta ce"Me yasa ba ki faÉ—awa kowa ba? Wannan fa cuta ce, bai halatta mai lafiya ta zauna da shi ba".
Na ce"Mama Baba nake tsoro, ina so na yi masa biyayya, ba na so ya ce na ƙi karɓar zaɓinsa, ya riga ya yarda da shi, ya ce duk wata fitina da za ta taso sai dai daga ɓangarena".
Mama ta dinga salati ta ce"Wannan wace irin ƙaddara ce?"
Na ce"Mama taimaka ki tafi da ni gida don Allah, marata ciwo take yi, ba na so na rasa cikin nan, idan na haihu sai na dawo ya kashe ni, ko babu komai na samu mai yi min addu'a da kuma abin da za a gani a tuna da ni ko bayan raina, don Allah Mama ki tafi da ni".
Mama ta yi shiru kamar mai tunani, kafin ta ce"Sayyada ina fargabar yadda Babanki zai É—auki batun nan, ki bari na fara tattaunawa da shi tukunna".
Ai kuwa na riƙe ta gam, na dinga rusa mata kuka, har ta yarda ta taya ni haɗa kaya muka tafi gida tare, a raina kuwa ayyanawa nake na bar gidan nan har abada.
[12/10, 3:53 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, KU YI MIN ADALCI KU BIYA NI HAKKINA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015
19
A daidaisahu ma sai kuka nake tana rarrashina, sanda muka ƙarasa gidan Baba ba ya nan, don haka nake ta fargabar dawowar tashi, can da na daidaici Ustazuna ya kusa dawowa cin abincin rana, sai na yi masa massage na ce masa ina gidanmu kuma na taho da mukullin, babu jimawa kuwa ya kira ni, na ɗauka, ya ce"Assalamu alaikum, Assayyada lafiya? Wane babban lamari ne ya faru da har kika fita ba tare da izinina ba?"
Na ce"Na gaji ne, ba ni da lafiya kuma na ga hakan bai dame ka ba, buƙatarka kawai ka sani, don haka ba zan iya ba, na gaji da aurenka".
Nan take ya fara jero"Subhanallah! Subhanallah, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".
Na kashe wayar, ya sake kira na ƙi ɗauka, ya yi min kira ya fi goma, ƙarshe ma na kashe wayata, ai ya san hanyar gidan namu ya zo ya karɓi mukullin ƙaddararren gidansa.
Bai zo ba da rana, sai can wajen magriba ya zo, ya aiko ana sallama da ni, don har lokacin ban kunna wayata ba, Mama ta leƙo ɗakin da nake a zaune ina nazari ta ce"Ina ga shi ne ya zo, ki leƙa ki ba shi mukullinsa".
Na ce"Mama don Allah ki kai masa, walla tsoro nake ji, gani nake kamar zai riƙe ni".
Ta ce"Ni za ki aika kai masa mukullin kenan? Kuma riƙe ki sai idan ke kika so".
Ta koma harkar gabanta, na tashi ina jin kamar zan rusa ihu, na saka hijjabi na É—auki mukullin na fita, a zaure na same shi yana ta shafa gemu, yana gani na ya taho ya ce"Assayyada lafiya? Me ya yi zafi haka?"
Na ce"Babu komai, ka karɓi mukullinka".
Ya ce"Subhanallah, shin kin manta da cewar duk matar da ta fita ba tare da izinin mijinta ba Mala'iku suna tsine mata a duk wani taku É—aya da za ta yi".
Takaici ya kama ni na ce"Ai a adaidaitasahun na zo ba takawa na yi da ƙafata ba".
Zai yi magana na katse shi da faÉ—in"Don Allah ka tafi, ni dai na gama aurenka haka".
Ya riƙo hijjabina yana cewa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ki dubi Allah Assayyada ki yi haƙuri, idan kika guje ni ya kike so na yi? Na ji zan sassauta kaɗan, zan rage in sha Allah".
Na fizge hijjabina na shiga gida, yana ta kirana muryar nan a make kamar an matse shi, ban ko juyo ba na shige gida.
Ustaz ya ƙi barin unguwar nan, bayan ya yi sallar magriba zama ya yi a ƙofar gida ya jira dawowar Baba, bayan sun gaisa Baba ya ce"Ya Sayyadar? Kuna zaune ƙalau ko?"
Ustaz ya sunkuyar da kai cikin jin kunya ya ce"Ai tana ciki, mun ɗan samu saɓani ne, shi ne ta taho gida ta ce ba za ta koma ba, duk da dai lamarin ba laifina ba ne amma na yafe mata Baba, a dai ba ta haƙuri ta zo mu tafi".
Abun ya bawa Baba mamaki, shi duk ya yi zaton Sayyada ta haƙura tana zaune da mijinta ƙalau, ashe ta ce bai isa ta bi umarninsa ba, nan take ransa ya ɓaci, ya ce"Malam Ashir tun yaushe kuke samun saɓani ba ka faɗa min ba?"
Ya sake sunne kai ya ce"Alal haƙiƙa Baba ba mu taɓa samun saɓani ba sai yanzu, shi ma kuma na san za mu sasanta ma, e ba sai kun shiga ba, bi ma'ana dai inda za a ba ni ita ta koma da komai zai wuce".
Baba ya ce"To mene ne ya haÉ—a ku?"
Ya ce"A'a fa Baba na yafe mata ni har zuciyata, tada zancen ma ba shi da daÉ—i".
Baba ya ce"Ina zuwa".
Ya shiga gidan ransa a ɓace yana ƙwala kiran Sayyada.
Ganina kwance a jikin Mama tana ba ni kunu a baki ina sha ya sa shi dakatawa, ya ce"Ke Sayyada me ya kawo ki gidan nan? Mene ne haka?"
Mama ta ce"Da farko ka fara kallonta ka gani".
Ta É—aga ni tana jijjiga ni, dayake akwai hasken wutar nefa tarr yake kallona, ta ce"Ka kalle ta da kyau a haka muka aurar da ita, ka kalli ramar da yarinyar nan ta yi, ka kalle ta sam ba ta da nutsuwa, ta firgice, wannan auren ban ga ranar shi ba, wannan ba miji ba ne, gaskiya a raba auren nan kawai".
Baba ya ce"Tambaya nake yi fa mene ne ya haÉ—a su? Me kika yi masa?"
Na ce"Baba ba komai, ba faÉ—a muka yi ba, ba ni da lafiya ne sosai shiyasa na taho gidan".
Ya ce"Yau ga shirmen banza saboda ba ki da lafiya sai ki taho gida? Kanki farau?"
Na ce"Baba jiri nake ina faÉ—uwa fa, kuma a haka zai saka ni girki da aikin gida dole".
Mama ta karɓi da faɗin"Shekarar yarinyar nan nawa da aure Allah bai ba ta haihuwa ba? Sai yanzu ta samu kuma sai a barta cikin bauta har cikin ya zube?"
Baba ya ce"Ke É—in wace irin wahala ce ba kya sha idan kina laulayi? Lalacin banza, wannan ya kai abin da zai sa ta kama hanya ta dawo gida babu izinin mijinta? To maza tashi ki bi shi".