Sashe 10
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsoro ya kama ni, zuciyata ta yi rauni na fara tunanin anya Sadam don gaskiya yake yi mini kuwa? Ban yarda da gaske yake ba, sai da daddare da Baba ya yi baƙi, bayan sun tafi ya zaunar da ni yake ce min iyayen Saddam ne suka zo, kuma sun nemi a ƙara masa watanni uku, don bai gama shiryawa ba, a ranar na ci kuka, haka na kira shi ina kuka, ni gani nake abun kunya ne 'yan'uwa da ƙawaye sun gana yin anko da shirin aurena kuma su ji an ɗaga saboda bai shirya, na kira shi na dinga yi masa kuka, shi kam ko a jikinsa, ƙarshe dai na ce na amince, ya ce ma ba ya so, sai kuma bayan kwana uku ya yarda muka haɗu, amma ya ce sam ba zai yiwu ya janye ɗagawar ba har sai ya ga gudun ruwana.
Tun daga lokacin muka jone a wannan sabgar, mun yi nisa sosai, bayan zuwana gidan na farko na sake zuwa sau uku, duk ranar da babu kowa a gidan sai ya kira ni na je gidan, mai gadi dai ya san da zuwana, amma ina tunanin ko tsoron tonawa Sadam asiri yake, ko kuma yana ba shi cin hanci ne, daga baya ma sai ya siya katifa ya saka a gidan shi, muke zuwa can, an gama ginin gidan komai tsaf, shi yasa nake mamakin dalilin da ya sa ba za a yi auren a wuce wajen ba.
Lokacin da auren ya rage saura wata ɗaya Saddam ya shigo min da babbar buƙatarsa, ya nuna yana buƙatar kusantata romance ya daina gamsar da shi kawai daurewa yake, kuka na saka masa da roƙon a bar wannan maganar, ya nuna min ba komai ba ne tun da dai aure za mu yi, dama abun nashi ne, don ya nema tun yanzu ba zai zama matsala ba, da na nuna ban yarda ba sai ya ce zai fasa auren ko kuma a ƙara ɗagawa, ni kuma a lokacin wallahi wata irin ƙaunarsa nake yi, ko ɗagawa ba na so a yi ballantana a kai ga fasawa, ga shi ni ma ya sabar min da romance ɗin, tsananin sha'awar shi tana neman kassara ni, shi yasa na matsu a yi auren.
Ban san da gaske yake ba sai da Baba ya kira ni a wani dare, ransa a ɓace yake tambayata abin da saurayina yake nufi, jikina ya fara rawa fa na ji wai jiya ya ce sai dai a ƙara ɗaga auren nan, a ƙara wata biyu ya zama saura wata uku a maimakon wata ɗaya, Baba ya ce ya gaji, idan bai shirya ba na watsar da shi na bawa wani dama a yi da shi, wallahi ranar tashin hankalin da na shiga Allah kaɗai ya sani, na ci kuka na gode Allah, na gaji da gorin da ake yi mini na wannan ɗage-ɗagen auren da ake yi, wasu har suna cewa kuɗin ne ba shi da shi, alhalin ni dai ban ga babu a tare da Sadam ba, maimakon na yi karatun ta nutsu na gane Sadam jikina yake so ba ni ba, amma ina, na kasa fahimta, sai nake ganin laifina ne da na ƙi bin umarninsa, don haka na amince da sharaɗin ba za a sake ɗaga auren ba, ya ce ya amince.
Na yi ƙaryar zuwa wani gidan, ranar muka haɗu a gidan shi, gabana yana ta faɗuwa, shi kuma Sadam yana ta rawar jiki da zumuɗin kasancewa da ni, irin wanda ango yake yi a daren farko, a ranar, a wannan gidan, wanda dai ya kasance gidan aurenmu a yanzu , a cikin ɗakin da yake nashi ne a yanzu, a kan ƙaramar katifa da filo guda ɗaya Sadam ya samu nasarar shiga hurumina, ya kawar da budurcina, ya mayar da ni cikakkiyar mace, na sha wahala daidai gwargwado, na ci kuka, haka ya mayar da ni gida wajen bayan isha'i, inda a ce Mama ta mayar da hankali sosai a gare ni za ta ga yadda tafiyata ta canza, duk da ina ta daurewa ina ƙoƙarin haɗe ƙafafuna, na kuma daure na ci abinci na yi sallah na kwanta, amma da safe na tashi fuskata a kumbure saboda kukan da na ci, idona sun jawur, ga shi na kasa haɗe ƙafata na yi tafiya kamar yadda na saba, da safen dai Mama tana ganina gabanta ya faɗi ta shiga tambayata mene ne ya same ni? Na ce mata ciwon kai nake yi da zazzaɓin, don kuwa da zazzaɓin na kwana, da yake lokacin sanyi ne, sai ta ce sanyi ya kama ni, shi ya kumbura min fuska, haka dai aka siyo min maganin zazzaɓi da ciwon kai na sha, na yi jinyata ni kaɗai, sai Sadam da yake yi mini sannu a waya sosai, tare da alƙawarin ba za a sake ɗaga aurenmu ba.
Sati É—aya da faruwar haka ya sake nemana, ya kalamance ni har na sake amincewa da shi muka haÉ—u, tun daga lokacin kuma shikenan, ya zamana duk sati sai ya neme ni sau biyu, ni ma yanzu abun har ya fara yi mini daÉ—i.
Na sakankance, muka saba da Sadam sosai kamar wasu ma'aurata, a haka har lokacin bikin ya sake zuwa, ya rage saura sati biyu, shiru ba a kawo lefe ba, ga shi a wannan karon Baba ya ce indai aka sake ɗagawa to ya zare hannunsa a lamarin auren gabaɗaya, kullum cikin fargaba nake, duk da na san dai ina bin shi a yadda ya ce, sanda aka shiga satin bikin aka yi masa zancen lefe, sai ya ce a yi masa haƙuri a ɗaga auren zuwa wata ɗaya, nan take Baba ya ce sai dai a fasa, Sadam ya ce ba fasawa ya yi ba, yana ta ba da haƙuri ya tafi, a daren nan na ci kuka, na dinga kiran wayarsa ba ya ɗauka.
Washegari tun safe Baba ya wakilta abokansa da yayansa ya ba da kuɗin auren da Sadam ya kawo a mayar da shi gidansu, abun mamaki da tashin hankali ne ya faru sanda suka ƙarasa gidan, domin iyayen Sadam uwa da uba cewa suka yi babu wanda ya san yana neman aure, ƙarshe dai na taƙaice muku labari Sadam iyayen bogi ya samu suka kawo masa kuɗin aure, ranar na ga tashin hankali, Baba ya fusata sosai, ya kira Sadam a kan ya zo ya karɓi kuɗinsa ya ƙi zuwa ya ce ya bar min, ban gama tsinkewa ba sai da ya yi mini massage ya ce na yi haƙuri mu haƙura da juna kawai, har ya ƙara da faɗin babana ba shi da kirki, shi kuma ba zai zauna a wulaƙanta shi ba, kiran duniyar nan ya ƙi ɗaukar waya, ni dai ranar a asibiti na kwana saboda zazzaɓi ne ya rufe ni ruf.
Sai da na yi kwana uku a asibiti aka sallame ni, da na dawo gida babu zazzaɓin amma fa an kasa samun kaina, gabaɗaya na rikice, Sadam ya daina ɗaukar wayata gabaɗaya, duk na rame na ƙare, abinci ma yafita kawai nake, abu biyu ne ya haɗar min, ga zafin rabuwa da shi, ga kuma tunanin na riga na ba shi kaina ya gama buɗe ni, me zai faru idan na auri wani ba shi ba? Idan ya tambaye ni game da yadda ya ji ni kamar bazawara me zan ce masa? Auren wanda ya lalata ni shi ne kawai mafitata, ko da kuwa zai sake ni a sati ɗaya, duk wanda ya sake aurena daga baya ai ya san dama sunana bazawara, bazawara kuwa kowa ya san hanya ce daga Kano har Maiduguri.
Kullum a kwance nake kamar ruwa, tun Mama tana kyarata da yi min faɗa a kan yadda na kasa mantawa da Sadam har ta daina, ta fara jana a jiki tana yi min nasiha da nuna min Allah zai kawo min wanda ya fi shi, amma inaa! Duk da haka na ƙi kwantar da hankalina, wallahi ban san abin da ya sakawa Mama zargina ba, kawai wataran sai ta zaunar da ni take tambayata ko dai Sadam ya taɓa sanina a 'ya mace? Ko na ba shi jikina? Na fara kuka ina girgiza mata kai alamar a'a, ba ta sake cewa kowa komai ba, sai washegari da safe ta ce na ɗauki hijjabina na fito, na ce"Mama ina za mu je?"
Ta ce"Siyar da ke zan yi".
Na ja bakina na yi shiru na saka hijjabin muka fita, muka shiga adaidaitasahun, ba mu tsaya a ko'ina ba sai asibiti, ban san bayanin da Mama ta yi musu ba, kawai dai na ga wata Nurse babbar mace ta kira ni, ta zaunar da ni take tambayata a tsanake wai lokacin da muke soyayya da saurayina wani abu ya taɓa shiga tsakaninmu ne? Na ce mata a'a, ta ce na faɗi tsakanina da Allah, na dinga hawaye har da rantsuwa ta, na ce wallahi babu komai, aka yi min gwajin ciki da na HIV, kowanne nagative, ta ce to na hau gado za ta duba ni, gabana ya yanke ya faɗi, na fara roƙonta kar a yi haka wallahi lafiya ƙalau nake, sai da ta ɓata rai sannan na saddaƙar na hau gadon bayan na cire pant ɗina na ajiye, da ta duba ba ta ce min komai ba, amma a gabana ta yiwa Mama bayanin ba daɗe da sanin namiji, a ranar na ci kuka, don kukan da Mama ta yi ya tada hankalina sosai, haka muka koma gida ni ina gursheƙen kukan nadama, ita tana share hawaye.
A wannan ranar dai na ga ta kaina, domin Baba bulala ya saka ya zane ni, da ƙyar aka ƙwace ni, kuma ya ce ya zare hannu a lamarina gabaɗaya, babu shi babu ni, cewa ya yi ma sai dai na bar masa gidansa, duk yadda aka ba shi haƙuri ƙin haƙura ya yi, sai gidan yayansa na tattara na koma wato mahaifin Anisa.