Sashe 44
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani wasai nake jina, na rabu da alaƙaiƙai auren Ustaz, auren ƙadddara, yanzu me ya rage min? Sai lissafin watannin iddata, abu ɗaya ne ya dame ni shi ne tsohuwar soyayyar Sadam da take taso min ta yi min tsaye a zuciya ta hana ni sukuni, na dinga tuna rayuwar da muka yi kafin aure da kuma bayan aure, a yanzu ko na tuna muguntar da ya yi min ba na jin haushinsa sosai, tun da sai yanzu nake ganin yadda ya nuna nadamarsa ya kuma so mu zauna, amma na bijire a lokacin, a raina na gama yanke idan na gama iddata babu wanda ya fi cancanta na aura sai Sadam, ni da kaina zan nemi soyayyarsa na kuma dage har sai na komawa aurensa a karo na biyu, duk da ina sane da furucin Baba a kan aurenmu da Sadam sai bayan ran shi. Wani lokacin ina yiwa Baba uzuri a kan tsanar Sadam da ya yi, tun da yana tuna yadda ya lalata masa 'yarsa ne, amma ban da abun Baba tun da na yafe ai ya kamata shi ma ya yafe, tun da Hausawa sun ce kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba.
Takarda na samu na rubuta ranar da aka yi sakin, ina ta lissafin daga lokacin da zan yi period na farko, sai dai me? Haka wata ya zo ya wuce ni, ban yi period ba, na ƙara kwana biyar a kai ina jiran zuwan shi amma shiru, abun ya fara ba ni tsoro, da na tuna wannan fyaɗen da Ustaz ya yi min ranar da na je kwasar kaya, na shiga fargabar ko dai na samu ciki? A sace na aika wata yarinya a maƙotanmu ta siyo min tsinken gwajin ciki, ina gwadawa ya nuna positive, sai na rasa me nake ji, farin ciki ko akasin haka? Da gaske nake son haihuwa ina so na ga jinina, amma ya makomar wannan ɗa ko 'yar da zan haifa? Shikenan sai ya taso ba a tsakanin uwa da ubansa ba? Ƙila ma Ustaz ya ce na ba shi ɗan shi, ko kuma na yi aure Sadam ya ce ba zai riƙe ɗan da ba na shi ba, jikina ya yi sanyi, amma ta wani fannin farinciki nake yi a raina.
Na kasa shiru a ranar sai da na sanarwa Mama ina da ciki, na yi zaton farin ciki za ta yi, amma sai na ga ta dafe ƙirji ta ce"Ciki? Sayyada kamar ya kina da ciki, ban gane ba, yaushe kika same shi?"
Na ce"Mama kafin auren ya mutu mana".
Ta ce"A iya sanina duk wannan jinyar da kika yi a asibiti ban ji an ce kina da ciki ba, kuma babu binciken da ba a yi ba a kanka, sannan daga asibiti nan aka wuto da ke, kuma a nan gidan kin yi period Sayyada, ta yaya za ki samu ciki?"
Gabana ya fara faÉ—uwa, na sunkuyar da kai, sai yanzu na ga wautata, shaf na manta da amsa wannan tambayar.
Ta daka min tsawa ta ce"Ta ya za ki samu ciki? Na wane ne?"
Na fara hawaye na ce"Wallahi Mama fyaÉ—e ya yi min".
Ta ce"Wane ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Na ce"Shi ne, wallahi nashi ne".
Mama ta ce"Shi wa?"
Na ce"A ranar da na je kwasar kayan nan, har na ce miki na faÉ—a a kwata, shi ne ya ritsa ni a gidan ya yi min".
Mama ta hau salati tana tafe hannu, ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Sayyada me kika yi kenan? Me kika ja wa kanki? To wallahi ban yarda da ke ba, ban yarda kwasar kaya kika je ba, kin je kawai kun haÉ—a baki da shi, don ubanki kina son shi me yasa kika yi shiru aka kashe miki aure?"
Na sake fashewa da kuka na ce"Wallahi Mama ba na son shi, na tsane shi, kawai ƙarfina ya fi, amma ni ban taɓa son shi ba".
Mama dai ba ta sake cewa komai ba, har na ƙaraci kukana, ƙarshe ma ta bar min ɗakin.
Kunya ta sa na kasa ko motsawa na bar ɗakin, haka za ta shigo ta yi abin da za ta yi ta fita duk ina zaune, sai kiran sallar azhar ne ya sa na fita daga ɗakin, na yi alwala sai na shiga ɗakina na yi sallah, Mama ta biyo ni ɗakin ta kawo min abinci, kaina a ƙasa, ta ajiye tana cewa"Gara ma ki saki jikinki, kin yi yadda kike so ai burinki ya cika, Allah Ya sauke ki lafiya".
Haka na dinga zaman ɗaki, ko fitowa taya ta aiki na kasa, har dare da Baba ya dawo, yana ƙwala min kira na ji zuciyata ta tsinke, don na tabbata Mama ta sanar da shi halin da nake ciki, na ji kamar na nitse a ƙasa a neme ni a rasa, haka na fita na shiga ɗakin da suke, kaina a ƙasa na ce"Baba sannu da zuwa".
Ya ce"Ke da gaske ciki ne da ke?"
Na gyaÉ—a masa kai alamar e.
Ya ce"Kuma kin tabbata na mijinki ne?"
Na ce"Wallahi Baba na shi ne".
Ya ce"Mene ne dalilinki na munafurtarmu kina gabanmu a cikin gidan nan ki ba shi dama ku keɓe? Kenan neman sasancin da yake zuwa ne har kuka samu wannan damar? Ashe kenan kina son shi mu ne muke yi miki yaƙi a banza ko?"
Na ce"A'a wallahi Baba, da na je kwasar kayana ne, ya tarfa ni a gidan".
Baba ya kalli Mama da neman ƙarin bayani.
Ta ce"E ta ce za ta je ta kwashe abubuwa ta masu muhimmanci a lokacin, sai na ce su tafi da Anisa, a ranar ne dai abun ya faru".
Nan Baba ya rufe Mama da faɗan me yasa za ta bar ta ta je ita kaɗai? Mama ta ba shi haƙuri, ya kalle ni ya ce"Yanzu shi mijin naki ya san kina da cikin?"
Na girgiza kai alamar a'a.
Ya ce"To idan Allah Ya kaimu gobe za ki je asibiti a sake tabbatarwa, daga nan sai na kira shi na sanar da shi, Allah Ya raba lafiya, rabo ne ya riga ya rantse".
Na tashi a sanyaye na bar ɗakin, na zauna ina shafa cikina da bai ma fara ɗagowa ba, tun yanzu ƙaunar abin da zan haifa ta shiga raina, sam ba na hango zaman haihuwa da rainon da zan yi a gida.
Washegari na shirya na tafi asibiti, niƙabi na saka na rufe fuskata, ina shiga harabar asibitin gabana ya tsinke ya faɗi, sakamakon ganin ƙaddarata, Sadam ne tafe yana amsa waya ya doshi motarsa zai shiga, bai buɗe ba, ya dai jingina a jikinta yana yin wayar, zuciyata ta tsaya cak da aiki, kafin bugun zuciyar ya canza, gabana ya dinga faɗuwa, wata irin ƙauna da kewarsa suka taso min, tsohon tsumin soyayyar shi na shekarun baya ya dawo sabo fil a zuciyata, ya ƙara ƙiba, jikinsa ya goge, duk da baƙi ne kuma ba kyakkyawa ba amma kana kallon fatarsa kana yana cikin kwanciyar hankali, daga inda nake ina jiyo ƙamshin turarensa, ganin bai gane ni ba, ya sa na ɗage niƙabin, ai kuwa muka yi ido huɗu, ya tsaya cak da wayar, kafin na ga ya katse kiran, ya mayar da wayar aljihu, ya tsaya yana kallona, sai na dinga taku ɗaya bayan ɗaya har na ƙarasa inda yake, ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Kin gama idda ne?"
Na ce"Dama ka san aurena ya mutu?"
Ya ce"Ina dai hasashen haka, na san kina gidanku".
Na ce"A ina ka sani?"
Ya ce"Lokacin da kika yi ciwon damuwar nan, matata tana cikin nurses É—in da suka kula da ke, a bakinta nake jin labarin".
Na ce"Amma ya aka yi ta san ni ce?"
Ya ce"Ai tun muna tare da ke na sha nuna mata hotonki, sannan ta san sunanki ma".
Na ce"Ta haihu ko?"
Ya ce"Ki je gida za mu yi waya anjima, Please ki É—auka idan na kira".
Na ce"To".
Ya shiga mota ya ja, na shiga asibitin ina waiwayen shi kamar wata doluwa.
[25/10, 9:37 pm] Sadiya Abdulrazak: 27
A raina kuwa mamaki nake yi ashe matar shi ta san ni, har ma tana kai masa rahotona? Ni kuwa ban santa ba, kuma zan so na santa, ana yi min gwajin jini aka tabbatar da ina da ciki, na san na wata ɗaya ne, don haka ban yi wahalar yin scanning ba, na koma gida zuciyata cike da kewar Sadam da son kafa sabuwar rayuwa da shi, a yadda na ga soyayyata da tausayi a idonsa na tabbata zai iya aurena, to amma zai iya jirana har na haihu? Kuma ina makomar yaron da zan haifa? Zan rabu da shi ne idan ya ce ba zai riƙe ni da ɗana ba, ko kuwa ma uban ɗan zai karɓe abunsa? Da wannan tunanin na koma gida, kaina har ya fara ciwo, Ustaz ya shammace ni, amma ta wani fannin ya taimake ni, tun da ya ba ni abin da nake nema, wato haihuwa.
Ina shiga gida Mama ta tambaye ni cikin ne? Na ce"Mama shi ne".
Ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Mamaki ya kama ni, na fara tunanin shin Mama ba ta so na haihu ne a rayuwata da ta tada hankalinta don na samu ciki ko kuwa?
Na ce"Mama wai me yasa kika damu?"
Ta ce"Ke ba ki damu ba ko?"
Na ce"E".
Ta ce"Sayyada na san kin ɗauki lokaci ba ki haihu ba, ga ƙannenki nan duk da yaransu, dole za ki so ki haihu, amma ban so kika samu ciki a wannan gaɓar ba, akwai yiyuwar mijinki ya mayar da ke, sannan idan ma haka ba ta faru ba to fa za ki yi doguwar idda, sai kin haihu kin yaye ɗan kafin ki yi wani auren, ban so ki yi wannan da ƙuruciyarki ba".
Na ce"Mama ko zan dawwama ban yi wani auren ba, indai na haihu to na gode Allah, kuma zancen kome babu shi har abada".
Ta ce"To shikenan, Allah Ya rufa asiri, Ya sauke ki lafiya".