Sashe 46
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Akwai wata yarinya da ta taɓa cewa tana son shi, ranar sun je sun yi wa'azi a wata walimar aure da aka yi a gidan su yarinyar, ta auren yayarta, shi ne ta karɓi lambarsa, suna gaisawa, har dai ta nuna tana son shi, shi ne yake ta hanya-hanya saboda 'yar masu kuɗi ce yana ganin kamar ba shi da halin da zai iya riƙe ta, har yanzu dai suna waya jifa-jifa, tun kafin ya auri Sayyada suke tare, yanzu sai ya ga me zai hana ya gwada sa'arsa? Don haka bayan rabuwarsu da Sayyada ya fara ƙarfafa firar tasu, har ma ya saka ranar da zai je, sai dai a wannan karon ya yanke duk wacce zai aura sai ya faɗa mata larurarsa, idan ba ta amince ba shikenan, Idan kuwa ta amince wallahi ba zai sake ta ba, sai ya more sadakinsa har da alakoro.
Ana cikin haka sai ga Baban Sayyada ya kira shi ya ce ya zo yana neman shi, ya cika da mamaki, gefen zuciyarsa kuwa farinciki yake yi yana fatan Allah Ya sa dai Assayyada ce ta fara kewarsa ta nemi a yi kome, har wanka ya sake yi, ya saka kaya masu kyau na ƙasan akwati, ya fesa turare ya kama hanya bayan sallar isha'i.
Baba ya yi masa iso har cikin tsakar gida, ina ɗaki ya ƙwala min kira bayan isowar Ustaz, na fito, ina kallon shi gabana ya faɗi, raina ya ɓaci, don dole na zauna na gaishe shi, na mayar da kaina ƙasa, suka gaisa da Baba, Ustaz ya ce"Ma sha Allah! Baba lya kira ni, Allah Ya sa dai kiran alkhairi ne".
Baba ya ce"Alkhairi ne in sha Allah!".
Ustaz ya fara hango tabbatar hasashensa, ya ce"To Alhamdulillah, ma sha Allah".
Baba ya ce"Malam Ashiru idan ba ka manta ba akwai ranar da Sayyada ta je É—iban kayanta a gidanka kafin auren nan ya mutu hakane?"
Ustaz ya ce"A ƙwarai hakane, don wannan rana ba zan manta da ita ba".
Baba ya ce"Shin wani abu ya shiga tsakaninku a ranar?"
Ustaz ya ce"Ƙwarai kuwa, haƙiƙa ta na ni haƙƙina a wannan ranar Alhamdulillah!".
Baba ya ce"Ma sha Allah! Allah mai yadda Ya so, to malam Ashiru a wannan haÉ—uwa taku Allah Ya yi ikonsa, rabo ya shiga tsakaninku, a yanzu haka Sayyada tana da cikin wata É—aya, an samu tabbaci daga asibiti".
Ustaz ya washe baki ya she"Allahu akhbar, Alhamdulillah, ma sha Allah! Allah mun gode maka".
Ya kalle ni ya ce"Assayyada kin ga ikon Allah ko? Kin ga ashe rabo ne ya kawo ki gidan a wannan sa'in ko? To Alhamdulillah yanzu ya ake ciki? Amm Baba ko za ka É—an ba mu waje?"
Baba ya tashi ya shiga É—aki, shi kuma ya matso kusa da ni, na yi saurin matsawa, ya ce"Assayyada ashe ke ce za ki kawo min jinina duniya? Alhamdulillah! Yanzu ya kenan?"
Na ɓata rai na ce"Na me kenan?"
Ya ce"Wai da na ga an samu rabo, sai nake tunanin ko za ki haƙura ki yafe min, sai ki dawo gare ni, bi ma'ana a yi kome, amma fa ba dole sai kina so".
Na ce"Ba na so, kuma ba zan so ba har abada".
Ya ce"To a gaskiya Assayyada ni ba zan yi miki dole ba, kar na je ki mace min a gida, to sai dai ga ki sani tun da kina da ɗana ko 'yata a cikinki haƙiƙa ba a rabu ba, bi ma'ana zan dinga zuwa kullum ina ganin lafiyar ɗana, idan ta kama ma za ki buɗe min cikin na ga yanayin kwanciyar, sannan kuma na kai hannu na shafa shi, tun da babu damar kai masa ita babbar ziyarar, bi ma'ana idan an je yaƙi an gama kashe arna shi ma na ciki akan kai masa ziyara ai, to yanzu a madadin haka, za ki buɗe min cikin ina shafawa, domin ya taso da jin ƙauna ta uba a zuciyarsa ba wai iya ɗuminki zai sani ba, sannan kuma bayan Allah Ya sauke ki lafiya kin yaye shi, zan keɓi ɗana, bi ma'ana ba zan bari ya taso a matsayin agola ba, ko kuma goyon kaka, duk macen da na samu ta yi mini adalci ta iya zama da ni da larurata, wannan ɗana ko 'ya rabonta ne, ina fatan dai la ba'asa ko?"
Na ce"Ciki dai ga shi an sanar maka ka san da shi, tun da fatar cikina za ka gani idan ka kalli cikin ba shi ba to wallahi ba zai yiwu na dinga buɗe maka ciki ba kai ba likita ba, zuwan naka ma ba shi da wani amfani, tun da idan na yi magana ba jin muryarsa za ka yi a cikin tawa ba, ba na ƙaunar ganinka, don Allah ka siyawa kanka mutunci kuma ka riƙe shi tun ban tattaka shi ba, idan na haihu na yaye sai a yi duk wacce za a yi".
Ya ce"To la ba'asa, shikenan Assayyada, na yafe miki, e wallahi idan don ta ni ne Ni ba baƙon zafi ba ne, na yafe miki, sai dai kuma ya za ki yi da hakkin raba uba da ɗa da kike ƙoƙarin ɗauka?"
Na tashi a fusace na ce"Na raba ɗin, wa'azin ƙarya kawai na son zuciya".
Na shige ɗaki na bar shi yana ta rafka salati kamar an yi masa mutuwa, ya leƙo ɗakin nawa ya ce"Shikenan Assayyadda, na gode sosai, sannu kin ji, sannu da dakon ciki, ina tausaya miki, ina fatan Allah Ya sauƙaƙa miki laulayi, sannan kullum zan dinga zuwa, kuma zan dinga taho miki da saƙo, bi ma'ana kayan ƙarin jini ingantattu".
Na yi banza da shi, ya ce"Assayada".
Na juyo na kalle shi.
Ya rage murya ya ce"Zan kwana da kewarki".
Na yi tsaki, ya wuce ya tafi.
08028966015
[26/10, 7:55 pm] Sadiya Abdulrazak: 28
Kafin na yi bacci sai da na kira Sadam, bai ɗauka ba, ban fasa kira ba, sai da na ga shigowar saƙon shi, ya rubuto min"Ina kusa da matata, kamar yadda yau kika gayyato tsohon mijinki gidanku, ya mayar da ke ko ba ku gama sasantawa ba?"
Duk sai na ruÉ—e, na tashi zaune, fargabar zargin da yake yi min ta danne kishin ce min da ya yi yana kusa da matarsa, na yi masa replay da faÉ—in"Wallahi ba abin da kake zato ba ne, Baba ne ya kira shi ya sanar da shi ina da ciki, bayan haka babu wata magana a tsakanina da shi, tun da É—ansa ne ka ga dole a faÉ—a masa ya san da cikin".
Ina ta jiran amsar shi shiru, raina duk ya ɓaci, na fara tunanin yana can maƙale da matarsa, haka na yi bacci cikin zulumi da ɓacin rai. Washegari da safe wajen ƙarfe takwas sai ga kiran shi, na ɗauka muka gaisa sama-sama ya ce"Me kike cewa jiya? Kika ce wai an sanar da shi zaman cikin ne?"
Na ce"E".
Ya ce"To kuma cikin da za a zubar mene ne ma amfanin a dinga wani tereren shi?"
Na ce"Ba terere ba ne, shi ai dole ya sani".
Ya ce"Da wannan damar zai yi amfani ai ya mayar da aurenku ko?"
Na ce"A'a fa, babu batun kome".
Ya ce"Dole za a yi shi nan gaba, ni hankalina ba zai taɓa kwanciya ba sai na ga kin gama iddarki, kuma tun da ga hanya mafi sauƙi da za ki gama idda me zai hana a bi kawai? Cikin nan fa yana fita kin gama idda, sai mu fara sanin inda muka dosa".
Na ce"Ni fa ina jin tsoron zubar da cikin ne, ɓari yana da ciwo, na yi har sau biyu, sannan na san yawan yin shi matsala ne, ina fargabar abin da zai biyo baya wallahi, kuma ina son haihuwa sosai".
Ya yi tsaki ya ce"Kawai ki ce kina son mijinki dai, kina so ki koma gidansa ki haihu a can, wannan shi ne".
Na ce"Wallahi ba haka ba ne".
Ya ce"Kin ga Sayyada ni ba yaro ba ne da za ki raina min hankali, ki je kawai ki haihu ki koma gidan mijinki Allah Ya raya Ya ba ku zaman lafiya".
Kafin na yi magana ya kashe wayar, na dinga kira ya ƙi ɗauka, haka na haƙura, na yi wunin ranar suƙuƙu da ni, ana sallame sallar Isha'i sai ga Ustaz yana sallama da ni, baƙinciki ya ƙara ƙume ni, Allah Ya taimake ni Baba yana nan, ya ce kar na fita bari ya ke ya ji da me ya zo.
Ustaz yana tsaye da ledarsa a hannu, ya duƙa ya gaida Baba, Baba ya amsa yana haɗe fuska ya ce"Malam Ashiru lafiya dai ko?"
Ustaz ya washe baki ya ce"Lafiya ƙalau Baba, dama na zo duba lafiyar ɗana ne".
Baba ya ce"Kamar ya? Dama kana da wani ɗa a cikin gidan nan ne ko dai ɓatan hanya ka yi?"
Ya ce"Baba É—aba da ke tare da Sayyada nake nufi fa".
Baba ya ce"Ka zo ganin É—an ko uwar É—an?"
Ustaz ya ce"To la ba'asa idan ma dukansu ne zan gansu".
Baba ya haɗe rai ya ce"Kai Malam Ashiru, tsaya ka saurare ni da kyau, ka fita idona na rufe, daga yau kar ka sake ƙafarka ta sake tako gidan nan da sunan zuwa wajen Sayyada, ba zai yiwu ba, kai ban da zuciyar musulunci ma ta sa mun yi maka afuwa har ka isa ka dinga sintirin zuwa gidana? To ka kiyaye ni, ɗan a hannunta yake ballantana ka ce ƙarba za ka yi? Kar na sake ganin ƙafarka a gidan nan daga yau, idan ta kama a neme ka zan kira ka, babu wata kulawa da za ka ba ta wacce za ta gagare mu".
Ustaz ya ce"To shikenan Baba, amma ni ma da na duba na ga har yanzu Sayyada a cikin iddata take, a ƙa'ida ma ni ne zan dinga ciyar da ita, to amma ganin ba za ku bari ba yasa ban yi wannan yunƙurin ba, sai kuma na ce to duk da haka ya kamata na yi wani huɓɓasa, bi ma'ana na dinga kawo mata abubuwan ƙarin jini kullum, kamar zogale hala da 'yar kankana tun da yanzu lokacinta ne, amma ya kake gani?"