← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 89

Sashe 24

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ajiye wayar na tashi na kwanta a ƙasan katifar inda yaran Anisa suke kwance, don a nufinta ni da ita mu kwana a katifar, a raina na ce'Kwana nawa ne ma na tafi gidan mijina?'

Washegari da safe ya turo min saƙon barka da safiya, da na duba sai na ga ya yi min miss call ƙarfe uku na dare, sai wajen ƙarfe goma ya kira ni, muka gaisa yake cewa"Allah Ya sa dai jiya da na kira ki ba ki ɗauka ba sallah kike yi a daidai lokacin".

Na ce"Gaskiya bacci nake, wayar ce a silent shiyasa ban ji ba".

Ya ce"Ya subhanallah! Assayyada Allah Ya sa dai ba kya cikin shagalallun da suke raya dare tun farko har ƙarshensa da bacci".

Na ce"Ina yin sallah, sai dai idan bacci ya ci ƙarfina".

Ya ce"Ma sha Allah! La ba'asa, ai kwanaki ya rage mu zama a tare, ko bacci ya yi miki nauyi kin ga kina da mai tunatar da ke".

Na ce"Na gode sosai, zan ji daÉ—in hakan".

Ya ce"La ba'asa, yanzu me kike yi? Ni dai yau da na tashi bayan komawa bacci wajen ƙarfe bakwai saura, sai na yi wanka, na karya da sauran abincin jiya da Inna ta ɗumama, na shirya na tafi kasuwa, yanzu haka ina kasuwa, shin Baba ya sanar da ke maƙota muke a kasuwa?"

Na ce"Bai sanar da ni ba, kenan a kasuwa ya sanka?"

Ya ce"Ƙwarai kuwa, ya san ni tun da daɗewa, kasancewar ni ne nake jan su sallah, Baba mutumin kirki ne mai dattako, Allah Ya saka masa da alkhairi".

Na ce"Amin Ya Allah".

Ganin zai sake kwaso zance na ce"Bari na je na yi aikin gida".

Ya ce"Na'am, la ba'asa, anjima za mu yi waya, amma ki yi haƙuri ba zan zo ba, saboda jiya bayan komawa ta gida na shiga wani yanayi, ke kuma na ga kamar idan na so ki ɗan rage min kewa ba za ki iya ba, duba da ganin yadda jiya kika saka hijjabi".

Na ce"E gaskiya ba zan iya ba, tun da kwanakin babu yawa, kamata ya yi mu yi haƙuri har mu tare".

Ya ce"To la ba'asa Ya Assayyada, Allah Ya ƙara mana haƙuri bakiɗaya".

Na amsa da Amin, muka ajiye wayar.

A ranar Mama ta kira ni da yamma, ta ba ni maganin sanyi da na ƙarin ni'ima ingantattu, na duƙufa sha ina amfani da su, kullum Malam Ashir zai kira ni sau biyu a rana, safe da dare, mun saba da shi babu laifi, kullum sai ya kira ni da daddare ƙarfe uku, idan na ɗaga sai ya ce na tashi na yi sallah, sai na tashi ɗin. Ana gobe zan tare aka je aka yi jeren kayana, a ranar kuma ya zo ya tambaye ni babu wata walima da zan yi? Na ce babu, iyayena mata dai za su yi wuni a aranar don mutane su shaida auren, ya ce"Ma sha Allah, idan na fahimta daidai kenan hakan yana nufin ba kya buƙatar komai dangane da ɗan kuɗi haka ko?"

Na ce"Ba na buƙatar komai".

Ya ce"To Alhamdulillah! Sai dai Allah Ya sa dai akwai 'yan kyawawan suturu da za ki dinga ado da su, dayake Baba ya ce ba sai na yi lefe ba, dubu ɗari kawai yake buƙata a matsayin sadaki, amma bisa adalcina in sha Allah bayan kin tare zan yi miki abin da ya sawwaƙa".

Na ce"Na gode sosai".

Ya ce"Alhamdulillah, yana da fa'ida ki san ita rayuwar duniya hudusun ce kuma fana'un, lahirarmu ya kamata mu gina ba ƙyale-ƙyalen duniya ba".

Na ce"Allah Ya sa mu dace".

Ya amsa da amin.

Daga nan muka taɓa fira, ya tafi.

Washegari aka yi wuni a gidanmu, ni dai babu wanda na gayyata, amma wasu daga cikin ƙawaye da suka kasance 'yan'uwa sun zo, na san duk Anisa ce ta gayyace su, bayan magriba Babana ya aiko na je, na je ya zaunar da ni ya dinga yi min nasiha, da faɗin kar ya ji wata ɓaraka daga wajena, ya yarda da Malam Ashir yana da tabbacin za mu zauna lafiya Indai ba ni ce na tsiro da fitina ba, zaren neman yafiyata na sarƙafe da wannan auren, idan na ja shi sannu a hankali zai yafe min, idan na ja shi da ƙarfi ya tsinke na huta, na dinga kuka ina faɗa masa zan yi biyayya da dukkan ƙarfina, Mama ma ta yi min nasiha da fatan alkhairi, a gidan na zauna bayan sallar isha'i malam Ashir ya zo da babur ɗinsa ya ɗauke ni, haka na ɗare bayan babur babu ɗan rakira, na ja hujjabina na rufe rabin fuskata, tun da muka fara tafiya wata kalma ba ta haɗa mu ba, sai tasbihi yake yi da hamdala, har muka ƙarasa ƙofar ƙaramin gidan nasa, ya tsaya yana cewa"Alhamdulillah, amaryata mun iso gidanki".

Na sauka daga babu ɗin, ya saka mukulli ya buɗe gidan, ya shigar da babur, na bi bayansa, ya faka shi daga gefe, ya koma ya saka sakata, ya zo yana ta hamdala ya buɗe ƙofar ɗakin duka biyu, ya ce"Bisimillah Assayyada, udkul bis salam".

Na yi bisimillah na saka ƙafata a cikin ɗakin, falo ne, na zauna a kujera gabana yana faɗuwa, jikina duk ya mutu, ya yi sallama ya shigo yana ta aikin murmushi, da leda a hannunsa, ni dai lokacin da ya ɗakko ni ban ganta ba, shi yasa na fi zaton yanzu ya ɗakko ta daga ɗakin gadon, ya ajiye ledar yana cewa "Assayyada yana da kyau mu fara gabatar da Sallah kafin komai, domin mu nuna godiya ga Allah da Ya sanya mu cikin zaɓaɓɓu cikin bayi wanda ya huwace mana mu keɓe kanmu mu raya sunna, domin mu hayayayyafa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa sallama ya yi alfahari da mu ranar gobe ƙiyama".

A raina na raya wannan mutumin ba dai surutu ba, yanzu faÉ—in tashi mu yi sallah ne ya kwaso dogon zancen nan?

Na amsa da to, sannan na tashi, na yi alwala shi ma ya yi, ya ja mu sallah a falon, bayan mun idar ya dinga kwararo mana addu'ar neman albarka a cikin aurenmu, sannan ya dafa kaina ya yi min addu'a, ya ce"Assayyada a gurguje ga leda nan sai ki É—auka ki buÉ—a ki ware kaza da lemo, sauran kuma abun karin kumallo ne, wanda za mu sarrafa shi da safe idan Allah ya sa muna cikin rayayyu kuma lafiyayyu".

Na ce"To".

Na ɗauki ledar na buɗe, na fito da kazar sai lemo coca cola jarka biyu, sauran kuma suga ne wanda ba zai wuce ƙullin naira ɗari ba, sai madara yar ta leda guda ɗaya da milo shi ma guda ɗaya, sai ganyen shayi guda ɗaya, wannan dai me guda biyu a cikinsa ɗin, sai wani matsolon biredi, wanda indai da iya shi kaɗai zan karya babu ƙwai ko indomi ba lallai na ƙoshi ba, ɗan ɗari uku ne, ɗari ukun zamanin Tunubu ba ta da ba, abun ya ba ni mamaki, amma na yi ƙoƙarin shanye mamakina, na tashi na kai kayan shayin kitchen, na adana, sannan na ɗauki faranti da kofina biyu, zan juye kazar ya karɓa yana murmushi ya ce"Yana da fa'ida a ce miji yana taya matarsa hidimar gida, ya juye ƙedararriyar kazar, daga gani 'yar Hausa ce ba wata babba ba, a raina na ce'Allah ga Sayyada'.

Ya rage kayan jikinsa ya zama daga shi sai singlet da boxer, sai yanzu na kara ganin ramar shi, kunya duk ta kama ni, ya ce"Amaryata ko da ba za ki rage kayan jikinki yanzu ba, zan so a ce kin zo kin zauna a nan cinyata".

Na ji kamar ba zan iya ba, da jikin Sadam kawai na saba, yau ga ƙaddara ta saka zan raɓi wannan busasshen mutumi, na ce"Umarni ne?"

Ya ce"Ƙwarai kuwa, a yanzu a ƙarƙashin ikona kike, duk wani abu da zan faɗa miki umarni ne, musamman ma a wannan dare mai albarka, haka na tashi na ajiye mayafina, na je na yi yadda yake so, yana cin kazar yana ba ni a baki, kaɗan na ci na ce na ƙoshi, na tashi na fita, ɗayan ɗakin na shiga na rage kayan jikinana fito na shiga wanka, na fito na same shi ɗaure da wani tsohon towel, amma fes yake babu ƙazanta, ya yi min murmushi ya ce"Hana habibiya, inda kin faɗa min za ki shiga wanka ne ai da mun shiga a tare ko? Cikin hakan akwai fa'ida".

Na yi murmushin yaƙe na ce"Gobe sai mu yi".

Da sauri ya ce"In sha Allah".

Ya zuba ruwan shi ma ya yi, lokacin da ya shigo É—akin na saka rigar bacci har na kwanta, tunani kawai nake yi, a yadda wannan mutumin yake rawar kai yana kiran kansa da sunan hariji yau ba zai saurara mini ba, hawaye ya siraro gefen idona, wai ina ji ina gani da yardata a yau wani ba Saddam ba zai shiga hurumina, rayuwa kenan.

Malam Ashir ya gama komai ya hayo gadon, tun kafin ya kai hannunsa jikina na ji yana karanto addu'ar saduwa da iyali, hakan ya ƙara bugun zuciyata.

Tun a ranar na fara zargin anya kuwa Sadam hariji ne? Domin a ya daɗe ya yi minti talatin, duk ranar da ya yi awa ɗaya to zarginsa nake na ce akwai abin da ya sha, kuma sosai yake tara min gajiya, amma wannan mutumin idan na lissafa daidai yanzu haka dai idan bai yi awa uku ba to ya yi biyu da rabi, na gaji duk kuwa da gyaran jikin da na yi, tun da nake da Sadam bai taɓa irin wannan daɗewar ba, ko sanda nake buduruwa ne kafin aurenmu, tun ina daurewa har na gajiya, da muryar kuka na ce"Malam bai isa ba ne?"

Yadda kuka san fa kurma nake magana, bai ma nuna ya ji ba sambatu kawai yake yi ya yi Hausa ya yi larabci, da na ga da gaske ba zai saurare ni ba na ture shi da ƙarfi ina faɗin"Na gaji fa!" Na sauke numfashin da nake jin kamar ya kusa ya fara min nisa.
Chapter 24 · 0% Book details