Sashe 89
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da alama dai mai martaba ya yi fushi da Hajiya Halima sosai, domin kuwa sai da ta yi wata biyar a gida, duk magiyar da take yi masa ya ƙi ba ta damar dawowa, da ta gaji da gashin da kanta ta sanarwa iyayenta laifin da ta yi masa, sam ba su goyi bayanta, don haka suka zubawa Isma'il ido ya yanke hukuncin da ya ga dama, ƙarshe Sayyada ta dinga kira tana roƙonta ta yi haƙuri, idan ta faɗa masa ta yafe mata ƙila zai yafe shi ma ya yi mata afuwa, idan Sayyada ta yi masa maganar ko ƙala ba ya cewa, ƙarshe ma sai ya gargaɗe ta a kan kar ta sake yi masa zancenta, ganin haka ya sa ita ma Sayyadar sai ta ga dama take ɗaukar wayar Hajiya Halima idan ta kira ta, idan ba ta so ba sai ta ƙi ɗauka, sai da ya mula ya mulmule sannan ya je ya dawo da ita, a gaban iyayenta ya yi gargaɗin idan ya sake kama ta da irin wannan neman fitinar komai zai iya faruwa, ta ce ta amince, sanda ta dawo cikin Sayyada watansa bakwai, da fari ta so shiga jikin Sayyada a ƙoƙarinta na nuna komai ya wuce yanzu za su zauna lafiya, amma Sayyada ba ta ba ta dama ba, saboda ta tafi a kan duk wanda ya ce ba ya sonka to ba zai taɓa sonka ba sai dai don wata manufa tashi, don haka take taka-tsan-tsan da ita, haka zamansu yake kadaran-kadahan, sai dai idan Abiy da Daddy sun shiga ɓangrenta ba ta hana su, kuma ta bi dangin Ismail duk ta nemi yafiyarsu, ta cigaba da shiga dangin idan sabga ta tashi za ta je a yi komai da ita, su ma kuma sun karɓu nadamarta, yanzu idan Sayyada za ta je gidan duk sati tare suke zuwa, duk da har yanzu ita ɗari-ɗari take yi, amma Hausawa sun ce motsi ya fi laɓewa.
Allah Ya sauki Sayyada lafiya, ta haifi 'yarta mace, ta ci sunan mahaifiyar Isma'il É—in ana ce mata Mimi, a wannan haihuwar Hajiya Halima ta shiga cikin mutane an yi taro da ita, duk da ba a san mene ne a zuciyarta ba.
SAYYADA
Soyayyar mijina kullum kamar linka min ita ake yi a zuciyata, ji nake kamar na fi kowa dacen miji, muna farantawa juna, ya so ya yakice sarautar shi amma inaa ya riga ya saba, wataran sai ya manta ya dinga yin magana da jam'un nan, ni ma idan na so tsokanar shi ina yi masa, ya biya mana mun je umara mu duka har Hajiya, aka bar yaran a gidanmu, amma mun tafi da Mimi, bayan mun dawo ya yi min alƙawarin idan na yaye Mimi kuma ban samu wani cikin ba ya yi min alƙawarin zan je aikin Hajji, sai dai kash! Kafin na yaye ta na samu wani cikin, nunawa da na yi ban ji daɗi ba kawai sai da muka kusa yin faɗa da shi, ba dama na ce zan yi hutun haihuwa sai ya ce na na son shi, ba na tausayin shi, so nake ya tsufa babu 'ya'ya, ƙarshe har da cewa zai auro wacce ba za ta gaji ba, idan ya ce haka sai na kwana ina fushi, saboda tsananin kishin shi da nake ji, tsoro nake wata ta zo ta raba ni da shi, ban je ba a shekarar, amma ya wanke min zuciyata, tun da ya biyawa iyayena sun je, haihuwa ta uku na haifi ɗa namiji, kuma a ranar ya yi min alƙawarin zan huta, ya cika alƙawin kuma, domin sai da na yaye ɗan, na je aikin hajjin da nake buri na dawo sannan na daina planing ɗin.
Yanzu ne na gane yadda ake yin tsantsar soyayya ba irin ta Saddam ba, wataran idan ina tunanin irin abubuwan da na yi a kan Saddam sai haushi ya kama ni, na wuni cikin ƙunci, na dinga tunanin to me ma na gani a jikinsa? Me ya ja hankalina har na aikata haka? Shi yasa kullum addu'a nake yi Allah Ya raba zuri'ataeda sharrin makauniyar soyayya, Allah Ya tsare musu mutuncinsu ba don halina ba. Isma'il ya saka yaran a makaranta mai kyau, sannan da daddare tare muke zama mu koya musu wani karatun, Hajiya Halima ma idan ta so tana zuwa a zauna da ita a falona a yi fira, zaman lafiya dai ya wanzu a gidan Masu martaba.
USTAZ
Yana dawowa daga tafiyar nan ya zaunar da Rauda da Rakiya suka tattauna, har zuciyarsa ya so ya saki Rakiya, amma da ya sanarwa mahaifiyarsa sai ta fashe da kuka ta ce so yake ya tona mata asiri ya tonawa kansa, tun da ita Rauda idan ta so islancinta haka nan ma za ta iya cewa sai ya sake ta, kuma gidansu babu kwaɓa babu harara, don haka Rakiya ce gatansa, kuma ko bayan ranta ba ta amince ya sake ta ba, ya ba ta haƙuri ya ce ya amince, amma dole ya saita gidansa.
Ya yi gyaran murya ya ce"Assalamu alaikum ya ku matana masu albarka".
Suka amsa sallamar.
Ya ce"To ku saurara ki ji ni da kyau, a gaskiya wannan lamarin na zamanmu akwai gyara a ciki, mu mutane ne, kuma ba don kashe arna Allah Ya halicce mu ba, saboda haka mu yi wa kanmu adalci, mu dinga abun nan saffa-saffa, a yi na Musulunci a haƙura da na kafirci, Allah Ya yi mu mu duka masu yawan buƙata, to Alhamdulillah mun gode masa, amma ke Rakiya ki sani ba fa abinci ba ne, yau ko abinci ai ana ƙoshi, duk jarabata ko sanda na yi auren saurayi bi ma'ana zamanin Maraƙisiyya ban kwana ina kashe arna ba, to don haka ki ajiye wannan ƙudurin naki a gefe, duk dare idan Allah Ya ba ni iko zan dinga biyawa duk wacce nake ɗakinta buƙata daidai gwargwado, bi ma'ana mastaɗa'a, za a yi bacci, sannan za a tashi a yi sallar dare, da asuba za a dinga haɗuwa a falon Rauda ina biya muku karatun Qur'ani da hadisai, da ɗan sanin da Allah Ya ba ni, duk wacce ta ga haka ya yi mata shikenan, wacce ta ji ba ta gamsu ba ta yi bayani ga biro da takarda yanzu na sallame ta".
Rauda ta ce"Na amince, Allah Ya sa mu dace".
Ya kalli Rakiya ya ce"Ke fa?"
A sanyaye ta ce"Shikenan, tun da ya zan yi?"
Ya ce"Ai babu dole, idan kina ganin za ki samu wanda ya fi ni ki faÉ—a a sallame ki".
Ta ce"A'a, Allah Ya ba mu zaman lafiya".
To daga nan gidan Ustaz ya hau kan saiti, aka daina ƙure kashe arna, kowacce yana ba ta hakkinta iya yadda zai iya, sannan wannan karatun na asuba sai ya kawo fahimtar juna tsakanin Rakiya da Rauda, dalili kuwa shi ne, ita Rauda kanta yana ja, ana yin karatun za ta ɗauke, saɓanin Rakiya da take shan wahala kafin ta iya, kuma Ustaz sai ya kafa musu wani sharaɗi, duk wacce ba ta yi karatun yadda yake ba to ranar kwananta zai zuge tazugensa, wannan kuwa shi ne babban tashin hankalin Rakiya, don haka idan ba ta iya ba sai ta je ta roƙi Rauda ta ƙara koya mata, gudun kar a bar mata arna a raye, da haka har suka saba ake yin fira, suka samu kusan lokaci ɗaya, Rakiya ce ta fara haifo ɗanta namiji, bayan sati biyu Rauda ta haifi mace, Ustaz ya roƙi alfarmar Isma'il kan yana so yaransa su saba da juna, domin yanzu Dawoud ne a gefe, don haka duk sati sai an kawo shi gidan Ustaz wani satin kuma shi Ustaz ɗin sai ya kai yaran nashi gidan Sayyada, ta haka ne Dawoud ya gane wane ne ainahin mahaifinsa.
Wannan shi ne ƙarshen yadda gidan Ustaz ya kasance, kuma shi ne ƙarshen labarin na duka.
*ABIN LURA*
Sunana labarin nan ku yi mana adalci ba ku yi min adalci ba, tun da aka yi jam'u za a fahimci adalcin ba mutum ɗaya ake neman a yi wa ba, da farko Sayyada ce take neman adalci a wajen Saddam, saboda ya lalata mata rayuwa kuma ta sadaukar ne saboda so, amma ƙarshe sai ya bayyana shi ba ma sonta yake yi ba, ba shi da niyyar aurenta. Adalci na biyu kuma iyayen Sayyada ne ba a yi wa ba, saboda sun bawa Sayyada tarbiyya daidai gwargwado amma sai ta yi fatali da wannan ta biyewa saurayi ta ɓata sunan gidansu. Daga baya ta yi nadama, adalci na uku shi ne ya kamata iyayen su yi mata uzuri su yafe mata, amma Baba ya ƙi yafe mata, wanda hakan ne ya sa ta faɗawa halaka a gidan Ustaz har ta kusa rasa rayuwarta. Adalci na huɗu shi ne, a lokacin da Saddam ya so su sasanta da Sayyada lokacin suna tare a kan rikicin hana ta haihuwar nan da ƙara aure da ya yi, Saddam ya yi nadamar azabtar da ita da gaske, ya so su samu maslaha, amma ta ƙi ƙarshe har ta nemi ta nakasa shi, wannan ma ba ta yi masa adalci ba. Sannan Ustaz da ya auri matan da masu irin larurar shi ba wannan ma rashin adalci ne, saboda akwai cutarwa a cikin lamarin, da Allah Ya halicci hariji sai ya halicci mace harija saboda a samu adalci ta kowace fuska. Adalci na gaba kuma Hajiya Halima ce ba ta yi wa Isma'il adalci ba, ya zauna da ita da larurarta, ko bayan ya yi aure ya haihu bai canza mata ba, bai yarda an ci zarafinta ba, amma sai take nuna baƙin ciki ga samun ƙaruwar shi, wannan ba ta yi masa adalci.
Da dai sauran abubuwa suna nan idan kun yi nazari za ku gano su.
Abin da na rubuta daidai Allah Ya haÉ—a mu a ladan, kuskuren da na yi Ya yafe min, Tammat bi hamdullah!
08028966015