← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 89

Sashe 7

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin a sallami Mama ya yi zuwa biyu asibitin, bayan an sallame ta kuma ya zo gida ya sake duba ta, nan fa ya riƙe ni sosai a waya, muka saba, amma har lokacin bai yi zancen yana sona ba, sai dai fira kawai kala-kala, har ta kai duniya fira da shi ta fi yi min daɗi sama da kowa, shiyasa kuwa idan bai kira kira ni sai na ji kamar ba ni da laka duk na rasa kuzarina, iyayena duk a zaton su soyayya muke yi, kamar yadda ni ma na yi zato, domin kuwa zuwa lokacin na kamu da soyayyar shi da ƙarfi kuwa, a zatona tun da yana ta nuna mini alamomin soyayya ai ba sai ya furta ba, akwai ƙawata da take faɗa min ita ma daga gaisuwar mutunci da firar duniya, ba ta san lokacin da suka faɗa soyayya ba, kawai sun wayo gari ne sun tsinci kansu a matsayin masoya, tsakanin ita da shi babu wanda ya yi zama na musamman ya yi wa ɗan'uwan shi bayanin na ga ni ina so, za mu fara soyayya, ga shi yanzu har sun yi aure, shi yasa na yi zaton ni ma haka ce za ta kasance mana ni da Sadam, don haka na ƙara zura jiki, saboda ni idan ina yin soyayya ina yinta da duka zuciyata da ƙarfina, haka ma idan ina ƙin mutum, akwai Ashiru, wani ɗan'uwan Babana da yake sona tun ina yarinya, ni kuma na tsane shi, da fari ya dage ya ce zai iya zama da ni ko ba na son shi, amma da na matse lamba wajen nuna masa ƙiyayyata tsirara a hankali na fita daga ransa ya janye da kansa

Mun riga mun saba da Sadam, kullum muna tare a waya, duk ranar Alhamis da Juma'a da ba mu da islamiyyar dare yake zuwa mu sha fira, ganin shi shi ne babban farincikina, shi yasa nake alla-alla ranakun zuwan nashi su zo, dangi kowa ya ji na samu wanda zan aura, ballantana kuma ƙawayena wanda yanzu ba ni da wata fira sai ta Sadam, mun yi wata shida tare da shi sannan na yi kammala secondary, kuma a bisa tsarin Baba dama 'yarsa mace tana yin Candy sai zancen aure, ko ɗar ba na ji, tun da na san ina da mijin da zan aura, sati na ɗaya da Candy Baba ya zaunar da ni da batun aure, ya tambaye ni akwai wanda nake so? Nan take na faɗa masa ina da Sadam.

Wata ranar Alhamis da Sadam ya zo, kafin na fita Baba ya tsare ya ce masa ya ba shi sati É—aya ya turo magabatansa idan da gaske yake, ya ce masa to.

Da na fito sai na ga fuskar Sadam a murtuke ba kamar yadda ya saba ba, hankalina ya tashi, saboda ni fa farincikinsa shi ne nawa a lokacin, na ce"Yaya Sadam, me ta faru na ga kana ɓata rai?"

Ya yi shiru kamar ba zai ce komai ba, kafin ya sauke numfashi ya kalle ni ya ce"Ke Sayyada!"

Na yi mamakin jin yadda ya danganta sunana da ke, sannan ya kaurara murya.

Na gama can jinin jikina ni na yi masa laifi, gabana sai faÉ—uwa yake yi, kamar zan yi kuka na ce"Na'am".

Ya ce"Mene ne alaƙata da ke?"

Wannan tambayar tasa sai ta saka ni a ruÉ—ani da fargaba, na ce"Yaya Sadam, ai ka fi ni sanin amsar wannan tambayar da ka yi mini, akwai wata matsala ne? Duk na rasa gane kanka".

Ya ce"Ina son jin amsar nan daga bakinki, saboda na lura yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke ni ba, mene ne alaƙata da ke? Ina nufin mene ne ya haɗa mu, me muke yi?"

Na sunkuyar da kai na ce"Mutunci ne ya haÉ—a mu, daga baya kuma muka jone muka zama É—aya, ina nufin soyayya muke yi ko?"

Ya ce"Tun da muke da ke na taɓa cewa ina sonki?"

Na ji kamar an rufto min wani abu a kaina, na ji kawai na fi kowa shiga muzanci a duniya, ga shi ba ya ko murmushi ballantana na yi tunanin wasa yake yi min, nan take idona ya tara ruwa suna dab da fara tsiyaya, shi kuwa ko a jikinsa ya sake maimaita"Na ce ina sonki ne? Dama soyayya muke yi?"

Na saki hawayen da rawar murya na ce"Dama ba ka sona Yaya Sadam, don Allah ba na son irin wannan wasan".

Ya ce"Ba wasa nake yi miki ba Sayyada, ni fa kawai na ɗauki alaƙarmu ne a matsayin abota da kuma girmama juna, ki yi haƙuri gaskiya ban taɓa jin son ki ba ballantana na yi tunanin zan aure ki, don haka ki sanarwa iyayenki ba soyayya muke yi ba tun wuri".

Daga haka ya shiga motarsa ya ja ya tafi ya bar ni tsaye kamar an shuka ni, na kasa ko motsi, zuciyata sai tiriri take yi, na ja ƙafa ina share hawayena na shiga gida, Allah ya taimake ni babu kowa a tsakar gidan, na faɗa ɗakinku na kwanta a katifa na fashe da kuka, ƙannaina suka shiga tambayata mene ne, na ce kaina ke ciwo, Mama ba ta yarda da ni ba, kuma tambayar duniya na ƙi faɗa mata, a wannan daren ban runtsa ba, ko da a ce zan iya haƙura da soyayyar Sadam to da wane kalaman zan sanarwa duniya silar rabuwarmu? Sai na ce dama ba sona yake ba ni ce nake haukana?

Washegari na tashi jiki ba ƙwari, dayake ranar Asabar ce na tafi Islamiyya ta safe, idan muka dawo ƙarfe ɗaya shikenan ba a komawa sai kuma ta dare, a makarantar ma yau ban tsinci komai ma, kifa kaina a benci kawai na yi na ce ba ni da lafiya. Ƙaramar magana da ta zama babba, ta tabbata Sadam da gaske yake ba wasa yake yi mini ba, tun da ga shi bai sake kirana ba har dare ya yi, na kasa jurewa na kira shi, sai ya kashe ya kira ni kamar yadda ya saba, na ɗauka da rawar murya, shi kuma muryarsa ba kamar yadda ya saba ba, sam babu walwala ya ce"Sayyada ya aka yi?"

Na ce"Don Allah idan wani laifin na yi maka ka sanar da ni".

Ya ce"Laifi ai ke ce kika yi min, a kan me za ki faÉ—awa mahaifinki soyayya muke yi, har ya tare ni da zancen ya ba ni sati É—aya na turo iyayena? Na ce ina sonki ne?"

Na fara kuka, na kasa cewa komai, zuciyata kamar za ta buɗe ƙirjina ta fito.

Ya sassauta murya ya ce"Sayyada".

Da ƙyar na ce"Na'am".

Ya ce"Sona kike?"

Na ce"Ka yi haƙuri idan na yi katsalandan a cikin rayuwarka, ba laifina ba ne, laifin zuciyata ne, kuma ni a nawa tunanin duk wani namiji da zai nunawa mace irin kulawar da kake ba ni sonta yake yi, shi yasa ma ban kwaɓi zuciyata ba, ashe na yi kuskuren fahimta, ina sonka Yaya Sadam, ina tsoron halin da zan shiga idan da gaske ba ka so na, don Allah mene ne aibuna?"

Ya sauke numfashi ya ce"Ba ki da wani aibu, kuma zan iya soyayya da ke wannan ba wani abu ba ne, sai dai ni gaskiya ina da sharuÉ—an da na tanadarwa duk wacce zan yi soyayya da ita kafin ma a kai ga auren, kina ganin za ki iya bi?"

Aka ce wanda yake ruwa idan aka miƙa masa takobi kamawa yake yi, a yanzu neman mafita nake yi, don haka na ce"Na amince".

Ya ce"To saboda muhimmancin maganar, mu bar wa gobe in sha Allah zan zo sai mu tattauna baki da baki".

Na ce"Allah Ya kai mu, na gode".

Ya ce"Ni ma na gode, ki yi bacci mai daÉ—i".

Zan iya cewa tun daga wannan ranar da Sadam ya karɓi soyayya rayuwarmu ta canza, rikiɗa ya yi ya koma kamar wanda ban san shi ba, kamar ba wannan wanda muka yi sabo muka zama abokan juna ba, sai ya yi ta sha min ƙamshi yana zuba izza, ni kuwa kullum soyayyarsa ƙara faɗi take yi da tsayi a zuciyata.

Dokokin da ya kafa mini su ne, duk wani umarni da ya ba ni ya zama dole na bi, aurena zai yi, don haka bin umarninsa a yanzu shi zai tabbatar masa da ya yi dacen mace, kuma bayan auren za ta iya bin umarninsa, akasin haka kuwa tana nuna ko an yi auren bai isa da ita ba, don haka babu batun ya auri wacce ba za ta yi masa biyayya ba, cikin biyayyar nan har da sharaÉ—in tambayar shi duk inda zan je, dole sai ya san shige da ficena, ko da kuwa iyayena ne suka aike ni, sannan yana da damar ya bar ni na fita, yana da damar hana ni idan ya ga fitar da zan yi ba ta dace ba, na ce na amince.

Sannan ya ce ba zan sake saka gyale ba, babu ni babu kwalliya sai dai idan zai zo zance, duka na amince, ya ce idan ya gan ni da wani saurayi ko ana gobe ɗaurin aurenmu ne ya fasa, na ce na amince, a haka muka gina soyayyar kuka ta fara tafiya sannu a hankali, ina ta ƙoƙarin bin dokokin nashi, sai da ta kai har Mama za ta aike ni idan na faɗa masa ya ce ba zan je ba, kuma ba zan je ba ɗin, sai dai na yi ƙaryar ba ni da lafiya saboda na kaucewa aiken, daga karshe ko unguwa na je shi zai ba ni lokacin da zan dawo gida, idan aka samu matsala na wuce ba ƙaramin ɓaci raina yake yi ba, sai na ta bin kansa kafin na samu ya yafe min mu shirya, shi yasa nake taka-tsan-tsan da duk abin da zai sa na karya dokarsa.

Tun a cikin satin da Baba ya yanka masa ya turo Iyayensa aka saka ranar aure watanni takwas, shiyasa yanzu duk dangi kowa ya tabbatar da shi zan aura.
Chapter 7 · 0% Book details