Sashe 78
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban ce komai ba, amma a raina na saka wallahi sai ya biya bashin wannan basar da ni É—in da yake yi, bari dai komai ya wuce na koma, zai gane ni ma da tawa sarautar.
Ganin mun É—auki wata hanyar ba gidanmu ba ya sa na tambaye shi ina za mu je?
Ya ce"Kin nuna min wannan tantirin tsohon mijin naki shi yake bibiyarki, to ba zan juri haka ba, shi ne nake so hukuma ta yi maku tsakani, tun da dai ba za mu É—auki doka a hannunmu ba ko?"
Duk da zan so hakan, amma sai da na ji gabana ya faÉ—i, na ce"Hakane".
Ya ce"Idan akwai wani abun da ya kamata na sani ki sanar da ni".
Na ce"E, sai dai maganar kuÉ—in haya".
Ya kalle ni da mamaki ya ce"Kamar ya kuÉ—in haya? Wane ne yake yi wa wani haya?"
Na ce"Dama shi ne ya ce ya bar min gidanmu da muka zauna a ciki, shi ne yake turo min kuÉ—in haya".
Ya ce"Ina takardun gidan?"
Na ce"Bai ba ni ba, suna wajen shi".
Ya ce"Bayan aurenmu ma ya turo miki?"
Na ce"E, ana gobe zai kira ni É—in ya turo min É—ari uku".
Ya yi min wata kafirar harara ya ce"Hmm, na gode Sayyada".
Na ce"Don Allah ka yi haƙuri, ai dama ina da niyyar mayar masa to ba ni da account number shi ne".
Ya ja dogon tsaki "Ya isa haka, ki rufe min marakunyar bakin nan naki, ɗari ukun banza! Hmm wannan ya nuna min har yanzu ba ki gama karɓa ta, kuma lokaci ya yi da zan kama kaina, don na yi iya yi na, dama tun da ba kya sona tun farko na san ba lallai ne ki yi min adalci ba".
Jikina ya yi sanyi, na fara hawaye.
Ya zaro tisue a gaban motar ya jefa min, kafin ya ce "Ni ba kuka na ce ki yi min ba, ban da rashin adalci Sayyada idan kina buƙatar kuɗin me yasa ba za ki tambaye ni ba? Kuma batun ya ba ki gida ƙarya yake yi, idan niyya ya yi ya bar miki ai zai ba ki takardun a hannunki kuma ki cigaba da karɓar kuɗin hayan, ba dole sai kun cigaba da connecting da shi ba, da haka ya yi zan yarda kyautatawa ce ta sa ya ba ki, kuma ba zan yi fushi ba, tun da ai ba wani abu ba ne don miji ya bawa matarsa gida kyauta a lokacin da suke tare, to amma shi na shi akwai manufa!!!" Ya ƙarasa da ƙarfi har yana buga steering motar.
Duk na firgita na ce"Ni dai ka yi haƙuri".
Ya ce"Ba zan yi ba, na ƙi haƙurin, kuma wallahi Sayyada sai kin sha wuya kafin ki samo kaina".
Murmushi ya ƙwace min, na guntse bakina bai gani ba, saboda tuna yadda daga gwada shi don na ƙuntatawa matarsa ya gigice, ballantana yanzu da nake shirin ɗana masa babban boom ɗin da zai rikita masa lissafi, amma ban sani ba ko dai zai jure da gaske. Muka yi shiru har muka ƙarasa bai sake magana ba.
KuÉ—i sun yi a rayuwa, har mamaki na yi yadda ake ta girmama shi kamar mai marbatan gaske, aka ba mu wajen zama, ya kalle ni ya ce"Saura a fito da shi ki dinga kallon shi, laifikanki yawa ne da su a wajena, don haka ki bi ni a hankali, ba ni wayarki".
Na miƙa masa bayan na buɗe, ya fara danne-dannen shi, na ce"Ni ma ai sai ka ni taka".
Ya harare ni bai ba ni ba ɗin, muna nan zaune aka kawo Sadam, to ido ba a yi masa shamaki don haka dole sai da na kalle shi, a kallon kuma na ga yadda duk ya rame, ko riga babu a jikinsa amma babu alamar an dake shi dai, ya zauna yana ɓata rai, na kau da kai daga kallon shi, ɗan sandan ya ce da Isma'il "Alhaji ga shi nan, mene ne a tsakaninku?"
Isma'il ya ce"Yallaɓai tambayar shi za ku yi a tsanake mene ne yasa yake bibiyar matata don ya kasance tsohon mijinta? Sun rabu babu ko ɗan tsako a tsakaninsu, yanzu ta yi aure a kan me zai cigaba da bibiyarta har yana tura mata kuɗi kamar wata almajira? Ga shi nan dai ya yi muku bayani da bakinsa".
Saddam ya yi shiru yana ta ɓata rai.
Ɗan sandan ya talli ƙeyarsa"Ka yi mana bayani, me yasa kake bibiyar matar aure?"
BuÉ—ar bakin Saddam sai cewa ya yi"So ne".
"Kai kafiri ne da ba ka san hukuncin son matar aure ba? Ko ba ka san laifi ba ne a doka?" Ya tambaye shi a tsawace
Babu alamar damuwa a tare da Saddam ya ce"Ai matata ce, kowa ya san Sayyada tawa ce, kawai don mun É—an samu hargitsi silar na yi aure shi ne har ya je ya aure ta, don haka ya sake ta kawai shi ne mafitarsa".
Tass! Aka wanke shi da mari, gabana sai faÉ—uwa yake yi, Isma'il ya tashi a fusace ya ce"Ku yi duk abin da ya dace, ku daina dukan shi".
Zai bar wajen, ɗan sandan ya dakatar da shi yana faɗin"Ka yi haƙuri Alhaji, dama don ka hana a dake shi ne, da ya yi laushi tun jiya yau ba zai samu damar faɗin haka ba".
Na kalli yadda yake kallon shi yana huci, shi kuma Saddam ƙasa yake kallo fuskar shi babu alamun nadama ko kaɗan".
ÆŠan sanda ya ce"Ka ba mu dama mu kwana uku tare da shi a nan, idan ya yi laushi ya dawo nutsuwarsa sai ka dawo a yi sasancin".
Isma'il ya ce"A'a a yi masa warning kawai".
Sadam ya ce"Kar a ƙyale ni, ka saka su kashe ni, mene ne amfanin rayuwata dama indai zan zauna ba tare da Sayyada ba? Na riga na sha gabanka, taƙamarka da kuɗinka na banza ne, tun da ba su ba ka budurcinta da soyayyarta ba, ko yanzu idan aka buɗe zuciyarta soyayyata kaɗai za a tarar a ciki, tana zaune ne da kai saboda na ƙi ta, ba don tana sonka ba, kuma yanzu ma ai kai rago ne ba jarumi ba, da sai ka ba ni dama mu fafata a shiga takara a ga wanda zai yi nasara da ni da kai, shashashan banza, har ka mutu ba za ka ji daɗin Sayyada kamar yadda na ji ba".
Ni dai daga nan na tashi na fice da sauri ina kuka, ganin yadda Isma'il yake wata tsuma jikinsa yana karkarwa.
ÆŠan sandan ya kai masa wani naushi a baki, nan take bakin ya fashe, Isma'il ya ce"Ku kulle shi, idan ya gaji da zaman sai ku faÉ—a min a yi maganar, ku ce ya ba da account number shi".
Saddam ya ce"Ba zan bayar ba! Ita ta ce maka ba ta da buƙatar kuɗin ne? Tun kafin ka santa nake ba ta tana karɓa, kai ba ka isa ka hana ni ba".
Isma'il ya jinjina kai ya fita daga wajen, ransa a matuƙar ɓace.
Ina tsaye a jikin motar ina kuka ya zo, ya buɗe ya shiga, ni ma na shiga, yana ta huci, ban taɓa ganin shi a irin wannan ɓacin ran ba, hannunsa yana karkarwa ya fara tuƙa motar, ga shi ban iya mota ba ballantana na karɓa na ja, tsoro duk ya kama ni na ce"Ko za ka bari sai ka dawo cikin nutsuwarka sai mu tafi?"
Ya yi min wani mugun kallo mai cike da gargaɗi, na ce"Don Allah ka yi haƙuri".
Bai kula ni ba har muka ƙarasa gida, ya ajiye ni, har ƙofar gida, ya ba ni wayata, na zauna na ƙi fita ina kallon shi, na ce"Ka yi haƙuri, na fi ka shiga damuwa".
"Ai dole ki ba ni haƙuri tun da wani ɗan iska kina ji ya yi min gorin karɓar budurcinki da kuma nuna ya fi ni saduwa da ke, da matata ce ta yi miki wannan gorin sai kin yi mata rashin kunya".
Na ce"To ya zan yi? Ai ba da son raina ba, idan ban ba ka haƙuri ba me zan ce maka?"
Ya ja tsaki ya ce"Fice min dalla!".
Na fita da sauri, sai dai zuciyata ta karye, kafin na shiga gidan kuka ya ƙwace min, Mama ta taso da sauri"Subhanallah! Sayyada, me ya faru? Ke da wa?"
Na ƙara ƙaimin kukan nawa na dinga yi, ta kunce goyon bayana ta saka shi a kafaɗa ta ce"Tambayar ki da nake me ya yi miki?"
Cikin kuka na ce"Saddam ne, Mama zai kashe min aure, wallahi idan auren nan ya mutu na haƙura da aure har abada". Na sake rushewa da kuka, na yi ɗaki a guje.
Mama ta rabu da ni, sai da na gama kukan sannan ta ritsa ni da tambayar me ya haɗa mu da Saddam ɗin? Na kwashe komai na faɗa mata, sai kuwa ta hau salati kafin ta rufe ni da faɗa tana faɗin ni ma da nawa munafurcin da kwaɗayi da son zuciya, ban da haka a kan me zan yarda ya ba ni gida har da karɓar kuɗin haya kuma duk ban faɗawa kowa ba, cikin kuka na ce"Mama a lokacin ina buƙatar kuɗin, ina gidan baban yaron nan babu abinci mai kyau, ba ni da lafiya ma ya ƙi kai ni asibiti shi ne na taɓa kuɗin".
Mama ta fusata"Kin faɗa mana ba ki da lafiya? Ko kin roƙe mu kuɗi ba mu ba ki iya ƙarfinmu ba?"
Na ce"A lokacin Baba yana kan ganiyar fushi da ni, idan na cika kawo cikas ɗin shi cewa zai yi fitina ta ɓullo daga gare ni, kuma zai ce ban yi masa biyayya ba ban karɓi auren ba, shi yasa na bar matsalar a cikina".
Ta ce"Duk da hakan, ai kin san ni zan fahimce ki, kuma wanda ya ba ki a karo na biyu fa? Wace matsuwar ce ta sa kika karɓa?"
Na ce"Wannan na yi laifi, kuma don muna tare ne a lokacin shiyasa na karɓa, tun da ai bai fi kyauta ba".
"Shi kuma na ukun nan fa? Da me mijinki ya rage ki? Ko kuma har yanzu kuna tare da shi kuma soyayyar?"