Sashe 52
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta gane tana cikin matsala ba sai da suka yi sati biyu a wannan halin babu canjin da aka ce za ta gani bayan sati ɗaya, abun ya fara ba ta tsoro, ya koma kasuwar shi, idan ya dawo kafin sallar magriba sai ya yi, ana sallar isha'i zai dawo ya ɗora, sannan ya yi na safe ko asuba, don taka masa burki ta yi ta ce na safen nan sai dai ya zaɓi ɗaya ko asuba ko safiya, shi ne yake yin ɗaya ya haƙura, saboda haka ta hana shi dawowa cin abincin rana, da safe take saka shi ya zuba a kula ya tafi da shi, don kafin ya tafi kasuwa zai yi girki safe da rana, ita kuma da yamma sai ta yi musu na dare, duk ba ta da nutsuwa saboda takurar nan tashi, ta gaji sosai, har ta daina marmarin abun, a yadda take yawan jin sha'awa kafin aure ta yi zaton abun ba zai gundure ta ba har abada, kawai tana son mijinta ne, ko ta ce ba za ta ba shi ba idan ya marairaice yana ta wa'azi yana kuma nuna shi ya yafe mata ma sai jikinta ya yi sanyi ta ba shi ko da za ta cutu, amma zuwa yanzu ta fara gajiya.
Da daddare suna zauna yana cin abinci take cewa"Kaji fa sun ƙara yau, gobe sai ka ƙaro ko guda goma ne, don yau ma pepper soup na yi niyya, to na san ga guda ɗaya ce kazar shi ne kawai na saka ta a miya".
Gaban Ustaz ya ba da rass, ya ƙware da shinkafar bakinsa ya fara tari, ta shiga yi masa sannu, ya miƙa masa ruwa, ya sha ya sauke numfashi, ya cigaba da cin abincin, ta ce"Kuma dankali da doya ma sun yi ƙasa, dama ka ga kai ne me cin doya, sai kayan shayi ina ga bai fi saura na gobe ba".
Ustaz ya yi shiru ya ma ɓata rai kamar ba ya jinta, ta ce"Sweetheart magana nake yi fa".
Bai kula ta ba, sai da ya gama cin abincin, ranta ya ɓaci ta juya masa baya tana danna wayarta, ya sha ruwa ya yi gyaran murya ya ce"Rauda shin manta yana daga laduban cin abinci idan ana ci a yi shiru ba a magana? Wannan ba halin mace ta gari ba ne a ce miji yana cin abinci tana kawo masa wasu ƙorafe-ƙorafe da uzururruka marasa dalili".
Ta ce"Ka yi haƙuri".
Ya ce"Ya wuce ai".
A ransa kuwa tunani yake yi shi ta ina zai ce zai iya siyayyar duk irin ta'adin abinci da ake yi a gidan nan? Gaskiya dole a canza zama, washegari da ya duba madarar ya ga tabbas a yadda suke shan shayi wannan yau za ta ƙare, shi kuwa bai shirya siya kayan shayi yau ba, sai ya haɗawa Rauda shayi da kansa, ya zuba kaɗan haka na shi ma ya zuba rabin cokali, tana lura da shi ta ce"Sweetheart ya dai yau na ga ka zuba madara kaɗan?"
Ya yi gyaran murya ya ce"Ina fa lafiya? Wannan madara da nake sha da yawa kwana biyu ita ce take tada min ulcer, to ban faɗa miki ba ne, jiya ina kasuwa ta taso min, sai da na je asibiti, na yi wa likita bayanin abubuwan da nake ji a jikina, ya ce ulcer ce ta ci ƙarfins, da tangaɗi fa ba ke asibiti jiyan nan".
Rauda ta ce"Subhanallah, amma shi ne ba ka faÉ—a min ba?"
Ya ce"Ai ba na son tada miki hankali ne, na san za ki shiga damuwa shiyasa, to likita ya ce na rage shan madara da milo sosai, sannan na rage shan suga, na daina cin doya, dankali, kaza, jan nama, ya ce duk kifi ya fi su amfani, shi ma ba sukumbiya ba, ko karfasa ko ƙawara, kin san shi karfasa ƙananu ne ba ma wata tsoka da za ki ji a jikinsa, musamman idan ya soyu, shi kuma ƙawara shi ne mai kwayoyin nan a jikinsa, amma ai ana taune su idan sun soyu, to wannan ƙayar akwai sirri a jikinta, wallahi ya ce ta fi wannan tsokar nama da muke ci, don haka dole za a canza tsarin gidan, don mu samu mu inganta lafiyarmu".
Rauda ta ce"Amma ni ai ba ni da ulcer".
Ya ce"To Rauda ai ba sai cuta ta kama ka mutum yake kiyaye sharuɗanta ba, kafin cutar ake ake yin riga-kafi ai, don haka ke ma ya zama dole ki kiyaye, daga yanzu kifi za a dinga ci a gidan nan, ƙawara ko karfasa".
Rauda ta ce"A'a gaskiya ba zai yiwu ba Sweetheart, saboda..."
Salatin da Ustaz ya rafka ne ya katse maganar da ta guntso, ya fara girgiza kai yana cewa"Subhanallah, wa iyazubillah, kaico, kaiconku ya ku matan wannan zamani masu rauni da biyewa ƙyallin duniya, kaicon macen da miji zai ce fari ta ce baƙi, kash, Rauda ban so kika kasance cikin irin waɗan nan matan ba, a ce miji yana faɗa kina musawa? Subhanallah, shin kin manta sai na ɗaga ƙafa za ki shiga aljanna? Tirr, amma kin yi min bazata, Rauda kin shammace ni".
Duk sai ta ruɗe, ita ba ta ga abun rashin kunya a maganarta ba, amma sai zuzutawa yake yi, dama ta lura babu wuya ya kai mutum wuta, kamar za ta yi kuka ta ce"Ka yi haƙuri".
Ustaz ya taɓe baki ya ce"A'a la ba'asa, ni kar ma ki damu, don idan ta ni ne na yafe miki, sai dai ya za ki yi da hakkin da Allah ya ratayawa mace a kan mijinta? Wannan tsakaninki da Allah ne".
Ta ce"Ka yi haƙuri kuma ni ba da wata manufar na faɗa ba, me ma na ce ne da zafi? Gaskiya ka zuzuta abun".
Ya ce"A haf! Rauda na yafe miki, sai kuma ki nemi yafiyar Allah".
Ya tashi ya tafi ɗaki yana ɓata rai, jikinta duk sai ya yi sanyi, yau ne rana ta farko da suka fara samun saɓani da Ustaz, ta gyara falon, ta bi shi ɗaki tana ta ba shi haƙuri, yana faɗa mata shi fa ya yafe mata, kawai yana taya ta jimami ne saboda fushin da Allah zai yi da ita a kan saɓawa miji".
Duk da ya yi na asuba sai ya so ya ƙara, ita kuwa ba ta jin za ta iya ba shi, don haka ta ɓata rai ta ce kanta ciwo yake yi, ya ce"A haf! Ashe dai ba za ki canza ba, ashe ba kya tsoracewa azabar Allah Rauda, shin kin san illar gujewa shimfiɗar miji kuwa?"
Ta ɓata rai ta ce"Har na haddace wannan wa'azin naka, idan haddar kake buƙata yanzu zan zayyano maka ita, amma wallahi ba za ka samu komai daga wajena ba a yanzu don ni ba inji ba ce, ba kuma jaka ba ce".
Ustaz Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya Allah ga matata nan Rauda, mai yawan saɓawa miji, Allah na yafe mata".
Ya ce"Rauda in don ta ni ne wallahi na yafe miki har zuciyata, sai dai ya za ki yi da azabar da Allah ya tanadarwa masu hali irin naki?"
Ta bar É—akin ba ta ce masa komai ba, halinsa na faÉ—a mata azabar Allah da tsinuwar mala'iku ya fara isarta fa, haka ya tashi ya shirya ya tafi kasuwa, wajen azhar ta kira shi a waya ta yi masa tunin kajin.
Ya ce"Subhanallah, wato kenan Rauda duk irin illolin da na faɗa miki a kan cin nama da kuma muhimmancin gujewa ƙyallin duniya a musulunce ba ki yarda ba ko?"
Ta ce"Na yarda mana, amma gaskiya ba zai yiwu lafiyata ƙalau na daina cin nama ba, Please ka aiko min ko ka kawo min".
Ya ce"To shikenan, da yake babu cash a jikina kuma na manta ban fita da ATM ba, bari sai na ci bashin ko guda É—aya ce, idan na dawo sai a siya ko?"
Ta ce"A'a bar shi kawai bari na fita na siyo".
Ya ce"Rauda bari ki fita kamar yaya? Dama haka ake fita babu izini? To kin san da cewar duk macen da ta fita babu izinin mijinta har ta je inda za ta je ta dawo duk taku É—aya da yake yi..."
Ta katse shi da faÉ—in"Mala'iku za su dinga tsine mata, ai na sani, kuma yanzu ba ga shi na tambaye ka ba?"
Ya ce"Subhanallah! Wannan É—aga murya da kika yi min na yafe miki, sai dai kuma ya za ki yi da faÉ—in Manzon Allah na cewar kar mace ta É—aga sautinta sama da na mijinta? Anya kuwa Rauda?"
Ta yi shiru, tana takaicin halin shi wani lokacin.
Ya ce"Wannan labari kike ba ni to ba neman izinin fita ba, tun da ai ce min kika yi za ki fita, mata da yawa suna yin wannan kuskuren, sai dai kawai mu ce Allah Ya shirya su, Ya sa mazajensu su dinga yafe musu, sai kuma su ji da fushin Allah wanda shi ne ma babban".
Ta ce"To ya ake neman izinin?"
Ya ce"Alhamdulillah kin dawo kan hanya kenan, cewa za ki yi ina neman izininka zan fita na siyo kaza, ni kuma sai na ce miki na amince miki ki fita ki siyo kaza cikin aminci ki dawo cikin aminci, to wannan shi ne asalin neman izini, gwada mu gani".
Ta ce"Ina neman izininka zan fita na siyo kaza"
Ya ce"Alhamdulillah, Rauda matata na amince miki ki fita ki siyo kaza cikin aminci, ki dawo cikin aminci".
Ta sauke numfashi ta ce"Na gode" Ta katse wayar a ranta tana ayyana iyayin shi ya yi yawa.
Ta ɗauki ATM ta fita, ta siyo kaji guda biyar, dankali da doya har da kayan shayin, ta duba duk wani abu da take buƙata ma ta ƙara siya, har lemula ta siya wanda za a ƙara a firji, mai adaidaitasahun ya kawo ta har kofar gida, ta dinga shiga da kayan, da Ustaz ya dawo ya gani ya yi ta farinciki, a ransa ya ce 'Ashe ma kina da kuɗin da kika noƙe'.