Sashe 19
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikinsa ya yi sanyi sosai, jin wai Sayyada tana kulle, ya lumshe ido yana godewa da Allah da ba ta kashe shi ba, yana jin shigowar Safna, amma ya yi kamar mai bacci, tun É—azu take ta zagin Sayyada da tsine mata, ya rasa yadda zai yi ta fahimci ba ya so, ya san inda a da ne da cewa za ta yi tsautsayi ne, don a baya kafin aurensu ba ta ganin laifin Sayyada, amma tun da aka yi auren ta canza wasu halayen nata.
SAYYADA
Na ci kuka sosai a wannan daren, na zubewar cikina, da safe aka sallame mu muka koma gida, aka ce a je gidana a kwaso min kayan sakawata, amma fir na ƙi, tun da na san abin da na aikata, sai kayan ƙanwar Anisa na saka da na yi wanka, na kwanta lamo kamar mara gata, wajen goma na safe sai ga shi Baba ya kira baban su Anisa, ya ɗauka ya tambaye shi ina gidansa? Ya ce ina nan, bai ce komai ba ya katse kiran, babu jimawa kuma aka fara sallama daga waje, shi ya fita ya duba, ganin 'yan sanda gabansa ya faɗi, suka ce sun zo tafiya da ni, ya tambaye su me na yi? Suka ce idan an je office ma ji, yana shigowa ya faɗa na fashe da kuka ina roƙon don Allah kar su bari a tafi da ni, Baba ya ce"Kin yi laifi ne?"
Na ce"E, na sokawa Sadam wuƙa a cinya, amma wallahi tsautsayi ne".
Duka gidan aka ɗauki salati ana sallalami, haka aka ja ni aka tafi da ni, ina ta gursheƙen kukan nadama. Ina ji ina ga i aka tura ni cikin sell, tsorona ma kar Baba ya ji ya ƙara linka fushinsa a kaina, wallahi da gaske na yi nadama, don ma dai ana ba ni abinci mai kyau, kuma ba a dake ni ba sai tsangwama da hantara, ga sauro a wajen ba na iya bacci mai daɗi, komai dai ba ya yi min daɗi, sai da na yi sati biyu a wannan halin sannan watarana aka fito da ni, aka faɗa min Sadam ya ce ya yafe min, tun da shi aka cuta kuma Iyayensa da suka kawo ƙarar sun ce ya yi yadda ya tsara shikenan za a sake ni, amma sai na je na ba shi haƙuri, yana gida yau an sallame shi, na ce to, jikina duk a mace.
Haka suka tisa ni a gaba har gidan Sadam, inda yake zaune da Safna, ban ma san inda gidan yake ba sai yanzu, a tare da ni akwai Baban Anisa, ko na ce babana a yanzu, shi ma jikinsa duk ya yi sanyi, kuma da alama ya a fushi da ni, domin ban gan shi ba sai yau, tun da aka rufe ni ba a bar kowa ya gan ni ba.
Ni ce ta farkon shiga falon, tun da tusa ni a gaba suka yi, ina shiga idona ya sauka a kan Sadam, dake zaune a falon yana waya, yana sanye da jallabiya, zuciyata ta buga, na shiga tunano irin cutar da ya yi min ba alkhairinsa ba, ɗaya daga cikin 'yan sandan ya daka min tsawa da faɗin"Ki durƙusa ki yi abin da ya kawo ki!".
Na lumshe ido hawaye ya sakko min, sannan na durƙusa ɗin kamar ɗalibi a gaban malami, tun da nake ban taɓa durƙusawa Saddam ba sai yau, suka shiga gaisawa da mutanen, ni kuma kaina a ƙasa, suka gama Baba ma ya ba shi haƙuri sosai, kafin falon ya yi shiru, wannan ɗan sandan me rawar kai da fala-falan kunne ya sake yi min tsawa kamar zai hau kaina ya ce"Ba za ki yi abin da ya kawo ki ba? Stupid!".
Sadam ya É—aga masa hannu alamar ya rabu da ni.
Jikina ya hau rawa, da muryar kuka na ce"Na yi kuskure, don Allah ka yi haƙuri ka yafe min".
Ya kalli mutanen falon ya ce"Ku É—an ba mu waje".
Duk suka fita, ya rage daga ni sai shi, ya zuba min ido yana kallona, kafin ya ce"Sayyada, da gaske za ki iya kashe ni inda ban sake ki ba?"
Na girgiza kai alamar a'a, na ce"Ka yi haƙuri don Allah, barazana ce, da kuma zugar zuciya".
Bai ce komai ba, kallona kawai yake yi, duk na tsargu kunya ta kama ni, ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Allah ne shaidata, na yafe miki ko da ba ki nemi yafiyata ba, amma kina da zuciya mai duhu Sayyada, ki yawaita addu'a Allah Ya raba ki da sharrin zuciyarki, Allah Ya sa ki fi ƙarfinta, domin da alama zuciyarki ta fi ƙarfinki".
Sai na rushe da kuka sosai, ya ce"Shikenan za ki iya tafiya, Allah Ya kyauta".
Na ci gaba da kukan ban ko motsa ba.
Ya ce"Sayyada akwai wata matsalar ne? Ko Baba bai karɓe ki ba?"
Na ce"Ai ni da kai mun san ba zai karɓe ni ba, amma ba wannan nake yi wa kuka ba, a ranar da abun ya faru na yi ɓari, ashe ina da ciki ban sani ba".
Shi ma ya ji zuciyarsa ta doka, ya ce"Ciki? Da gaske kin samu ciki kuma ya zube?"
Na jinjina kai ina cigaba da kukan na ce"Wallahi da na san ina da shi da na haƙura, da ban aikata komai ba, don Allah ka yafe min, mun rasa jininmu ta sanadina".
Ya sauke numfashi ya ce"Babu komai, haka Allah Ya tsara, kenan hakan yana nufin kin gama idda ko?"
Ban ba shi amsa ba.
Ya ce"Kin gama idda Sayyada, shikenan mun yi rabuwa ta gaske, Allah Ya ba ki kalar mijin da kike so, na yafe miki, ban sani ba ko za ki iya yafe min tarin cutarwar da na yi kiki?"
Na ce"Na yafe maka, ni dama fatana na yi nesa da kai, hakan ne kawai zai saka na manta".
Ya yi guntun murmushi ya ce"Shikenan, Allah Ya yafe mana bakiÉ—aya, za ki iya tafiya".
Na tashi na fara tafiya ina share hawayen rashin dalili, har na je ƙofa ya ce"Sayyada".
Na tsaya ban amsa ba, ban juyo ba, ya ce"Idan kina neman taimako ko na kuɗi ko wani abun za ki iya tuntuɓata kin ji?"
Na gyaÉ—a masa kai alamar na ji, na fita daga É—akin.
Su 'yan sandan shiga suka yi wajensa, ni kuma muka fice daga gidan ni da Baba, a adaidaitasahun ma yana ta yi min faɗa da nasiha, ina ta kuka da ba shi haƙuri, tun da yanzu shi ne gatana, idan ya yi fushi da ni ina zan kama?
Littafin nan na kuÉ—i ne a Kan Naira 700
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015
[05/10, 7:51 pm] Sadiya Abdulrazak: 13
Haka muka koma gida jikina a mace, nan na shiga roƙon Baba ina cewa"Don Allah Baba wannan abun da na yi wa Saddam ya zama sirrinmu, don Allah kar a bari Babana ya ji".
Baba ya ce"Ai ya ma riga ni ji, kuma wannan ya sake fusata shi sosai a kan lamarin, amma ni a shawarata duk da ya ce kar ki sake taka gidansa, to kar ki biye masa, duk ranar Juma'a za ki dinga zuwa ki gaishe shi ko ba zai amsa ba, zancen kayanki na gidan mijinki kuma za mu yi magana da mijin naki idan ya sake warwarewa sai a kwaso miki idan ajiyewa za a yi ga É—aki nan, idan siyarwa za a yi sai a siyar, tun da kin gama iddarki".
Na share hawaye na ce"To Baba, na gode".
A ranar da yamma sai ga Mama ta zo gidan, ita ma sosai ta nuna ɓacin ranta kan abin da na aikata, har ta zubar da hawaye, wanda ya sake sawa na ga tabbas na aikata laifi mai girma, ina kuka na ce"Mama ki yi haƙuri, don ki daina yi mini kuka, na yi kuskure, ku yafe min".
Ta ce"Sayyada kar ki saka na fara nadamar haihuwarki fa, wallahi ban taɓa tunanin ko ɓera za ki iya rutsawa ki cakawa wuƙa ba, sai ga shi kin aikata haka ga mijinki, Sadam yana sonki na sani, kawai na tsane shi ne saboda ina ganinki a cikin ƙunci, an yi ya fi dubu namiji ya lalata mace, idan aka tilasta ya aure t sai wulaƙanci da muzgunawa su biyo baya, shi yasa na yi zaton ke ma haka ne ya faru da ke, amma ba haka ba ne ke ce kika riƙe shi, yanzu ƙiyayyar har ta kai ki ɗauki wuƙa ko caka masa? Hmm shikenan tun da auren ya mutu, Allah Ya ba ki wani na gari".
Na girgiza kai na ce"Mama ni fa ba zan yi aure ba, na haƙura kawai".
Ta ce"Ai kuwa aure ya zama dole, sai dai idan ba ki samu wanda zai aure ki ba".
Ta shiga yi min nasiha, ta daɗe a gidan, sai bayan magriba ta tafi, ta bar ni da kewarta, da kewar gidanmu, da ɗakinmu, yau ba ni da damar zuwa gidan da aka haife ni na kwana duk silar Saddam, nan take na sake jin tsanarsa a zuciyata, da gaske na yi nadamar aikata masa wannan abun, amma har yanzu na tsane shi, kuma gani nake laifinsa ne, tun da shi ya ƙi sakina ai.
Haka na gyara zaman gidan Baba, Wanda nake jin a yanzu ya fi Babana sona, tun da shi ya yi min uzuri, nasiha ce kullum tsakanina da shi da shawarwari na ƙwarai, duk ranar Juma'a ina zuwa gidanmu na gaida su, kuma Baba yana amsawa, amma daga nan bai taɓa ce mini komai ba, na gode Allah ma da bai hana ni shiga gidan ba.