Sashe 66
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka rayuwar ta fara, tun da aka yi auren Rauda ba ta samu cikakkiyar nutsuwa ba, kuma a hakan ma bayan an gama cin amarci sai ya zamana ba kullum ake yi ba ma, idan an yi yau gobe babu, tun tana daurewa har ta fara nunawa, da ta ga za ta cuci kanta sai ta fara bayyana masa, idan ya gama samawa kansa nutsuwa sai ta ce bai ishe ta ba, sai dai duk yadda ya so ya koma second round ba ya iyawa, sai dai ya yi ta jagwalgwalata har ta É—an rage, ba don ta gamsu ba, a hankalin kuma ta fara sabar masa da ita fa kullum take so, tun yana daurewa yana biye mata, har ya fara nuna gajiyawarsa, tana ta tsiro da dabarun jan hankalinsa, ta yi shiga ta É—aukar hankali, amma wataran duk da haka dai ya ce mata yau a gajiye yake, ko kuma bacci yake yi, sai ta raba dare cikin takaici, akwai ranar da ta fara lalubar shi, ya janye hannunta yana cewa "Wai ke Rauda wace irin jarababbiya ce? Wallahi da buduruwa na aure ki da babu abin da zai hana ni zargin ba ta kaina kika fara sanin namiji ba, kai shi yasa ma auren wata bazawarar matsala ne, ke kuwa tsohon mijinki wane iri ne haka? Amma dai ya yi miki banzan sabo".
Maganar ta yi wa Rauda zafi sosai, daga ranar ba ta sake neman shi ba, idan ya neme ta shikenan idan bai nema ba ta haƙura, ƙarshe ma sai ta bar masa ɗakin, ta koma kwana da ɗanta, sai dai ranar da ya buƙace ta ya kira ta. Ai kuwa cikin lokaci ƙanƙani soyayyarsa ta dinga malalewa daga zuciyarta, musamman da yake nuna bai damu da ɗanta ba a fili, zuwa lokacin ta riga ta yi nadamar auren shi, ta fara tunanin da zai sake ta babu abin da zai hana ta komawa gidan Ustaz ko da ma zai yi mata kishiyar.
SAYYADA
Da lokacin da Baba ya É—ibar min ya yi, sai ya zaunar da ni cikin lumana yake ce min"Sayyada watanni uku cika cikin hukuncin Allah, an ba ki wayarki, sannan kina ta fita duk inda kika so, a cikin watannin nan kin haÉ—u da wanda kuka fara soyayya?"
Na ce"Baba ban haÉ—u da kowa ba".
Ya ce"To kina so a ƙara miki lokaci ne ko kuma za ki karɓi shi wannan mutumin da na dakatar da shi?"
Na ce"E ba shi dama Baba".
Ya ce"To shikenan Allah Ya yi miki albarka, zan sanar da shi in sha Allah".
Washegari sai ga kiran waya da baƙuwar lamba, na ɗauka muka gaisa ina son tuna inda na san muryar, ya ce"Kin gane ni kuwa? Isma'il ne, manemin aurenki".
Na ce"Ok".
Ya ce"Na karɓi lambarki ne dama, don na faɗa miki zan shigo yau, kuma mu dinga gaisawa ko?"
Na ce"Allah Ya kai mu".
Ya ce"Ok, to ya garin?"
Na ce"Ƙalau".
Ya ce"To sai na zo".
Ban amsa ba na katse kiran, na zauna jigum, ina tunanin yadda rayuwa take yi da ni. Da yamma ya zo kamar wancen lokacin, ya kira ni a waya ya ce yana ƙofar gida, na saka hijjabi na faɗawa Mama ya zo, ta ce"To sai kin dawo".
Na fita na same shi a tsaye, fuskar shi babu yabo babu fallasa, babu murmushi irin na wanda yake neman soyayya a wajen mace, na yi masa sallama, ya amsa, a wannan karon na gaishe shi, ya É—an É—age gira ya ce"Yau kin ga damar gaisuwar kenan?"
Ban ce komai ba.
Ya ce"Watanni uku ban gan ki ba, har na cire tsammani tun daga ranar da Baba ya ce ya dakatar da ni, na yi zaton ma kin samu wani ne, sai kuma jiya kwatsam ya kira ni, shin kin amince da auren ne ko kuwa dai kin yarda a yi duk da ba kya sona?"
Na kalle shi sosai, babba ne fa ba yaro ba, inda ya yi haihuwa wuri ko bai haifi kamata ba, zai haifi wacce ta kusa kai ni, amma yana abu irin na yara, yaran ma 'yan rainin hankali, kodayake ya same ni ne a araha dole ya dinga gadara.
Kamar zan yi shiru, sai kuma na ce"In sha Allahu na gama soyayya, na gama jin son wani har duniya ta naɗe, mutum ɗaya nake so, kuma shi ma soyayyar ta mutu, ba iya soyayyar ba, zuciyata ce ta mutu murus, don haka tambayata ina sonka ma ko kuma ƙoƙarin sakawa na so ka ɓatawa kai lokaci ne, zan aure ka, amma ba zan taɓa sonka ba".
Ya ce"Za ki dinga ziyarar shinfiɗata dai ko? Kuma za ki haifa min 'ya'ya, dama wannan kawai nake buƙata daga gare ki, matata tana yi min duka sauran, kuma ita tana sona, sannan albishiinki, ni ma har yanzu ban ji ina son wata mace bayan matata ba, kuma ba na tunanin zan so ki har abada!".
Tun da na ji ban ji zafin maganganun shi ba, na tabbatar da gaske zuciyata ta mutu ta fannin duniyar soyayya, tun da Sadam ya nuna ba ni da sauran daraja a idonsa kuma na jure to wane ne zai nuna min ƙiyayya na yi mamaki".
Na ce"Ya tabbata auren manufa kake so ka yi da ni, ni kuma zan yi ƙoƙari sosai a zuciyata na kau da hakan, zan saka a raina ni auren biyayya zan yi, domin faranta ran iyayena da suka duba cancantarka suka kawo min kai, ba zan tula musu ƙasa a ido ba, sai dai idan ka zalunce su Allah Ya saka musu".
Ya yi 'yar dariya ya ce"Ki kwantar da hankalinki Sayyada, yanzu yaushe ya dace a bar ranar auren? Ni idan son samuna ne a saka sati biyu ma".
Na ce"Ka tattauna da iyayena ko yau suka ce a É—aura a shirye nake".
Ya ce"Ok, ki je gida ki kwantar da hankalinki".
Na shiga gida, duk yadda na so na manta da kalamansa sai na kasa, ina ta tunanin sabuwar rayuwar da zan shiga, ko me zan tarar? Amma sam hakan bai sa na ji cewar wai zan bijirewa auren nashi ba.
Bayan kwana biyu Baba ya ce min sun yi magana daAlhaji Isma'il ya ce yana so a saka rana sati biyu, ya nake gani? Na ce"Baba duk yadda ka yanke ya yi".
Baba ya yi shiru yana kallona, kamar dai wanda yake son gano wani abu a tare da ni, kuma na san hakan ba ya rasa nasaba da wannan canjin nawa na lokaci É—aya.
Ya ce"Sayyada me yasa duk kika canza ne? Miƙa wuyan naki da biyayya kamar ya so ya yi yawa, kar fa mu shiga hakkinki".
Mama ta ce"Ni tsorona ma ko wani shirin take yi".
Na ce"Wallahi ba na shirya komai sai alkhairi, kawai Allah ne Ya shirye ni, kuma in sha Allah daga yanzu zan dinga yi muku biyayya, zan zauna lafiya da duk wanda kuka zaɓa min". Na ƙarasa maganar muryata tana rawa.
Baba ya ce"To shikenan, a dai bar shi a wata É—aya, gobe za su zo da kuÉ—in aure, zan sanar da su a saka wata É—aya, ai kamar yau ne, sannan mun yi magana da shi a kan É—anki, ya ce yana so ki tafi da shi, saboda yana son yara sosai".
Na ce"To na gode".
Mama ta ce"Tun da an yaye shi ai da an bar shi a nan wajena".
Baba ya ce"Tun da shi ya nema a ba shi É—in".
Aka shiga shirin biki, ya ba da kuÉ—in aure miliyan É—aya, na ciro kuÉ—in account É—ina duka na bawa Mama na ce a yi min abin da ya dace, Mama ta ritsa Ni da tambaya a kan inda na samu kuÉ—in, na faÉ—a mata wanda Saddam yake ba ni ne tun muna tare, ta ce"Yanzu saura nawa a account É—inki?"
Na ce"Duka ne na ciro babu komai a account É—in".
Ta ce"Ok" A ranta kuma tana ayyana za ta gani idan tsohon kuɗi ko sabo yake ƙara ba ni.
Duk sati yake zuwa zance, wanda ba na tsintar komai sai takaici, tun da gadara kawai yake zubawa da kalamai masu kaushi, amma bana nuna masa ɓacin raina, haka har ranar auren ta zo, na ɗinka kaya kala-kala masu kyau da tsada, komai na siya na lefe, akwati ne kawai ban siya ba, kayan ɗaki kuwa ya ce ya yi min, sannan ba ya buƙatar gara, don haka na siya kayan kitchen masu kyau, ƙannaina kuwa su suka dinga kawo min maganin gyara jiki, wanda ni ya dace a ce na kai musu, ina sha ne kawai saboda na kare mutuncina, ba wai don son na birge shi ba, don har yanzu ba na jin wata sha'awa tun aurena da Ustaz ya kashe min ita murus.
Waɗanda suka je gidana suka gani suna ta yabawa, ni dai ina ta tunanin sabuwar rayuwar da zan fara, fara ce ko baƙa? Allah masani, na dai saka a raina zan zauna da shi da zuciya ɗaya, na kuma yi masa biyayya daidai gwargwado.
08028066015
[09/11, 8:35 pm] Sadiya Abdulrazak: 40
Da daddare na fito daga wanka a sanyaye, tsirarun 'yan'uwana dake ɗakin suna ta azalzalata saboda sai da motocin ɗaukar tawa suka zo ma na tsiri yin wankan, duk cikinsu Anisa ta fi ba ni haushi, ita ke ta waya da mijinta tun ɗazu, don yana cikin masu ɗaukar amaryar, tana ce masa ga ni nan zuwa a yi haƙuri, a tsanake nake yin komai kamar wata wahainiya, zuciyata babu yabo babu fallasa tamkar yadda fuskata take, ba na cikin farinciki, kuma ba baƙinciki nake yi ba, daidai lokacin da na ɗauki sarƙa ina sakawa a tsanake Anisa cikin fusata ta ce"Haba don Allah Sayyada, kin san mutane nawa ne suke jiranki a nan? Wulaƙanci dai ba shi da daɗi".
Na yi mata mugun kallo na ce"Duk wanda ya ga ba zai iya jira ba ya tafi mana, uban wa na gayyata a masu jiran nawa? Ki zaɓi wata cikin ɗakin nan ki lulluɓa mata mayafi ki kai masa mana, kin ga sai ki warware nawa auren ki saka ya sake ni".