← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da ya fita sallar isha'i kafin ya dawo na juye sauran taliyar da ba su cinye ba, na cinye, da ya dawo muka ci sauran shinkafar rana, ya ce na ɗakko Qu'ani, na ɗakko ya tambaye ni inda na tsaya, na faɗa masa na yi sauka, amma ta biye ce, ya ce to za mu fara hadda, kullum zai dinga ɗora min aya biyar, muka fara daga Suratul baƙara, ba mu tashi ba sai da na haddace, sannan ya shiga wanka, yana fitowa ni ma na shiga, kafin na fito ya yi shirin bacci, wallahi har fargabar kwanciya a gadon nake yi, haka dai na kwanta ina saddaƙarwa, ya ce "Assayyada akwai azumin gobe Litinin sai ki ɗaura niyya".

Na yi shiru saboda tsakani da Allah ni dai ba na yi, kuma ban yi niyya ba.

Ya ce"Dama akwai indomin nan É—aya da rabi ko? Sai mu yi sahur da ita, kin san akwai albarka a cikin sahur".

Na ce"Amma ni fa ba na yin azumin Litinin da Alhamis"

Ya ce"Me yasa?"

Na ce"Kawai, ai niyya ne, ba dole ba ne".

Ya ce"Amma ai sunna ne Assayyada".

Nan ya tisa ni a gaba da wa'azi tare da kwaɗaitarwa a kan ladan dake cikinsa, har sai da na amince zan dinga yi, sannan ya janyoni ya shiga sana'arsa, tun ina daurewa har na fara roƙonsa, yana ba ni haƙuri da cewar gobe babu na safe babu na rana don haka yana da fa'ida yanzu a yi nisan zango, wallahi ustaz dai sai da ya ga na fara jan numfashi kamar zan fita a hayyacina sannan ya ƙyale ni, ya shiga jero min godiya yana cewa"Da a ce za a hasko miki ɗumbin ladan da muka samu a yanzu da kin ce a koma fagen fama, na faɗa miki tamkar fa an jere arna guda saba'in ne, yanzu a nan anya kuwa mun kashe guda goma? Idan a zahiri ne aka ba ki bindiga ai sai inda ƙarfinki ya ƙare, to da haka za ki dinga hasashowa sai kin fi ba ni haɗin kai".

Ina kuka na ce"Idan ba ka kashe arna ba ai za ka kashe mumina, a gaskiya idan aka cigaba da tafiya a haka zan cutu".

Ya ce"Yi haƙuri daure Assayyada ba za ki cutu ba da yardar Allah".

Da ƙyar na dafa ruwan zafi na shiga ciki, na ɗan samu sauƙi, na kwanta, da ya tashe ni sallar dare na ƙi tashi, na ce kaina ciwo yake yi, ya zo ya yi min kamun kai, yana ta yi min sannu, ƙalau nake kawai bacci ne a idona, ga jikina duk tsami, sai shi ya dafa indomin ina ji yana ci bai tashe ni ba, sai da lokacin sallah ya yi ya tashe ni, ya ce na tashi yanzu za a kira sallah, azumin kuma na haƙura tun da ba ni da lafiya, ya tafi masallaci.

Wani abun murna da farinciki ina zuwa banÉ—aki don yin fitsari na ga period É—ina ya zo, farin ciki ya mamaye ni, ko banza zan huta na kwanaki uku, sai na ga yadda zai yi da jarabarsa ai.

Yana dawowa daga masallaci na faɗa masa zuwan baƙon nawa, ya ce"Subhanallah!".

Ya ce"Dama idan ana azumi irin wannan sai dai a raba É—aki, ni bari na je daga falo".

Ya tafi falo ni kuwa na koma baccina.

Sai da gari ya yi haske, ya fita ya siyo min biredi da suga na Naira ɗari, sai madara guda ɗaya babu milo, kafin ya fita na ce masa ina son shiga maƙota a gaisa, ya ce"Amma tun yanzu? Kin ga fa ban fiya son wannan shige-shigen ba, ba shi da wata fa'ida, na dai fi gane idan kin ji wani abu ya fara, haihuwa, biki, rashin lafiya sai ki shiga".

Na ce"To".

Ya ce"Amma dai ki shiga É—in, kar ki daÉ—e".

Na ce"Me za a dafa?"

Ya ce"To kin ga ba don ba kya azumi ba ai da shinkafa gwangwani É—aya da rabi ma ta ishe mu, amma yanzu dole lissafin ya canza".

Ya yi jim kafin ya ce"Ba za ki iya cinye rabin taliya ba, To ina ga ki raba taliya gida uku sai ki dafa kashi É—aya ki ci, da daddaren kuma sai ki dafa mana shinkafa gwangwani É—aya da rabi ko?"

Nan ce"To".

Sai bayan ya fita na shiga kitchen É—in, sai na ga indomi É—aya ya dafa ya bar rabin, kuma ya cinye ta tass, na É—akko tawa na dafa guda É—aya, na tafasa shayin na sha da biredi sannan na ci indomin.

Wajen ƙarfe goma na ɗauki ATM ɗina na fita, na fara shiga maƙota muka gaisa, yawanci duk manya ne, wacce na ga kamar sa'ata ce ita na tsaya muka yi fira , har nake yi mata ƙorafin rashin shigiwarsu, tun da su ya kamata su fara shigowa kafin ni, ta ce"Hmm, ai gidan naku ne ba koda yaushe ake shiga ba".

Na ce"Ban gane ba".

Ta ce"A'a, da na ga rufewa kike yi ne dai, shi yasa na ce haka".

A yadda na lura da magana a bakinta, kawai dai ba ta don faɗa mini ne, na yi mata sallama na tafi, wajen me P.o.s na je na ƙwalulo kuɗin cikin account ɗina dubu bakwai, na sayi suga na dubu ɗaya, madarar gari gwangwani huɗu, na haɗu da me kifi na siya na dubu ɗaya, na koma gida na yi jollof ɗin rabin taliya da kifi, na ci na ƙoshi, na rage 'yar kaɗan, da yamma na ƙarasa abata, sannan na tashi na ɗora jollof ɗin shinkafa, gwangwani biyu da rabi na dafa a maimakon ɗaya da rabi da ya ce, kuma sai ga shi mun cinye ta tass.

Aka zo bacci, na yi zaton zai juya min baya ne ya bar ni yau na yi baccina cikin salama kamar kowace mace da take auren lafiyayye, sai ya ustaz ya ce ba haka ba, abubuwan da ya dinga yi min a ƙoƙarinsa na samawa kansa nutsuwa sai da na ji dama ba na fashin sallah na ba shi duka kawai na huta. Da safe ma haka ya tisa ni da romance, da rana dai yau bai dawo ba.

A haka rayuwar tamu ta fara miƙawa, a hankali ya koya min yawan karatun Qur'ani, tun da kullum sai ya ba ni hadda na kawo masa ita, sannan sallar dare har na saba, idan na ƙi tashi ya shiga shafa min ruwa a fuska yana kwaɗaitar da ni ladan dake cikin tsayuwar dare, abinci kuwa yadda ya tsara min ba haka nake yi ba, dafawa nake wanda na san zai ishe mu, mahaifiyarsa ta zo gidan sau ɗaya, ƙannensa mata sun zo su ma, abu ɗaya ne ya fara haɗa mu faɗa shi ne yadda na gajiya da yawan buƙatarsa, idan ya matsa min da wa'azi sai na saka masa kuka, kuma na ƙi zuwa ɗin, wataran ya rabu da ni wataran kuma ya yi ko ba na so, sai dai ya dauki fushi da ni.
[11/10, 5:34 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, KU YI MIN ADALCI KU BIYA NI HAKKINA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015

18

Duk maƙotan da na shiga babu wacce ta biyo ni, ko yara babu wanda yake shigo min, sai kace mugun abu, wataran sai na gaji da zaman kaɗaicin, idan na tambaye shi zan shiga sai ya hau yi mini wa'azin babu gaira babu dalili, har da na cewa "ka da ku yi fita, fita irin ta jahilan farko' ga shi idan ya tisa ni a gaba da wa'azi mai razanarwa a kan bijirewa umarmin miji duk sai na firgice, da wannan yake cuta ta, na bi umarninsa ko ba na so, ɓangaren abinci dai ba na biye masa, dafa wanda zai isa nake, yanzu sai na ci na ƙoshi ma kafin ya dawo, saboda na ga idan na zage na ƙoshi a gabansa wannan ma laifi ne, sai ya hau nasihar an ce a raba ciki gida uku.

Ƙarshe dai da na gaji na fara shiga maƙota ba tare da sanin shi ba, wannan wacce take sa'ata gidanta nake shiga, sunanta maman Haneefa, sai mu sha firarmu, amma sam ba ta shigowa gidana ni, wataran da na ritsa ta da tambaya sai take ba ni labarin ai ita ƙawar tsohuwar matar Ustaz ce, sun yi zaman mutunci sosai da Maraƙisiyya duk da wata uku kawai ta yi a unguwar, tun tana ɓoye Ustaz hariji ne har aka gane, saboda a lokacin ba shi da lokacin dawowa daga kasuwa, safe, rana, dare koyaushe dawowa yake, ya tisa ta a gaba, sai da kowa ya lura ba ta iya haɗe ƙafafunta a buɗe take tafiya, kuma kana kallonta ka san tana cikin damuwa, har dai ta fito ta faɗa mata ga yadda mijinta yake.

Na ce"To amma maman Haneefa don kin san halinsa mene ne na cewa ba za ki shiga gidansa ba".

Maman Haneefa ta ce"Hmm, ai ba ki ji abubuwan da suka biyo baya ba ne".

Ni kuwa har da gyara zama na ce"Mene ne ya faru?"
Chapter 28 · 0% Book details