Sashe 32
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da rana ma na dafa shinkafa gwangwani uku, na ci na ƙoshi na saka sauran a kula na tura ƙarƙashin gado, na kwanta na ɓata rai, da ya dawo cin abinci na yi banza da shi, ya shiga kitchen ɗin ya dafa taliya, ya zuba min na ƙi ci, ya koma kasuwa, da daddare ya tafi sallar isha'i na ci sauran shinkafata, sai ga shi ya shigo da gurasa, ita ma na ƙi ci, duk hankalinsa ya tashi yana ta ba ni haƙuri wai kar yunwa ta lahanta ɗan cikina, na yi banza da shi.
Kwana uku muna a haka da shi, shi duk a zatonsa ba na cin abinci, rana ta huɗu da daddare sai ga shi ya siyo tsire ya juye a faranti ya kawo min har da lemo, wannan ne na ɓata rai na ci, saboda ina marmarinsa, to abin da ba samu kake ba.
Bayan mun kwanta sai mutum ya matso, na matsa, ya sake matsowa ya ce"Haba ya ke Assayyada, tun da kika ci tsire ai na yi zaton komai ya wuce kuma shikenan, ashe da saura?"
Na yi shiru gabana yana faɗuwa, ya ce"Wallahi kwanakin nan da na ɗaga miki ƙafa ni kaɗai na san halin da nake ciki, yau dai na kai maƙura, a gaskiya ya zama dole ki ba ni hakkina ko ba kya so, indai kuma ba so kike na kauce hanya ba, bi ma'ana ta yi istimna'i, ke kuma ki kwana cikin tsinuwar mala'iku har sai kin wayi gari, ni wallahi na yafe miki ma, amma tsinuwar kawai nake guje miki".
Ya ƙaraci wa'azinsa ban kula shi ba, da ya da gaske ba zan ce na amince ba, ban kuma hana ba, sai ya birkito ni, ya fara cim ma ƙudurinsa, kamar ya manta da ciki a jikina, da na gaji ban ce masa na gaji ba kamar yadda na saba, kuka kawai nake yi mai cike da ƙunar zuciya na tsantsar baƙinciki da nadamar yarda da aurensa, a raina ina tunanin shi ne bai yi min adalci ba ko mahaifina?
[13/10, 7:20 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, KU YI MIN ADALCI KU BIYA NI HAKKINA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015
20
Da asuba ma bayan ya dawo daga masallaci haka ya min yadda ya so, ban kula shi, sai da ya yi iya yinsa, ban gaishe shi ba kamar yadda na saba, sai shi ya gaishe ni ban amsa ba, ya ce"Assayyada za ki dafa mana shayin ne ko na É—ora?"
Na yi banza da shi, ya shafawa kansa lafiya ya dafa, ya sha ya rage min da guntun biredi, da zai fita ya ba ni É—ari biyu da hamsin, ya ce"Kasancewar yau ba zan dawo da rana ba, kuma na ga babu kayan miya, shi yasa na ba ki wannan, anjima sai ki saka babban hijjabi ki suturta jikinki ki fita nan gabanmu akwai mai siyar da kayan miya, sai ki siya, bi ma'ana attaruhu da tattasai na É—ari biyu, ita albasal wato albasa ta naira hamsin, kin san sunanta kenan da larabci, shi kuma attaruhu da tattasai larabawa suna ce masa fil-fil, ma sha Allah".
Ko kallon shi ban yi ba, ya ɗora da faɗin"A bisa adalci da alƙawarin da na yi miki na duba na ga akwai buƙatar na daure na yi jarumtar rage round ɗaya a zamantakewarmu, shiyasa na cire wannan lokaci na rana, don haka ba zan dawo cin abincin rana ba, dama alal haƙiƙa a zahiri ba wai abincin nake buƙata ba, kawai don dai a raya sunnar ne, amma abinci ni kin san bai dame ni ba, ko kunu na siya na naira hamsin na zuƙe shi a leda cikin yana ɗagowa".
Ya ƙaraci surutunsa ya fita daga gidan.
Na kifa kai a kujerar da nake ina sakin kuka, Allah ne kawai ya san halin da nake ciki, sai kuwa matar da ta auri irin mijina, na yi kuka a ranar sosai, kukan baƙincikin halin Babana da ba zai tsaya ya fahimce ni ba, kuma a ranar na yanke cewar na gama kuka a auren Ustaz, na daina kai wa kowa ƙara zan zauna har sai na mutu, a ranar na kashe wayata na jefa a sif, ban siyo kayan miyan ba, shayin da ya bar min ma ban sha ba, na kwanta kawai ina tunanin yadda rayuwata take wakana, na san na yi laifi a baya, amma ai na yi nadama na tuba, ni na san auren Ustaz ƙaddarata ne da jarabawa, amma a yanzu na fara tunanin anya kuwa ba kamun Allah ba ne? Anya ba abin da na shuka nake girba ba? Zamanmu da Sadam nake tunawa, tabbas ya yi min cuta kala-kala, amma da ya tuba ya so mu gyara zaman me yasa ban yarda ba? Yanzu da wannan halin da nake ciki a wannan gidan me kama da kurkuku ai gara ma zama da kishiyar, tun da ban ga me matar Sadam ta tsare min ba, rabin abin da ya sa na ji zafin auren shi ne saboda tunanin za ta riga ni haihuwa, to ashe Allah Ya tsara ni ɗin ce dai zan riga ta samun ciki da Sadam, amma a garin shirmena cikin ya zube, wallahi a yau na ji inda za a mayar da bara bana da na yi haƙuri na zauna da Sadam, sai yanzu na gane ƙarya ma nake yi, Sadam ba fyaɗe yake yi min ba, wannan rayuwar da nake ciki yanzu shi ne fyaɗe na ainihi, tun da aka yi auren nan a ranar farko, kasancewarmu da shi ta farko ne kawai na san na ji shaukin abun, amma tun daga ranar ban sake fahimtar komai ba sai azaba kawai, na tsani sex gabaɗaya, gani nake ma ya riga ya kashe min sha'awata, ji nake kawai ba zan sake son kasancewa da namiji ba ko ba shi ba, na tsani namiji.
Ban ci komai ba duk yunwar da nake ji, har dare, na yi azumin da babu lada, ana idar da sallar magriba ya dawo gidan, ya ƙaraso falo da nake a kwance, ya zauna ya fara shafa ni yana cewa"Assayyada na yi kewarki fa yau, na yankewa kaina hukunci mai tsanani, minus one ɗin nan anya zan jure kuwa?"
Ban kalle shi ba, ban kuma hana shi ba, ya ce"Wai ni kam Assayyada me kike nufi ne? Na ga kin daina yi min magana gabaÉ—aya kin jingine ni a gefe, me na yi miki? Gaskiya ba na son wannan fushin, mu fa ma'aurata ne, idan akwai wani da kike zargin na yi miki ko ina yi miki buÉ—e baki za ki yi ki faÉ—a min ai, ni ba zan gane ba sai kin faÉ—a".
Ya dakata da shafa ni ya tashi ya shiga kitchen, ya fito ransa a haÉ—e ya ce"Wai Sayyada me kike nufi ne? Kenan yanzu kin daina girki a gidan nan ko me?"
Sai yanzu idonsa ya kai kan shayi da biredi da ya rage min, yana nan a inda yake, don yau ban yi ko shara ba, ba wanke-wanke, babu wanka, sallah kawai nake tashi na yi.
Cikin tsawar da ban taɓa ji ya yi ba ya ce"Ke Sayyada! Ba da ke ake magana ba? Me yasa ba ki yi girki ba?"
Ni ma a tsawace na ce"Ban yi ba É—in kuma ba zan yi ba! Ba dai ina ba ka abin da ka aure ni domin shi ba?"
Ya ƙure ni da wani irin kallo, na kau da kai ina ƙare haɗe fuska, ga yunwa tana sakaɗata amma don taurin kai ba na jin zan yi girki, ya yi ƙwafa ya fice daga gidan, sai bayan sallar isha'i ya dawo da ledarsa, bai kula ni ba ya zauna yana cin gurasar da ya shigo da ita, ya gama ci ya yi wanka ya shiga ɗakin gwado, wallahi na yi zaton zai yi fushi ya ƙi nema na, wajen ƙarfe tara sai ga shi ya leƙo falon, har yanzu fuskarsa a haɗe take, ya ce"Ke Sayyada, to tun da kin ce ba don ki dafa abinci na auro ki ba, la ba'asa na ji na yarda, sai ki taso a fara gabatar da abin da aka yi auren domin shi ko?"