Sashe 26
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban ce komai ba, ya fara cin abincin ya ce"Ina sauran kaza da na ba da umarnin ki sanya ta a cikin miyar?"
Na ce"Ni fa ba cinye tun da safe, saboda wannan ɗan shayin sam ban ƙoshi ba".
Ya ce"La ba'asa, dama ba zuba shayin kaɗan ne don sugan ya ba da ɗanɗanon da ake so, amma idan kina ganin za ki iya sha ko da zaƙin nasa ya yi rauni kin ga idan Allah Ya sa gobe muna cikin rayayyu kuma lafiyayyu bayan an gama haɗawa sai ki ƙara ruwa a naki".
Takaici ya hana ni cewa komai, ya gama zai fita na ce"Me za a dafa da daddare?"
Ya ce"Subhanallah, kina nufin yanzu nan macaroni leda É—aya ce muka cinye?"
Na ce"Saura yar kaÉ—an dai, ko ni kaÉ—ai ba isa ta za ta yi ba, zan ma iya cinye ta da yamma".
Ya ce"Subhanallah, Assayyada akwai buƙatar a yi miki tuni kan wata aya da Allah subhanahu Wa ta'ala Yana cewa "Kada ku yi almubazzaranci, lallai masu almubazzaranci su 'yan'uwan shaiɗanu ne, Assayyada kada daɗin duniya ya saka ki shagala ki manta wannan ayar, kuma shi kansa cin abinci barkatai ba shi da wani amfani, illa ne ma ga lafiya, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce a raba ciki gida uku, kashi ɗaya abinci, kashi ɗaya ruwa, kashi ɗaya iska, idan kika cike duka cikinki kin kaucewa faɗin ma'aiki, Ya ke Assayyada haƙiƙa ina da zama da ke, yanzu sauri nake yi, bari na dawo za mu yi magana, ita rayuwa ba haka take ba".
Na ce"To yanzu dai me za a dafa".
Ya ce"Kar ki sake É—ora tukunya, wacce ta rage É—in ki ci, idan ya so ni zan taho da wani abun sai na ci".
A sanyaye na ce"A dawo lafiya".
Bayan fitarsa na zuba tagumi, na kalli farantin da ya ce abinci ya yi masa yawa, kuma ga shi ya cinye shi tass, hakan na nufin dai noƙe cikinsa yake yi ba don ya ƙoshi ba kenan, ni Sayyada wa na aura? Wace rayuwa na shigo haka?
Na yi wanke-wanke, na yi sallar azhar, na kwanta bacci ya ƙara ɗaukata, wannan bacci nawa har da gajiyar da ya tara min, ana kiran sallar la'asar na tashi, cikina wayam kamar an yashe abincin da na ci, dama indai na yi baccin rana haka nake tashi da matsananciyar yunwa, da a gidan Sadam ne sai na sha Cornflakes, golden morn, Cerelac, snacks, yogurt, ko na haɗa shayi na sha, ba na ma rabuwa da manyan biscute kala-kala, idan ta raya min sai na yi alawar madara na yi ta sha, to yau ga ni a gidan da ko garin kwaki ba a ajiye ba, madara leda ɗaya mu biyu, Ya Allah.
Duk yadda na so na na danne zuciyata kar na ƙi cin macaronin nan sai da na cinye shi, saboda yunwa nake ji, har ga Allah ba zan iya kaiwa dare ban ci abinci ba, wajen magriba zuciya ta dinga raya min na dafa taliya na ci na ƙoshi na maze, amma dai na haƙura, ina tunanin tun da ya ce zai shigo da wani abun ƙila irin kazar jiya ce, ma ci tare.
Na É—auki waya na kira Mama muka gaisa, ta ce gobe za a kawo min gara, Baba ya haÉ—o min kayan gara, ita kuma yau É—in dubulan da cincin take yi min shi yasa ba a kawo ba, gobe za a haÉ—a a kawo".
Na ji daÉ—i sosai, na yi mata godiya, ta ce"Sayyada kina lafiya ba wata matsalar dai ko?"
Na ce"Lafiya lau Mama".
Ta ce"Don Allah ki kwantar da hankalinki, ki riƙe aurenki Sayyada, yaron yana sonki tun da har bai damu da abin da kika aikata ba, yanzu da kin fito za a ce ba kya zaman aure".
Na ce"Zan zauna in sha Allah Mama, Ku taya ni da addu'a Allah Ya ba ni ikon jurewa".
Ta ce"Kenan akwai matsala?"
Na ce"A'a, kawai dai ban fara jin son shi ba ne har yanzu".
Ta ce"Ai yanzu aka fara zaman Sayyada, indai kin buÉ—e zuciyarki za ki so shi, babanki ya ce mutumin kirki ne".
Bayan mun gama wayar, na kira Baba muka gaisa na yi masa godiyar gara, ina jinjina lallai Baba yana son wannan auren nawa, tun da wancen bai yi min ba. Na kira Babansu Anisa muka gaisa, na kira Umma ma, ina idar da sallar magriba ya dawo gidan, ya zauna na yi masa sannu da zuwa, na ce"A kai maka ruwan wanka?"
Ya ce"E kai min, ba don ina gudun shigar lokaci ba ma ai da kin taimake ni kafin wankan".
Ban kula shi ba don na fara tunanin cire shi daga cikin mutane, idan ba doki ba wane ne zai yi wannan aikin? Na zuba ruwan na kai, da ya fito shiga wankan sai da ya riƙe ni a tsakar gidan ya tattaɓa ni, da ƙyar na samu ya tafi wankan, bayan ya fito ya zauna yana karanta Qur'ani da ƙira'a mai daɗi har lokacin isha'in ya yi, ya tashi yana cewa"Bari na je lokaci saura kaɗan, ni nake Limancin sallar isha'i".
Na ce"A dawo lafiya".
Ana idar da sallar ya dawo, da leda a hannunsa, wallahi na yi zaton kazar ce ko balangu haka, ya ce na É—akko masa faranti, na É—akko a raina ina raya yau ba zan yi irin na jiya ba na bar masa kazar nan, sai na ma fi shi ci wallahi.
Yana juyewa kawai na ga ashe gurasa ce, itan ma yar kaɗan, sai tilin kabeji da albasa, raina ya ɓaci, ya kalle Ni ya ce"Assayyada ki kawo wannan macaronin sai mu haɗa mu ci bakiɗaya".
Na ce"Ni fa na cinye shi".
Ya ce"Subhanallah kin cinye? Ina fatan dai kin ƙoshi ko? Bi ma'ana yanzu gurasar nan sai dai ki ci don marmari".
Na ce"Wallahi yanzu ma yunwa nake ji, ni fa macaroni ba ya ma ƙosar da ni sai dai kawai na ci".
Ya ce"Subhanallah, lallai akwai matsala, haƙiƙa macaroni ya haramta a gidan nan, nan gaba ba zan sake siyo shi ba, duk abin da ba zai ƙosar ba mene ne amfaninsa?"
Na ce"Sai a ci don marmari".
Ya yi murmushi ya cd"Assayyada kenan, yanzu dai matso mu ci wannan É—in, duk da ba ta da yawa, amma idan mun yi hakan ma sunna ne".
Na ce"Ban gane ba".
Ya ce"Nana Aisha ta ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama bai taɓa cin gurasa ya ƙoshi ba, don haka mu ma kin ga ya kamata mu ci ta don marmari ko".
Na ce"Hakane".
Yana ci yana ba ni a baki, sai wasu abubuwa yake yi min masu kama da tausa, har muka gama, muka yi brush, ya tafi É—akin gado, ni kuwa ina sane na yi zamana a falon.
Can sai ga shi ya biyo ni yana cewa"Haba Assayyadata ya ga aikin lada kuma za ki ware kanki ki yi zaune a falo?"
Kamar zan yi kuka na ce"Ba na jin bacci ne, zan taho".
Ya ce"Dama ba bacci zan yi ba ni ma, taimaka mini za ki yi, daure kin ji habibiyata".
Ya kamo hannuna, yana cewa"Ni tsinuwar mala'iku nake jiye miki, in don ta ni ne zan iya yafewa".
Yau ma haka ya tisa ni a gaba kamar abinci, sai da na fara yi masa kuka sosai sannan ya sarara min yana cewa ya yafe min, amma bai ƙoshi ba, ban iya bacci ba sai da na shiga ruwan zafi, wani wahalallen bacci ya ɗauke ni wajen sha ɗaya da rabi, ƙarfe uku ya tashe ni, haka ya ja mu jam'in sallah muka yi addu'o'i, sannan muka koma bacci, yau ma da asuba da ya dawo sai da ya ƙara tisa ni a gaba, da safe ya fita ya siyo indomi guda uku, ya miƙo min yana cewa"Wannan ɗaya da rabi za ki dafa mana mu karya, bi ma'ana ta kwana biyu ce, ga suga nan, amma babu madara tun da zai kasance ne tamkar sinadari, kasancewar ba da biredi za a ci ba".
Ya shiga ɗaki ya bar ni riƙe da ledar da sakakken baki, indomi ɗaya ce take ƙosar da ni, tsakani da Allah, idan tare da Sadam ne uku nake dafawa, yanzu shi wannan wayo ne ko cutar da kai?
08028966015
[09/10, 6:07 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, KU YI MIN ADALCI KU BIYA NI HAKKINA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015
17
Na shiga kitchen ɗin, na dafa kamar yadda ya ce ɗin, na tafasa shayin, na kai falo, na tarar da shi zaune a kujera yana gyangyaɗi, na tsinci kaina da hararar shi, ina sane na buga cokaci a jikin farantin ya ɗan yi ƙara, sai kuwa ya farka firgigit, yana shafa fuska ya ce"Yi haƙuri ashe bacci ya ɗauke ni".
Na ce"To ai dole ka yi bacci, ka raba dare kana abu É—aya, sannan ka sake katse bacci ka yi sallah, kuma ba samun space É—in baccin rana kake ba, abun ya maka yawa".
Ya ce"Hakane, amma ai duk sun zama dole ne, babu wanda za a rage a cikinsu, farkon dare a bawa gangar jiki hakkinsa, ƙarshen dare kuma a nemi lahira, kin san na ɗan jima babu auren, na saba yin bacci a farkon dare, yanzu kuma abubuwa sun samu, shiyasa dole bacci ya dinga gizgata kafin jikin ya saba".
Na yi shiru ban ba shi amsa ba, na zuba masa shayin a kofi, na juye duka sugan, ya ce"Subhanallah, ya za ki zabga wannan uban suga har haka?"
Na ce"Ka sha ka ji idan ya yi yawa".
Ya ce"Ba lallai ya yi yawa ba, amma ke fa?"
Na ce"To wannan manejin na mene ne? A ce suga ma ba za a siyo wanda zai isa ba?"
Ya tsaya yana kallona na 'yan sakanni, kafin ya fara girgiza kai kamar wanda ya ji maganar da ta ba shi mamaki ko tsoro, ya ce"Kaico! Kaiconki Ya ke Assayyada, shin kin manta ni mijinki ne? Kin manta a ƙarƙashin ƙafata za ki samu aljanarki?"
Tsoro ya kama ni na ce"To yanzu me na faÉ—a me zafi a nan wanda zan iya rasa aljannata?"