Sashe 20
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wallahi duk a zatona Sadam ba zai iya haƙura da ni tafarat ɗaya ba, na zata zai ta bina ne yana damuna da waya a kan na yarda a mayar da aurenmu, sai kuma wannan halin ko'inkula ɗin da ya nuna ya dame ni, sautari idan ina zaune sai na dinga tunanin shi, na dinga tuna ko ke yake yi yanzu? Ko yana zuwana gidana ya kwana ko kuwa shikenan ya zama na amaryar gabaɗaya, ƙila ma har ta samu ciki yana can yana zumuɗi, sai na ji haushi ya kama ni, tsakani da Allah na tsani matar Sadam, ina matuƙar jin kishinta har yanzu, gani nake ta cuce ni, domin da bai ɗakko zancen ƙara auren ba da tuni yanzu muna ta rayuwarmu cikin farincin kamar yadda muka saba, ina nan da implant ɗina a jikina, Safna ta tarwatsa komai. Wataran kuma sai na yi tunanin ko ita ma idan ya neme ta ba ta ba shi haɗin kai ba yana yi mata fyaɗe? Sai wata zuciyar ta ce ai ita ba za ta ƙi ba ma, na san ma jarababbiya ce irinsa, haka dai kullum ba ni da tunani sai na shi, na saƙa wannan na kunce wancen, har na zo ma ina jin haushin kaina, tun da ina ruwana da shi? Yanzu ai ba mu da wata alaƙa kuma.
Gani nake ko cewa da ya yi idan ina buƙatar taimako na tuntuɓe shi ya faɗa ne kawai, ba don da gaske zai taimaka min ɗin ba, musamman idan na tuna lokutan baƙinciki da suka wanzu a zamanmu, wanda suka shafe na farincikin.
Watarana kamar a mafarki sai ga kiran Sadam a wayata, gabana ya faɗi rass, na shiga tunanin abin da zai faɗa min, na dai yi shahada na ɗauka da sallama, a raina ina tunanin ko dai yana can yana kewata ne, ƙila ya kasa jurewa shi yasa ya kira ni zai roƙe ni, ya amsa sallamar, muka yi shiru na ɗan lokaci, ban gaishe shi ba ma, sai shi ya ce"Sayyada mun tashi lafiya?"
A takaice na ce"Ƙalau".
Ya ce"Ma sha Allah, ya zawarci da zawarawa? Da fatan dai kasuwar tana kyau".
Raina ya ɓaci nan take, sam ban tsammaci maganar nan daga bakinsa ba, ni zai rainawa hankali? Sai kace wacce ta kasa haja zai tambayi ya kasuwar zawarawa? Wannan ai wulaƙanci ne, ban gama mamakin zancen ba ya ce"Uhm Sayyada? Akwai kasuwar kuwa?"
A fusace na ce"Ka kira ni ne saboda ka wulaƙanta ni? To kasuwa Alhamdulillah! Ai rayuwar zawarci ta fiye min rayuwar gidanka sau dubu, don haka zawarawa da zawarci Alhamdulillah!".
Ya yi yar dariya ya ce"Mai da wuƙar, ni dama tambaya ce, na kira ne na tambaye ki yaushe za a kwashe kayanki daga gidan nan? Ina so zan saka 'yan haya ne".
Na tuna kamar akwai lokacin da ya ce ya bar min gidan nan da muke ciki, sai kuma na kasa tuna yadda maganar take, amma na ji babu daÉ—i da na ji wai ya kira ne don ya faÉ—a min na kwashe kayana, ta tabbata dai aure ni da Sadam ya kare, Kodayake ai hakan nake so dama.
Na ce"Zan faÉ—a musu za a zo a kwashe".
Ya ce"To a hanzarta don Allah".
Na kashe kiran ban ba shi amsa ba, takaici na ji ya kama ni, haka dai na faɗawa Umma saƙon shi, sosai na ji Baba ya burge ni da aka kwashe kayan a ranar, aka zo aka jibge su a gida, Baba ne ya ba da shawarar kar a siyar, idan na samu wani mijin kawai sai a yi auren cikin sauƙi.
A kwana a tashi na ɗauki watanni biyar a gida, a hankali kuma sai hankalin mazan unguwarmu da kewaye ya fara yo wa kaina, sai ka ji ana sallama da sayyada, sai na fita na ga wani gajarabul ɗin, ya cika ni da zantukan banza, to wallahi a zancen banza nake jinsu, saboda ni cikin wanda suka taɓa zuwa wajena babu wanda ya yi min, duk ba su kai Sadam class da gayu ba, duk da akwai wanda suka fi shi kyau, amma ni ba kyau nake dubawa ba, don da shi ne da ban zaɓi Sadam ba, a ya yi wuta mutum ya yi zuwa uku, zan saita masa hanya da kora da hali, idan ma bai ji ba ko an yi sallama da ni sai na ƙi fita, kafin Baba ya fara matsa min, a dole nake fita ko ba na son mutum, kullum nasihar Baba ita ce na tsayar da wani cikin manemana na yi aure, shi ne mutuncina kuma gatana, yana saka ran idan na yi auren na auri miji na gari Baba zai iya yafe min, don har da ganina tare da Sadam a ƙara hasala shi, a hankalin ni ma na fara son na yi auren, amma na rasa wanda zan zaɓa, wallahi duk ba su yi min ba.
Akwai wani Sulaiman ɗan layinmu, ya fi kowa naci, adaidaitasahu yake ja, kuma ko fili ba shi da shi, lissafinsa a gidan haya za mu zauna, yana da nutsuwa sosai, ga shi ya iya magana, to shi dai talaucinsa ne ya yi min yawa, har ga Allah zan ji takaicin a ce na fito daga danƙareren gidan Sadam har da mai gadi, na ƙare a gidan haya, ban da haka da zan iya daurewa na aure shiga shi.
Sai kuma wani Abubakar, shi kuma yana da rufin asiri ba laifi, duk da bai kai Sadam ba, yana da gidansa ɗan madaidaici, matsalarsa ɗaya ya taɓa yin aure yaransa biyu matar ce ta rasu, kuma shi a tsarinsa idan an yi auren ni ce zan riƙe masa yaran, sai nake ganin kawai zai aure ni ne saboda na zama mai raino, don haka shi ma nake ganin ba mijin aure ba ne.
Aliyyu shi kuma saurayi ne, yana da gidansa mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, yana sona sosai, sai dai yana zuciya da saurin fushi, da fari na so na yarda da shi, amma tun da na ga fara yi min faɗa idan ya kira ni ya ji ba na gida sai na samawa kaina lafiya, sai ya ce wai me yasa ban faɗa masa zan je wajen kaza ba? Nan dai na gane irin Sadam ne, kuma idan ya samu damata tsaf zai mayar da ni ruwa, shi yasa duk nake ta juyi don cikinsu babu na zaɓa.
Ana haka ne Anisa ta haɗa ni da yayan mijinta, ya rabu da matarsa yaransu uku, ina jin haka na ce a'a, bai yarda ba sai da ya fara zuwa, Baba ya ce shi dai ya yaba da shi, na dai fara kula shi ba don ina jin zan iya aurensa ba, amma da yake Alhaji Shamsi ya isa soyayya da tsara zance sai ya fara jan ra'ayina cikin hikima, ya fi Saddam kyau, sai dai ya fi shi shekaru ma, amma ba girma ta yi can-can ba, sannan gidansa babba ne, kuma yana da kuɗi sosai, har ya fi Sadam, sannan yana da kyauta, ya iya tsara ni, tun ina jin wasu halayensa ne kawai suka fara birge ni har na zo na yarda ƙaunarsa nake yi, kuma har zuciyata na yarda da aurensa, har na ji zan iya riƙe masa yaransa, kuma ma yana ta ƙarfafata ya ce akwai mai kula da su, idan an yi auren ma ita za ta cigaba da kula da su.
Da kullum idan na zauna na yi ta tunanin rayuwata ta baya da Sadam, amma yanzu rayuwata ta gaba da Alhaji Shamsi kawai nake hasashowa, wanda na yi wa lakabi da Alhajina, kowa ya san ni bayan mutuwar aurena ya gan ni a yanzu zai gane na samu kwanciyar hankali, Mama ta san da ina son Alhaji kuma ita ma ta yi na'am da shi, Baba ne dai ban sani ba ko ta faÉ—a masa.
Wata ranar Juma'a Alhaji yake ce min na faɗawa Bana ranar Lahadi za a zo neman aure, idan an ba shi sai a saka rana tun a wajen, ba ya fatan abun ya wuce watanni biyu, shi ma don yana son ya yi gyaran gidan ne, murmushi na yi, wani daɗi ta lulluɓe ni na ce"Alhaji yanzu mene ne abun gyara s gidan nan namu?" Kasancewar ya tura min vedion gidan, kullum sai na kalla, na dinga tsara ga falona ga inda za mu dinga hutawa ni fa shi.
Ya ce"Za a canza fenti, ƙofofin ma za a canza wasu, ai ke ta musamman ce Sayyadata don haka dole na yi miki gyaran da zai dace da ke".
Na yi murmushi na ce"Na gode sosai".
Ya ce"Wai lefe zan yi miki ma ko gara kuÉ—in?"
Na rufe fuska ina juya masa baya alamar kunya, ya yi dariya ya ce"Sayyada kenan, wai kina nufin kunya kike ji kamar wata buduruwa? Kodayake a wajena ke sabuwa ce dall".
Na ce"Ba wani nan, kawai dai kana koÉ—a ni ne".
Ya ce"Wallahi har zuciyata gani nake kamar buduruwa xan aura, ke ma ki manta da wanann ƙaton cikin nawa ki bar shi a saurayi za ki aura, da sai mun fi more rayuwar auren".
Na ce"Ai dama kai saurayi ne a wajena, shi yasa ma idan muka yi aure..." Sai kuma na kasa ƙarasawa na rufe fuska.
Ya ce"Ƙarasa mana".
Na ce"A'a mu bar zancen".
Ya ce"To ina bin ki bashi, za ki faÉ—a min ta chatting ko da a rubuce ne".
Na ce"Na yarda".
Ya ce"Lefen zan yi ko kuÉ—i?"
Na ce"Duk abin da su Baba suka ce".
Ya ce"To ma sha Allah, sai ki sanar musu kar ki manta, Jibi in sha Allah za a zo, na gaji da gwaurancin nan".