Sashe 16
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saddam ya ce"Don Allah Baba ka yi haƙuri, na san tana gidan nan, kawai dai ranku ne ya ɓaci, ba za ta je ko'ina ba ban da nan, don Allah a yi haƙuri, zan gyara idan laifi na yi mata".
Baba ya ce"To ban san kuma da wane yaren zan yi maka magana ka fahimta ba, yanzu ni na yi maka kama da wanda zan yi maka ƙarya kenan? To kai ma ka sani, ko sakinta ka yi ba ta da wajen zama a gidana, ballantana kuma yaji, don haka ka tashi ka bar min gida".
Sadam ya shiga ɗaga hanci yana shaƙo numfashi kamar sabon maye, ya ce"Amma Baba kamar fa ina jin ƙamshinta, ina nufin turarenra".
Ya tashi tsaye, ai kuwa ya ga ashe a kusa da hijjabinta dake kan igiya ya tsugunna, ya gane hijjabin kuma ya tabbatar da ƙamshin, ya ce"Wallahi Baba Sayyada tana cikin gidan na , don Allah ku fito min da matata mu tafi, Wallahi zan gyara, wasu abubuwan kuma laifinta ne".
Baba ya rasa abun cewa, can kuma sai ya tashi ya leƙa ɗakin Mama, ya dawo ya leƙa ɗakin da nake, ina bayan ƙofa ni da kayana, amma wayata tana yashe a tsakar ɗakin, ya ƙarasa cikin ɗakin ya ɗauki wayar da Sadam ya kira ko zai jiyo ringing a cikin gidan, ya ce"Wannan wayar..."
Ido huɗu da muka yi ya sa ya ƙarasa maganar, na fashe da kuka ina cewa "Baba ka yafe min".
IN SHA ALLAH GOBE ZAN KAMMALA FREE PAGES, GOBE BA ZAN KARÆI 500 BA, DISCOUNT ZAI ƘARE A YAU, 700 NE LABARIN NAN
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
[01/10, 5:41 pm] Sadiya Abdulrazak: Da matuƙar mamaki mai haɗe da tsantsar ɓacin rai ya ce"Sayyada!?"
Na maƙale a jikin bangon ina maƙerƙeta, saboda na yi zaton dukana zai yi, amma sai na ga ya fita yana ƙwalawa Mama kira, ta fito daga banɗakin da ta ɓuya ita ma tana karkarwa ta ce"Na gaji, na gaji da yadda rayuwar 'yata take ƙunsar takaicin namiji me yasa maza ba kwa yi mana adalci ne?"
A fusace Baba ya ce"Au haka kika ce? Ni ne mara adalcin? To ki tattara 'yar taki ku bar min gida, wallahi sai kun bar gidan nan, idan Sayyada ta sake kwana a gidan nan a bakin aurenki!".
Na fito da sauri ina kuka na duƙa a gaban Baba na kama ƙafarsa zan fara yi masa magiya, ya yi min wata ƙafa sai da na gangara, Sadam ya taho da sauri ya tada ni tsaye ya rungume a ƙirjinsa yana cewa"Baba don Allah ka yi haƙuri".
Na fara ƙoƙarin janyewa daga jikinsa ina cewa"Ka rabu da ni, ya dake ni ɗin indai zai wuce, don Allah Baba ka kashe ni idan na zama gawa na san na zama free za ka yafe min".
Mama ma kukan take ta ce"Na yarda zan bar maka gidanka, gara na haƙura da auren na zauna da 'yata na jiɓanci lamarinta, Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana ballantana kai ɗan'adam".
Na ce"Don Allah Mama kar ki yi haka, ni ban cancanci ki ɓata aurenki saboda ni ba, zan tafi kawai amma wallahi ba zan cigaba da rayuwa a gidan Sadam ba, idan kuma aka matsa min komai zai iya faruwa" Na fashe da kuka sosai.
Sadam ma idonsa ya yi ja, ya ce"Baba Sayyada fa 'yarka ce, a duniya na tsani na ga wani yana tozarta ta tun ranar da na aure ta, ko ba ka kore ta ba dama wallahi ba zan bari ta zauna ba, ai ba sakinta na yi ba, kuma ba zan sake ta ba, ko mutuwa na yi yau na bar wasiyya kar Sayyada ta dawo gidan nan, ta zauna a gidana na mallaka mata shi halak malak daga yau, ke ki wuce mu tafi!" Ya ƙarasa da daka min tsawa rai a ɓace.
Sam bai burge ni ba, haushi ya ba ni soyayya, domin wannan abin da Baba yake yi min bai saka na ji ba na son shi ba, abu É—aya na sani na yi masa babban laifi shiyasa ya kasa yafe min, na ce"Kar ka sake ka ce za ka faÉ—awa mahaifina magana, kuma aurenka na ce na gama shi, don haka dole ka sake ni".
Ya ce"Ina kayan naki suke?" Bai jira amsata ba ya shiga É—akin ya É—akko jakar.
Ya kalli Baba ya ce"Ba dai ba ka son ganinta ba? In sha Allah ba za ka sake ganinta ba daga yau".
Sannan ya kalli Mama ya ce"Mama ki yi haƙuri ki zauna ki riƙe aurenki, ko kin kashe aurenki ba za ki rayu da Sayyada ba, don wallahi babu kotun da ta isa ta saka na sake ta ballantana mutum, amma ki saka a ranki 'yarki tana cikin aminci, idan ta shiga ƙunci ita ta so".
Ya kalle ni ya ce"Sayyada mene ne amfanin zama a inda ganinki a wajen zai haddasa husuma da ɓace-ɓacen rayuka? Na yi miki alƙawarin kyautatawa daga yau, wallahi zan zauna da ke bisa adalci idan a baya ina yi miki abubuwan rashin adalci yanzu zan gyara zan yi miki adalci".
Ya riƙe hannuna yana cewa"Mu je gida, mijinki yana tare da ke har ƙarshen numfashinsa".
Na firge, ya sake damƙar hannuna ya fizge ni zuwa waje, ya jefa ni a motar ina ta kuka ya ja muka tafi, ban tsagaita da kukan ba shi ma bai rarrashe ni ba har sai da muka ƙarasa gida, ya faka motar ya ce"Ki fito".
Na ce"Wallahi Sadam cigaba da rayuwa tare da ni ba zai yi maka daÉ—i ba, za ka yi danasanin dawo da ni gidan nan".
Ya ce"Na ji na yarda, indai ke zai yi miki daÉ—i ai shikenan".
Na ce"Na tsane ka Saddam, ka kiyayi zama da wanda ya tsane ka musamman ma mace".
Ya yi shiru yana kallona, ni ma shirun na yi ina jin yadda tsanarsa ke ta'azzara a zuciyata wallahi ji nake shi ne wanda na fi tsana a duniya, sai yanzu nake ganin girman cutar da ya yi min, ina zan kai fushin mahaifina?
Ya ce"Sayyada, ki yi haƙuri kin ji? Amma idan kika duba ba ki da wata mafita wacce ta fi mu cigaba da rayuwar aurenmu, in sha Allah za ki samu haihuwa idan ma don ita ce, kuka kishiya babu ruwanki da ita, wallahi ba zan rage komai da nake yi miki na kulawa ba a matsayinki na matata, ni fa ba mahaukaci ba ne, ba kuma ba ni da zuciya ba ne, wannan ƙiyayyar da kike nuna min da rashin kunya abun yana yi mini zafi sosai, kawai ina daurewa ne saboda na san a baya na cutar da ke, sai nake ganin na dawwama da ke na riƙe aurenki da amana shi ne zai wanke ni a zuciyarki da kuma idon iyayenki, amma kin ƙi ba ni haɗin kai, ya zan yi ne? Me kike so na yi miki ki yarda da ni?"
Na ce"Ka sake ni, sakina kawai za ka yi na yarda kana sona kuma ka yi min halakci, don Allah idan kai É—an halak ne ka sake ni Sadam".
Ya yi huci mai zafi, ya fita daga motar, ya zagayo inda nake ya fito da ni, cak ya É—auke ni ya dire ni a falo, ya ce"Kina jin yunwa ne?"
Na yi banza da shi ina ta kuka.
Ya zauna ya riƙe hannuna yana ta wasa da shi, ya ce"Sayyada".
Ban amsa ba, ya cigaba da faÉ—in"Don Allah ki dakata da wannan shirmen, ina sonki, kina sona..."
Na katse shi da faÉ—in"Gyara kalamanka, ka ce dai a da na so ka, amma wallahi ban da yanzu".
Ya ce"Yanzun ma kina sona, ɓacin rai ne kawai, kuma na san za ki huce, yanzu dai ina so zamanmu ya dawo kamar farko, mu rayu cikin farinciki don Allah".
Na daka tsaki na ce"Ko za ka kwana ka wuni kana magana abu É—aya kawai nake jin kana maimaitawa, kalmar saki kawai za ka furta min na san an samu cigaba a kalamanka".
Ya ce"Ai kuwa ba za a samu cigaban ba, ni dai Allah Ya sani na yi iya yina, tun da taurin kai ne da ke ki je ki yi duk yadda kika ga dama, amma kar ki manta ni mijinki ne, aljannarki tana ƙarƙashin ƙafata".
Na ce"Ai ba miji irinka ake nufi ba".
Ya ce"Ok, ko me za ki yi, ki yi, ga wajen nan".
Yana gidan a ɗakinsa ni ina falo ina ta ƙunar zuciya, har aka kira sallar azhar, ya fita masallaci, na tashi na ɗauki jakata na fito ba don na san inda zan je ba, amma kawai burina na yi nesa da shi, na gujewa aurensa, na ji daɗin ganin Baba mai gadi ba ya nan, da sauri na ƙarasa, sai dai ina zuwa na ga kwaɗo a jikin ƙofar, na san dai ni ake tsarewa, tun da don zai tafi sallah ba ya rufe ƙofar ta ciki, na ja jiki na koma ina hawaye, ni ma sallar na yi, na zauna ina ta tunanin mafita, wata zuciyar ta ce na haƙura na zauna da Sadam mu gyara zaman, wata kuma ta ce idan ban bar gidansa ba baƙincikinsa ne zai kashe ni, saboda duk daɗin baki yake yi mini ba zai canza hali ba, kuma na fi yarda da ba zai canza ba ɗin, tun da tun yaushe muke tare? Tun yaushe yake cuta ta?
Bai dawo da wuri ba, saboda sai da ya je ya siyo mana abinci, ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ajiye min, na shige ɗakinsa da na shi, wajen la'asar ya fice daga gidan bai kula ni ba, bayan magriba ya dawo da abinci a kula, ya ajiye min, nan take na fara tunanin daga gidan shegiyar matarsa ya karɓo, don haka na ce"Ka ɗauke ba zan ci ba".
Ya ce"Ok".
Ya matsar da shi daga gabana, ya ce"Sayyada, yau na dawo É—akinki, kuma kwana biyu za a dinga rabon kwanan, ai ya yi ko?"
Takaici ne ya hana ni cewa komai, ina raba shi da kiwon kyalle yana kyalle ta haihu? Ya ce"Sayyada".