← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 89

Sashe 69

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya É—ago ya yi min wani kallo mai cike da gargaÉ—i, ni kuwa a raina na ce wallahi ko dukana za ka dinga yi ba zan dinga yi maka magana da jam'u ba, sarautar taka a wajen matarka kaÉ—ai za ta yi tasiri.

Na kauda kai, ya ce"Ok ki kwantar da hankalinki a hankali za ki hau kan hanya".

Ya tashi ya kamo hannun yaron, ya nufi wannan ɗakin da yake kulle, ya fara kiciniyar buɗewa, na bi shi da kallon rashin fahimta, na tashi na bi bayansu, ya buɗe suka shiga, ni ma na mara musu baya, domin na ga dalilin da ya sa sai yau za a buɗe ɗakin, turus na yi ganin ɗaki cike da kayan yara, ga gado na yara da sif da madubi, ga kuma kayan wasa nan kala-kala har da kayan ciye-ciye, yaron ya hau murna yana taɓa kayan, ya shagala da kallonsa yana murmushi, ya ɗauke shi ya cilla a gadon yana yi masa wasa, sai na daskare da mamaki.

A bazata na ga hawaye ya sakko masa still yana murmushi, ya share, ya juyo ya kalle ni ya ce"Sayyada ga Dauda nan mun ɗakko shi, mun yi alƙawarin za mu riƙe shi da amana kamar ɗan da muka haifa, ba mu taɓa haihuwa ba, kuma muna son yara, suna saka mu nishaɗi ko kallonsu muke yi, muna fatan nan da wata shekarar a ce kin samawa Dauda ɗan'uwa ko 'yar'uwa da za su zauna a ɗakin nan, duk da ba wai muna sonki ba ne kamar yadda ba kya sonmu, amma muna roƙonki ki rayu da mu alfarmar ɗanki da muke son rayuwa da shi, za mu yi miki adalci daidai gwargwado, idan kika yi biyayya kika daina raini da rashin kunya za ki ji daɗin zama da mu".

Farinciki ya kama ni, jikina ya yi sanyi, na ce"Na gode, Allah Ya saka da alkhairi".

"Babu wata godiya, Dauda ɗanmu ne ai, fatanmu dai a kula da mu sosai, kar a ba shi duka kulawar, duk wani abu da yake buƙata wanda yake nauyinki ne ko na mahaifinsa, ki sanar da mu za mu yi iya ƙarfinmu in sha Allah".

Na ce"Na gode sosai".

Ya juya ya fita daga É—akin yana cewa"A zo a zuba mana tuwon, a zauna har mu cinye ko kuma ma a bamu a baki".

Ban san lokacin da na harari bayansa ba, a raina na ce Allah Ya kiyaye, na bi bayan shi na zuba masa na zauna ina kallon gefe, ya ce"Ki saka hannu ki ci".

Na ce"Na ƙoshi".

Ya ce"To daga yau dole ne a dinga jiranmu yayin cin abinci, saboda tare ake ci da mu".

Na yi shiru, tun da ban gamsu ba, ba zan karɓi wannan sharɗin ba.

Sai da ya kusa gamawa sannan Abiy ya fito daga É—akinsa, ya fara yi masa murmushi yana cewa"Zo mu ci tuwo Dauda".

Raina ya fara ɓaci da wannan kiran sunan shi gatsal, na ce"Ba fa Dauda muke ce masa ba, Abiy".

Ya ce"Sunan babanki ne? Sai da muka tambaya aka ce sunan kakan shi ne na wajen uba, to mene ne haɗinmu da shi da za mu ɓoye masa suna?"

Na ce"Amma dai a ƙalla ai ya ce masa Dawoud ko".

Ya ce"Sayyada mun lura za a sha fama da ke kafin wannan raini da gillin su sauka daga kanki, mun faɗa miki mu fa sarakai ne, a ƙarƙashinmu kike, don haka dole ki bi ra'ayinmu da dokokinmu".

Na ce"Ni dai ban ji wani hadisi da aka ce a dinga yi wa miji jam'u ba, don haka sai dai ka bari idan na saba, idan kuma bakina bai juye ba sai ka yi haƙuri da ni".

Na yunƙura zan tashi, ya riƙo hannuna ya dawo da ni ya zaunar, ya tsura min ido, ni ma tun ina kallon shi har na ji ya yi min kwarjini, na kau da kai ina ɓata rai, ya ce"Ki kiyaye mu Sayyada, sannan idan muna cin abinci ba a barinmu mu kaɗai, idan kuma ba za ki iya ba za mu dinga kiran matarmu wacce ta san darajarmu tana taya mu ci".

Na kwace hannuna na ce"Ai ni zan fi son haka, da ka san da matar taka me yasa za ka zaunar da ni?"

Na tashi na koma falo, Abiy ya biyo ni sai ya kira shi, ya É—ora shi a cinya yana ta ba shi tuwon, da suka gama ya zo ya ce"Ga shi sai ki yi masa wanka don ya ji daÉ—in baccin ko".

Na karɓe shi, na yi masa wankan, na dawo falon na zauna, shi kuma ya shiga ɗakinsa, ina kallo ina danna waya har Abiy ya yi bacci Saraki bai fito daga ɗaki ba, na je na kwantar da shi a ɗakinsa, na tofe shi da addu'a, na nemi waje na zauna ina ta tunani, a haka dai wannan Sama'i'lan kamar zai yi mutunci, amma kuma ɗan rainin hankali ne na ƙarshe, ni dai zan yi masa biyayya iya wacce zan iya, abin da ya fi ƙarfins kuma sai na bar shi, na ji daɗi sosai da yadda ya nuna yana son ɗana, hakan ya saka ni ganin mutuncin shi, amma ba dai so ba, ina zaune a nan ɗin na ji ringin ɗin wayata daga falo, na tashi na je na cire ta a caji na duba na ga Sama'ila don da haka na yi saving, na ɗauka duk da na san yana ɗakinsa, ya amsa sallamata ya ce"Dauda ya yi bacci ne?"

Na ce"E".

Ya ce"To me kike jira kenan? Ki zo É—akinmu za mu ba ki hakkinki".

Gabana ya faɗi, ni fa dama ba auren ba, ina fargabar yadda zan sake haɗa shimfiɗa da namiji ne damuwata, na tsani sex gabaɗaya, haka na daure zuciyata ina tuna hakkinsa ne dole na ba shi, idan Ustaz yana cewa ya yafe min ƙila shi wannan ba zai yafe min ba, murmushi ya kufce min da na tuna wa'azin ustaz mai cike da son zuciya, na sake yin wanka, na shafa humra, na saka rigar bacci na ɗora hijjabi a kai na tafi ɗakin nasa, yana zaune a bakin gadon da counter maƙale a hannunsa yana motsa baki, ya tashi yana cewa"Muna fata da alwalarki".

Na ce"Akwai".

Ya ce"To Alhamdulillah!".

Ya yi min nuni da sallah, na ɗauka na shimfiɗa, ya ja mu sallah bisa sunna, muka idar ya dinga addu'a ina amsawa a hankali yadda ba zai ma ji ba, sai da ya gama ya shafa ya kalle ni ya ce"Da alama da gaske ba kya sonmu, tun da ƙiyayyar har ta kai ba za ma ki amsa addu'armu ba".

Na yi kamar ban ji shi ba.

Ya hau gadon ya kwanta,ya ce"To sai ki kashe mana fitilar ko, ba ma son haske".

Tsoro duk ya kama ni, na shiga damuwa, na kashe fitilar, na nufi gadon na kwanta can nesa da shi, muka yi kamar minti biyu a haka, kafin ya ce"Sayyada, ki matso ko ni ne zan matso?"

A raina na ce'Ai kuwa sarautarka ta ci uwar ƙarya ta kwana da yunwa a nan, indai ni ce zan matso ba kai ba'.

Na yi kamar ban ji ba, ya sake cewa"Ki matso kusa da ni mana ko ba kya ji?"

Ai kuwa na yi kamar ba na ji É—in ba.

Ya ce"Idan ba ki karɓi aurenmu ba ki tashi ki bar ɗakin nan, za mu ba ki lokaci har zuwa lokacin da za ki kawo kanki sai mu yi yadda muke so, amma ki sani ba za mu lamunci raini ba".

Ban kula shi ba, kuma ban fita É—in ba, wajen minti biyar da yin haka sai ji na yi mutum ya matso, a raina na ce'Ashe dai ka matsu'.

Tamkar 'yar tsana na zame masa, ya dinga juya ni yadda yake so, tun a romance ya ba ni mamaki, domin ya fi Sadam da Ustaz, amma sai dai jikina ne kawai yake sauraron saƙon ban da zuciya da ƙwaƙwalwata, hakan ya sa sam ban ji daɗi ba, sai ma ƙagauta da na yi ya gama ya rabu da ni, bayan komai ya kammala ya ce"Mun gode da yarje mana, sai dai mun yi Allah wadai da rashin ba mu haɗin haka, amma ki kwantar da hankalinki, a hakan ma za mu dinga bi, tun da dai burinmu shi ne ki samu ciki ki haihu ba wai mu samu nutsuwa da ke ba, ga matar samun nutsuwa can muna da ita, ke kuma sai ki samu nutsuwa da rashin kunyarki".

Ban ce masa komai ba, na tashi na bar ɗakin, na koma ɗakina na yi wanka na kwanta, zuciya tana ta bijiro min tunanin Sadam, da faɗa min a yadda yanzu yake sona da zumuɗina inda shi na aura da ba haka daren farkon mu zai kasance ba, amma da na tuna ya yi aure sai na watsar da wannan tunaninna dinga istigfari har bacci ya ɗauke ni, sam ban tantance me na ji a kasancewa da mijina ba, dama tun ina gidan Sadam aka raunata sha'awata da wannan dolen da yake yi min, ƙarshe kuma na zo na auri wanda yake neman rayuwata ma, ya ƙarasa kashe min sha'awar duka.

Washegari yana tashi Dauda ya fara tambaya, na ce masa yana ɗakin shi yana wasa, ya zauna kenan zai fara karyawa sai ga Hajiya Halima ta shigo da bata abincin, ta ajiye masa a table ɗin, na gaishe ta na bar wajen, sai kuwa ta zauna suna ta fira, sai bayan ta tafi shi kuma ya koma ɗakinsa na ga bai ci nawa abincin ba nata ya ci, na jinjina kai na fara gyaran gidan, ya fito yana cewa"Mu za ku fita, muna sanar miki yau za ki yi baƙi, 'yan'uwanmu za su zo ku gaisa, mun san kuma suna da yawa, saboda haka ki yi abincin sama da mutum goma, idan ba za ki iya ba, akwai mai taya Hajiya aiki ki je ki ce ta zo ta taya ki".

Na ce"To in sha Allah, game da tuwon daren naka kuma, babu cefanen miyar".

Ya ce"Ki yi list É—in abin da za a kawo, sai ki tura mana ta massage za a lawoyin sha Allah".

Na ce"To a dawo lafiya".

Ya amsa da amin.
Chapter 69 · 0% Book details