← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 89

Sashe 60

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safna ta ce"Tun kafin ƙaddararren aurenta ya mutu take bibiyar mijina, ina ta haƙuri, yanzu ma kullum sai sun yi waya da shi a gabana, sannan yau na same su a cikin mota suna aikata son ransu, kuma ba wannan ne karo na farko da suke haɗuwa ba, ko a hotels ko a gidana, yau abun ma ya kai ba za su iya haƙuri su ƙarasa wani wajen ba shi ne suka keɓe a mota...!".

Tana zuwa daidai nan na shiga ɗakina da gudu, na ajiye Abiy na rushe da kuka, sannan na lalubi wayata a jaka na kira shi, yana ɗagawa na rushe da kuka na ce"Ka cuce ni da ka sa muka haɗu yau, ga matarka nan ta biyo ni har gida tana yi mana ƙazafin wai muna aikata ma sha'a, na shiga uku Saddam, silarka iyayena za su ƙara ganin baƙina".

Ransa ya yi mugun ɓaci, ya ce"Safnan ce ta zo gidanku? Yanzu ta tafi ko tana nan?"

Na ce"Ba ta tafi ba, ta riga ta gama lalata ni a idon uwata, ya zan yi da rayuwata wane bayanin zan yi a fahimce ni?"

Ya ce"Sayyada, ki fita ki faÉ—awa Safna ni mijinta Sadam na sake ta!".

Na kashe wayar na zauna ina ta kuka, har ta gama bambaminta, Mama tana ta ba ta haƙuri ta bar gidan.

08028966015
[04/11, 7:42 pm] Sadiya Abdulrazak: 36

Tana tafiya Mama ta faɗo ɗakin da nake, gabana ya yi mummunan faɗuwa ganinta da taɓarya ta tunkaro ni, na miƙe tsaye ina"Ki yi Mama don Allah, kar ki kashe ni na rayata a wuyanki, wannan shi ne ƙaddarata".

Allah Ya taimake ni ta jefar da taɓaryar ta yi kaina, na maƙale a kusurwar ɗaki, ba zan tuna yaushe rabon da Mama ta dake ni ba, tun ina yarinya sosai, amma yau haka ta rufe ni da duka ta ko'ina, ina ta gursheƙen kuka, amma ba na zafin dukan ba, na jin haushin kaina a kan ɓata mata rai, da kuma tausayin kaina, saboda idan na rabu da Saddam ba na jin zan sake yin aure, sai yanzu na gane abin da yasa ake cewa mace ta yi haƙuri da mijinta, inda na san zan so Sadam bayan rabuwarmu kuma ba zan samu kamar shi ba, da na haƙura a wancen lokacin mun cigaba da zaman ko babu daɗi.

Da ta gaji da dukana sai ta fashe da kuka ta bar ɗakin, na rarrafa na ɗauki Abiy da yake ta kukan shi ma, na rungume shi na cigaba da kukana, har ya yi bacci, ina ji kira yana ta shigowa wayata, kuma na san Sadam ne, amma ban ma duba ba ballantana na ɗauka, nadama duk ta rufe ni, ban sake jin motsin Mama ba, sai da aka kira sallar azhar, na ji ta fito tana zuba ruwa a buta da alama alwala take yi, na kwantar da Abiy ni ma na fito bayan ta koma ɗaki, na yi alwalar na yi sallah kaina sai ciwo yake yi, wajen ƙarfe biyu da rabi na gane Mama ba za ta yi girki ba, na fita na shiga ɗakin nata, na tsugunna rakuɓe a jikin labule kaina a ƙasa na ce"Mama don Allah ki yi haƙuri ki yafe min, in sha Allah ba zan sake wannan kuskuren ma, kuma wallahi matar nan sharri ta yi min, na rantse da Allah ƙarya take, na san dai mun haɗu amma wallahi a kan hanya ne, ba mu taɓa zuwa wani waje ba".

Ƙala ba ta ce min ba, har na ƙaraci tsugunon na tashi, na ce"Me zan dafa miki?"

Nan ma ba ta kalle ni ba, na fito na kunna wuta na ɗora, jollof ɗin taliya na yi, har na gama ba ta ce min komai ba, na zuba na kai mata, na bar ɗakin, don ita na yi, ni ko yunwar ma ba na ji, na yi wanka na sha magani na kwanta, da na tuna ƙila fa aurena da Saddam ba zai yiwu ba sai hawaye ya ɓalle min, na wuni a ɗaki, zuwa la'asar na fita daga gidan, na siya awara da lemo, na ci na zauna jugum ina jiran dawowar Baba, duk da ina kokonton za ta faɗa masa ko za ta rufa min asiri? Baba yana dawowa bugun zuciyata ya canza, na yi tsuru-tsuru, na kasa fita na yi masa sannu da zuwa, ina jin lokacin da yake tambayar Mama me yake damunta? Gabana ya ba da rass, na miƙe tsaye, ban ji dai muryarta ba, amma na ji shiru, kafin kuma na ji Baba ya ƙwalla min kira cikin ɗaga murya"Sayyada! Ke Sayyada!".

Na ɗora hannu a ka, ina jin kamar na yi tsuntsuwa na bar gidan, sai da ya sake kirana sannan na fito, na rakuɓe nesa da su na ce"Baba sannu da zuwa".

Bai amsa ba ya ce"Zo nan Sayyada".

Na ƙarasa gaban shi na durƙusa ina kallon ƙasa, ban ankara ba na ji saukar mari a fuskata tass, na gigice na fara kuka, na ce"Don Allah ku yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake ba, kuma wallahi sharri ta yi min ƙarya take".

Ya ce"Yi min shiru! Mutuniyar banza, wato dai idan aka cire maka Zakka a gida babu yadda za ka yi sai ka ba da zakkar nan, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Sayyada so kike wani ciwon ya kama mahaifiyarki? Don wallahi ita abun ya fi damu, ni dai don na yafe ki har lahira ba komai ba ne a wajena, ashe tun kina cikin idda kike tare da shi?"

Ya kalli Mama ya ce"Wallahi ke ma da laifinki tun da dai har ya zo gidan nan da sunan zuwa barka ba ki faɗa min ba, tukunna ma, ba kya ɗaukar taɓarya ki sheme ƙafar ɗan banza? Kai Allah wadaran naka ya lalace".

Ni dai sai kuka nake yi kaina a ƙasa.

Ya ce"Gobe da kaina zan kai ki asibiti a yi miki gwajin ciki, idan aka samu babu to barkanki, kuma ki sani ba za ki sake fita ko ƙofar gida ba sai ranar aurenki, ko manemi kika samu na yi alƙawarin sai dai ku dinga zance a cikin gidan nan".

Na ce"Don Allah ku yi haƙuri".

Ya ce"Haƙuri ke ya kama, kuma kanki kika cuta Sayyada, ke kanki ba ki san ki yi wa adalci ba, ballantana mu iyayenki, idan kin yi mana kin rabu da shi ruwanki, idan kuma kin ga ba za ki iya rabuwa da shi ba to ki shiga duniya kawai, domin ba zan taɓa sauka a kan bakana ba, ke da Sadam kun gama zaman aure".

Wani abu ne yake cakar zuciyata idan na ji an ambaci rabuwata da Saddam, amma haka na daure ban musa ba, ya yi faÉ—an shi ya gaji don kan shi, ya ce na tashi na ba shi waje, na shiga É—akina na rushe da kuka, daidai nan kiran Sadam ya shigo.

Na ɗaga ina tsananta kukana, ya yi shiru yana saurarona, ganin abun ba na ƙarau ba ne ya sa shi faɗin"Ya isa haka Sayyada, kukan kuma na mene ne?"

Na ce"Ai ka fi ni sani".

Ya ce"To ba ya wuce ba? Na sake ta, kuma idan kin ga na dawo da ita to kin tabbatar min ba za ki aure ni ba ne, ke sai dai ma na auri wata, amma Safna na gama zama da ita in sha Allah, tun da na yi mata hukunci mafi tsauri ai ya kamata ki huce ko?"

Na ce"Ba kukan abin da ta yi min nake yi ba, kukan ɓatawa iyayena rai nake, an dake ni an yi min faɗa, na yi nadamar fitowa yau".

Ya ce"To ya zamu yi? Ni ma dukana ne kawai ba a yi ba, tun da daga gidan naku gidanmu ta wuce, to amma ya za mu yi? Matuƙar ba guduwa za mu yi wani wajen mu yi auren sirri ba ya zama dole mu fito mu nunawa duniya da su iyayen namu muna tare, kuma ba za mu rabu ba duk runtsi, wallahi Sayyada idan ba mu yi aure ba ke kika so".

Na ce"Ai ka san ba zan so haka ba sai idan ya zama dole".

Ya ce"Idan na zo zance kika fita, gobe ma kika fita ko dukanki suke idan kika dawo haka za ki daure, dole za su gaji, idan kuma suka ɗaure ki sai ki ƙi kula kowa da auren, ai ba za su kwaɗa ki su cinye ba ko? Da a ce kin auri wani ai gara ni da ke ɗin mu rayu ba mu sake yin auren ba, ni dai idan kin ga na yi aure to kin saɓa alƙawarinmu ne kin yi, daga nan na san ba kya tare da ni".

Na ce"Ina tare da kai har abada Sadam".

Ya ce"To gobe zan zo zance".

Na ce"A'a don Allah!".

Ya ce"Zan zo".

Ya kashe kiran, na kira ya ƙi ɗauka, na bi shi da saƙo ina roƙon shi kar ya zo, haka na kwana rai babu daɗi.

Washegari har na manta da furucin Baba na cewar zai kai ni asibiti, sai ga shi ya ce na shirya mu je, na ce"Wallahi Baba sharri ta yi mana, ba wani abu da ya taɓa shiga tsakaninmu".

Ya daka min tsawa rai a ɓace ya ce"Kin wuce mun tafi ko sai na targaɗa ki?"

Na saka hijjabi na goya É—ana muka tafi, ina ta hawaye a adaidaitasahu, sai da aka yi gwajin sannan Baba ya yarda, muna dawowa gida ya na zauna a tsakar gida, na zauna ya ce da Mama"Maza shiga É—akinta ki bincike min shi tsaf, ki kawo min wayarta da katin cirar kuÉ—inta, ko caza kar ki bari".

Mama ta shiga ta bincika, sai ga ta ta fito da wayoyina biyu har da kwalin sabuwar, da kuma ATM É—in, ta kalle ni ta ce"Yaushe kika siya sabuwar waya?"

Na sunkuyar da kai.

Baba ya ce"Har kya tsaya tambaya? Shi ya ba ta, shi ne ya ba ta, wa zai ba ta? Lallai ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron yaran zamani".
Chapter 60 · 0% Book details