← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 89

Sashe 8

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

08028966015
[25/09, 4:11 pm] Sadiya Abdulrazak: Tun ina ɓoyewa makusanta yadda Sadam yake juya ni, ni kuma nake bin umarninsa kamar shi haife ni, har abun ya bayyana kowa ya gane, ba ƙaramin faɗa nake sha a wajen Mama ba, ƙawaye ma suna ta ganin baikena, ni kuwa ko a jikina don ji nake indai Sadam zai yarda da ni ya yi farin ciki da ni na wuce wajen. Zuwa gidan biki ko na 'yan'uwa sai wanda ya ga dama yake barina, ballantana na ƙawaye, haka kowa zai tafi, a bar ni ni kaɗai a gida, kuma sam ba na damuwa, Anisa ƙawata ce kuma 'yar'uwata, amma lokacin aurenta haka ya hana ni zuwa wajen dinner, ranar na yi kuka, musamman na gorin da na sha a wajen 'yan'uwa, haka aka dinga caccake ni, ana tsinewa soyayyar tamu, kuma a daren sai da ya zo zance, saboda ma ya tabbatar da ban je ɗin ba, yana ganin fuskata babu walwala shi ma ya haɗe tashi fuskar, ya shiga yi mini faɗa yana cewa"Sayyada saboda na hana ki zuwa wajen wannan shirmen shi ne za ki ɗauki fushi da ni? To ko da na hana ki zuwa ai umarni ne na ba ki, kina da damar bijirewa, tun da ban ɗaure ki ba, yanzu ma ki tafi ai ba ki makara ba, ban yi miki dole ki bi umarnina ba, amma kin san sharaɗin da soyayyarmu ke saƙale da shi ko? Idan kin ga kin zaɓi rabuwar fine!".

Daga haka ya bar ƙofar gidanmu, na kasa bacci sai da na kira shi, ya ƙi ɗauka duk nacina, haka ita ma Anisa na dinga kiranta ta ƙi ɗauka, sai da ta yi mini massage sannan na haƙurwa, cikin saƙon take ce mini, tun da na zaɓi wani ɗan iska a kanta kar na sake nemanta, gobe ma ba ta gayyatata, don kar na je ya tsine min na bi duniya, na share hawaye a fili na furta"Ba za ku gane ba".

Washegari da sassafe sai ga kiran shi, na É—auka muka gaisa sama-sama, ya ce"Kin tafi gidan biki ko kina gida?"

Na ce"Ina gida".

Ya ce"To ki je, amma ki tabbata a gidanku kika yi sallar isha'i, duk wani shiririta da shirme da za ku yi kar ki sake ya wuce magriba, ki koma gida zan zo".

Kamar zan yi kuka na ce"Amma fa akwai kai amarya, kuma Mama ta ce yau a can zan kwana, tun da wajen kai amaryar za a iya kai wa dare".

Ya ce"Ni dai ga abin da na faÉ—a miki nan, ra'ayinki ne ki ji ko ki yi watsi da shi".

Daga haka ya kashe wayar, na runtse ido ina jin kamar zan yi ihu, na rasa manufar wannan takunkumin da yake saka min, mutane suna yawan faɗa min idan mun yi aure ba ƙaramin kulle zai yi mini ba, ana ta nuna min takaicin da matar kulle take ƙunsa, amma ni gani nake indai mijina yana sona yana faranta mini muna zaune lafiya kuma zai ɗauki duka ɗawainiyata mene ne don ya yi mini kulle? Idan aka cire wannan dokokin da yake kafa min wallahi yana da daɗin sha'ani ya iya nuna soyayya da kalaman kulawa, a takaice dai gani nake ni ce na fi kowa dacen mijin aure.

Ban ajiye wayar ba na ji shigowar saƙo, na duba na ga alert ne daga gare shi, na dubu hamsin, wani saƙon ya sake shigowa, na karanta faɗa min yake yi kuɗin gudunmawa ne na bawa Anisa, na tura masa da saƙon godiya, anko kala biyu aka fitar a bikin, kuma duka shi ya siyo min, ya kawo min a ɗinke kowanne da kalar takami da jaka da zai dace da shi, har da mayafai da set ɗin sarƙa mai kyau sosai, sannan ya haɗo min da dubu goma ya ce na yi liƙi, ban taɓa kuɗin ba, Baba na tambaya ya cika min na siyawa Anisa wani Jug me kyau na bata. Mama ta tafi gidan bikin tun asuba, sai ƙannaina da suke gab da gama shiryawa, dama umarni nake jira tun da na samu izini ni ma tuni na tashi na shiga wanka, na ce su jira ni, muka tafi tare, Na samu Mama na faɗa mata zancen kuɗin da ya ba ni na bawa Anisa, ta ce na ba ta dubu ashirin na bawa babarta talatin ɗin, na fita na je na ciro na bawa Umma na ce inji Sadam, nan fa aka dinga jinjina ƙoƙarinsa ana godiya, har na ji daɗi a raina, ya kankaro min mutunci.

Na samu Anisa a ɗakinta cikin ƙawayenmu na makaranta, ta kalle ni ta kau da kai, na faɗa jikinta ina dariya da faɗin"Allah Ya huci zuciyarki". Da ƙyar ta sauko daga fushin, na ciro kuɗin na ba ta na ce inji Sadam, ta taɓe baki ta ce"Ai ni ko miliyan zai ba ni bai burge ni ba, kuma ba na so ki mayar masa".

Na sauke numfashi ina tunanin ko ya za ta ji idan ta san ba zan je kai amarya ba? Kafin dai yamma ta yi ta saki jiki da ni, ta karɓi kuɗin har ma ta yi masa godiya ta wayata, kafin mu yi sallama ya sake jaddada min bayan magriba na dawo gida, na ce to, ai kuwa ana idar da sallar magriba na zame daga cikin 'yan biki na shiga ɗakin Umma na haye gado na lulluɓa da mayafina, kowa ya shigo sai ya tambaya sai na ce ba ni da lafiya, a dole Mama ta saka ni a gaba muka koma gida, raina babu daɗi saboda na so a ce na raka ƙawata ɗakinta.

A haka muka cigaba da soyayya, yana nan yana kafa min dokoki ni kuma ina ta biyayya saboda gudun ɓacin ransa, idan na kuskure na ga tijarar da har sai na yi nadamar aikata laifin. Ko da wasa wani saurayi ya tsayar da ni a hanya ce masa nake ni matar aure ce, don kada ma tsautsayi ya sa a ce masa an gan ni da wani na shiga uku. Kwanci-tashi aka samu wata biyar da saka rana, arenmu ya rage watanni uku, a lokacin ne kuma Sadam ya fara fito mini da wasu sabbin halaye wanda na kasa gane musu, zuwa lokacin ya siya min babbar waya muna yin chatting, kuma mun fi yin na dare, saboda ya ce sai daren yake da lokaci, ya fara da tura min stickers na kiss da hug, da na nuna ba na so sai ya nuna min ba komai ba ne, ni kuma sai na yarda da babu komai ɗin, tun da ba wani tsaraici ba ne ake bayyanawa, gaba-gaba kuma sai ya fara tura min ta romance, babu kunya sai ya turo min hoton ƙinjin mace, har ma ya dinga tambayata nawa irin wanne ne? Tun ina ƙin amsa masa har dai na fara, saboda gudun ɓacin ransa, kuma yana maimaita min don yana sona ne yana tare da ni, wai idan bai tura min ba wa nake so ya turawa? Sai ka ce dole aka yi masa sai ya turawa wata.

A ranar da ya fara tura min blue film hankalina ya tashi, saboda ban taɓa kalla ba ko da wasa, kuma na kasa jurewa har sai da na faɗa masa ba na so kar ya sake tura min, kashe wayar ma na yi sai da na yi kwana uku ban kunna ta ba, har ji nake yi kamar zan yi zazzaɓi, a cikin kwanaki ukun bai zo ba, a rana ta huɗu na kunna wayata ban ga saƙon shi ba, ban sani ba ko ya kira ni, gaskiya ya ɓata min rai kuma na fara zarginsa ma, idan ba yana yawon bin mata ba waye yake tura masa? Wata zuciyar take ƙila ɗakkowa yake yi a internet, ina kallon shi online bai yi min magana ba, sai na kasa jurewa ni na yi masa sallama, ya amsa ya ce lafiya? Na ce lafiya ƙalau, sai ya danna voice note ya ce min"Sayyada ba lafiyar jikinki nake tambayarki fa, tambayar dalilin yi min magana nake yi".

Na ce"Yanzu sai da dalili zan yi wa mijin da zan aura magana?"

Ya ce"To ai ba ki É—auke ni a matsayin wanda zai aure ki ba, ban da haka kawai don na tura miki vedio shi ne za ki kashe waya? Kenan idan da zan ce ki zo ki taya ni wuni ba za ki amince ba ko?"

Na yi shiru na rasa me zan ce masa ma, amma na shiga fargabar me Sadam yake nufi da ni?

Ya sake yin voice ya ce"Na rasa irinki wallahi idan kina wani abu kamar haihuwar ƙauye, ban da shirmenki mene ne a cikin wannan? To gaskiya ni ba zan iya soyayya da mace irinki ba, ballantana kuma aure, don irinki idan mutum ya aure ki ma takaici zai kwasa wallahi, don haka kina da zaɓi guda biyu, ko ki koyi yadda za mu dinga gamsar da juna ta haka ko kuma a fasa auren nan kawai, sai ki je ki nemi ustaz ki aura tun da na ga ni kallon ɗan iska kike yi mini".

Kamar zan yi kuka na ce"Ni fa ba haka nake nufi ba".

Ya kira ni a waya, ina É—auka ya ce"Ki buÉ—e baki ki yi mini bayanin me kike nufi? Wane kallo kike yi mini?"

Na ce"Ba komai wallahi, kawai dai ni na tsorata ne, ba na son gani".

Sai ya sanyaya murya ya ce"To me kike so?"

Na ce"Da dai za ka daina turo min".

Ya ce"Kina so na turawa wata kenan ko? Idan ba mu saba da wacce zan aura ba tun yanzu sai yaushe? Ko so kike sai bayan auren na dinga fama da koya miki abubuwa? Ni ba haka na tsara ba, amma ba zan yi miki dole ba shi yasa na ba ki zaɓi".
Chapter 8 · 0% Book details