Sashe 58
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce"Subhanallah, abun bai kai haka ba Assayyada, kuma yanzu rayuwa ta canza, na wuce wannan wulaƙancin in sha Allah, gaba kaɗan zan auri kamar ki biyu a rana ɗaya, ke kuma Allah Ya ba ki kalar wanda kike so".
Na amsa da Amin, ya yi min sallama ya tafi, tun daga ranar kuma idan ya zo ba ya ganina ɗan kawai yake gani ya tafi, ana jibi suna 'yan'uwan shi suka kawo kayan barka, sun yi ƙoƙari ba laifi, ni ma sun haɗo min da atamfa guda biyu, sannan dangina ma sun yi mana kaya ni da Dawoud, amma duk da haka sai da na ciri kuɗi na bawa ƙanwata Khadija na lissafa wasu abubuwan da nake so, ranar suna Ustaz ya kawo rago babba, don mahaifin Rauda ne ya ba shi kyautarsa, duk yadda ya yi da Rauda ta je barka ta ƙi, saboda da gaske take kishinsa, tana ta rainon cikinta ita ma, zuwa yanzu har ta fara sabawa da halin Ustaz na mammaƙo, ta riga ta gane ƙarya kawai yake yi ba wata ulcer da ta hana shi cin wasu abubuwa, don haka idan tana son cin abu sai ta siya da kuɗinta ta daga ta ci, saboda kar ta mora ta koyi taune ƙashi ta tsotse, tun da ta gane idan ta ci nama dare yake bi ya taune ƙashin.
Ita dai tana son shi, don haka ta ga za ta iya daurewa ta zauna da shi, musamman yanzu da ta zama irin jinsin shi, ƙarfi da yaji ya mai da ita wata ƙaramar harija, dole ne yanzu kullum sai ta neme shi, wataran ma sai biyu a rana, shi yasa Ustaz bajau da shi.
Tun da aka yi taron suna 'yan barka suka ɗauke ƙafa sai na samu kaɗaici, don ma dai kullum sai mun yi waya da Sadam da daddare, da rana ma idan na ga Mama ta yi bacci muna yi, ko mu yi chatting, hankali kwance muke farfaɗo da soyayyarmu tare da gina ta da wasu kayan aiki masu ƙarfin da rushe wannan soyayya zai yi wahala, muna ta samun shaƙuwa da shi.
Sanda na yi arba'in zan je kai Abiy allura, Sadam ya ce ya kamata mu haɗu, ban yi musu ba saboda ni kaina ina kewar shi, ina son ganin shi a zahiri mu gana, ranar na yi kwalliyar da rabona da yi tun ranar suna, na goya ɗaya, na yafa mayafi na tafi asibiti, ina cikin asibitin ya kira ni ya ce ya ƙaraso yana ƙofar asibitin, da na gama na same shi a tsaye a jikin motarsa, sai ya shiga, ni ma na buɗe na shiga, ya ja motar muka fara tafiya, na kalle shi na ce"Ina za mu je?"
Ya yi murmushi ya ce"Siyar da ke zan yi".
Na yi 'yar dariya na ce"Ai ni ba zan saidu ba".
Ya ce"To mu je gidana ki rage min zafi, ganin ki ya birkita ni".
Fara'ar fuskata ta ɗauke, raina kuma ya ɓaci.
Ya ce"Saki fuskar Babyna, wasa nake yi miki, amma da gaske fa a yanzu ke kaÉ—ai nake gani ki birkita min lissafi na ji ni namiji ne".
Na ce "To na ji a bar zancen".
Ya ce"An bar shi".
Ya karkata motar muka shiga wata unguwa, ya samu wajen wata bishiya ya yi packing, ya kashe motar ya kalle ni yana murmushi ya ce"Sayyadata, ya garin?"
Na ce"Lafiya lau".
Ya ce"Na ji daÉ—in ganinki sosai fa".
Na ce"Ni ma haka".
Ya ce"Sai yaushe za ki yaye yaron naki?"
Na ce "Ai da saura, a ƙalla dai ya yi wata sha shida".
Ya yi tsaki ya ce"Gaskiya ya yi tsayi, gabaÉ—aya wannan É—an iskan harijin ya canza min lissafi, kuma ke ce kika bawa abun goyon baya".
Na ce"Haka Allah Ya tsara, ka daina cewa haka".
Ya ɗaga kai yana kallon saman motar, yaron ya fara 'yan ƙananun kuka, na sauke shi, Sadam ya kalle shi ya taɓe baki ya ce"Ɗan ƙaddara kenan".
Maganar ta zo min a bazata, kuma ta yi min zafi, sam ban ji daɗi ba, amma na maze ban ce komai ba, na saka shi a kafaɗa ina rarrashin sa amma ya ƙi yin shiru, da alama dai yunwa yake ji, a dole na sauke shi na ɗora a cinyata na fara shayar da shi bayan na lulluɓe shi da mayafina, kunya duk ta kama ni.
Ban san kallona yake yi ba sai da na ji ya ce"Abin da kike rufewar wane ne baƙon shi? Indai ba canza ki aka yi ba ai kin san ni na fara sanin shi ko? Idan ma za ki jiki ko buɗe ki saki Malama".
Wannan yana daga cikin dalilin da ya sa na tsara ba zan yi soyayya ina shayarwa ba, tun da dole yaro zai buƙaci abincinsa, shayarwa a gaban wanda ba mahaifinsa ba kuwa yana iya haddasa abubuwa da dama, na yi shiru kamar ban ji shi ba, shi ma bai sake cewa komai ba, har yaron ya ƙoshi, na saka shi a kafaɗa, ya sauke numfashi ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Don Allah ko da lokaci ya yi idan aka hana ki aurena kar ki yarda, saboda idan ba ko aure ni ba zan cutu".
Na ce "Ni ma zan cutu sosai, in sha Allah ma ba za su hana ba, amma ka yi haƙuri idan sun hana mu haƙura kawai, saboda na yi alƙawarin ba zan sake saɓawa iyayena ba".
Ya ce"Ok".
Muka taɓa fira, ina ta jijjiga ɗana, amma Saddam ko ya ce ya sunan shi ballantana ma ya ɗauke shi, ban ji daɗin haka ba, har muka rabu bai ɗauki ɗan nan ba.
Na tari adaidaitasahu na koma gida, zuciyata fara ƙal saboda na ji daɗin ganin shi, sai na ji na ƙagauta wata allurar ta zagayo saboda mu sake irin wannan haɗuwar.
08028966015
[03/11, 7:29 pm] Sadiya Abdulrazak: 35
Idan Ustaz ya bushi iskar shi yana zuwa ya ga ɗan shi, har ma ya ba da kuɗi ya ce a siya masa pampars, ina nan ina ɓoyayyiyar soyayyata da Sadam, watarana ina zaune Mama ta ɗakko wayata ta ba ni, ta ce"Ga wayarki nan Sayyada, zan saka babanku ya siya miki sabon layi, ruwanki ne ki cigaba da shashancin da ba zai amfani rayuwarki ba, ruwanki ne kuma ki nutsu ki san inda yake yi miki ciwo, ki kawo miji ko wane ne, amma ban da Sadam, ba za ki aure shi ba indai ina raye".
Zuciyata ta tsinke, idona ya kawo ruwa amma ban bari ya sakko ba, babban kalmar da take rusa nutsuwata ita ce ba zan auri Sadam ba, haka na karɓi wayar na ajiye, washegari Baba ya kawo min sabon layi, sai na fara amfani da wayar ina rabawa mutane lambar, tun da ita ta wajen Sadam da shi kaɗai nake magana.
Da lokacin komawa kai Abiy allura ya yi, muka sake shirya haɗuwa, muka yi kamar yadda muka yi a wancen lokacin, muka sha firarmu a mota, a wannan karon ma nunawa ya yi kamar bai ga ɗana ba, na kasa haƙuri sai da na ce"Ba ka ga Abiy ba wai? Ba ka taɓa ɗaukar shi ba".
Ya yi gajeren tsaki ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Bari na faɗa miki gaskiya, da ina da ikon goge sunanki daga mahaifiyar yaron nan da na yi, ba ni da alaƙa da ɗanki ta kusa ko ta nesa, don haka ke nake so ba shi ba".
Na yi mamakin maganarsa, kuma ban ji daɗinta ba, na ce"Amma ai an ce maso uwa ya so 'ya'yanta, Sadam ya kyautu ka ce ba ka da alaƙa ko ta nesa da shi? Daga jikin wacce kake so fa ya fito, jinina ne".
Ya taɓa baki ya ce"Amma dai kin san ba a so dole ko? To idan dole za ki yi min na so shi sai ki buɗe zuciyata ki saka min, ba na son duk wani abu da zai saka na tuna kin yi rayuwar aure da wani ba ni ba".
Na ce"Amma yanzu kenan ko aurenmu muka yi ba za ka riƙe min ɗana ba?"
Ya ce"Gaskiya dai, ko da ubansa ba ya raye sai dai a bawa dangi shi, ba zan riƙe agola ba".
Da mamaki na ce"Amma idan ka rabu da matarka fa? Kenan ba za iya ba ni riƙon 'yarka ba?"
Ya ce"Ya zama dole ki riƙe, kamar yadda ya zama dole matar uban ɗanki ta riƙe miki ɗa, ni kalmar agola ce ba na so, kowane ɗa ya fi kyau da gidan ubansa, ko ba ki an ce da uba ake ado ba? Kuma kyaun ɗa ya gaji ubansa".
Jikina duk sai ya yi sanyi, hankalina ya fara tashi, don ni a shirina da ɗana zan tafi duk inda zan je, na sauke numfashi na ce"Wannan tsarin naka ba shi da wata alaƙa da kalmar da uba ake ado, shikenan Allah Ya zaɓa abin da ya fi alkhairi".
Na buɗe murfin motar zan fita, ya riƙo hannuna, na dakata na juyo na kalle shi, ya ce"Wai fushi kika yi?"
Na ce"A'a".
Ya ce"Fushi kika yi mana, amma na yi mamaki kuwa, da kika ce Allah Ya zaɓa abin da yake alkhairi me kike nufi? Kenan za ki iya fasa aurena don na ce ba zan riƙe ɗanki ba?"
Na ce"Ba zan fasa aurenka bisa wannan dalilin ba, tun da ai kana kan gaskiyarka ba hakkinka ba ne ka riƙe shi, sai dai sam ba ka yi min kara ba Saddam".
Ya ce"Ki yi haƙuri, na kasa sarrafa kishina ne, ina son ki Sayyada, kallon yaron zai dinga tunzura kishina, wallahi ƙiyayyar da na yi wa baban shi za ta shafe shi na zo ina cutar da shi, kin ga maganin kar a yi kar a fara ko?"
Na jinjina kai na ce"Hakane, zan tafi".
Ya ce"Ba za ki tafi ba, sai kin huce, na ga kin É—auki fushi da ni".
Na ce"Zan huce daga baya, ai na daina dogon fushi da kai".
Na yi ƙoƙarin zame hannuna da ya riƙe, ya ƙi saki, na juyo na kalle shi, idanunsa suka karantar da ni yanayin da ya shiga, tun da ba yau na san shi ba, na ce"Sake ni Sadam kar Mama ta ga na daɗe".
Ya ce"Hannunki ya rage laushi, me yasa?"