Sashe 79
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na girgiza kai da sauri"Wallahi bai rage ni da komai ba, kuma bai yi shawara da ni ba kawai kuɗin na gani, ku yafe min, tabbas ni ce na janyo Saddam rayuwata, ga shi baƙincikinsa yana ta bibiyata, ku saka baki kar aurena ya mutu, ya fusata sosai".
Mama ta ce"Ke ce kika ja komai, kai sanin wannan Saddam bai yi mana rana ba".
Ta tashi ta bar ɗakin, na yi jugum abun duniya ya ishe ni, wajen azhar na kira shi bai ɗauka ba, na tura masa saƙon ban haƙuri da jam'un da yake ƙauna, bayan la'asar ma na kira shi nan ma bai ɗauka ba, duk na shiga damuwa, na dinga bin shi da massages amma shiru.
Da Baba ya dawo Mama ta sanar da shi halin da ake ciki, sai ya yi shiru ya ƙi cewa komai saboda takaici, ba tun yau ba na gama yarda da cewar duniya za a daɗe ba a samu maƙiyin Saddam da ya kai Baba zafafawa.
Wasa-wasa sai da aka yi kwana biyar cif mai martaba bai zo ba, kuma ba ya ɗaukar wayata, tun ina yi masa saƙon har na gaji na rabu da shi, don ni ma na yi fushi, na fara tunanin ba sona yake yi ba, idan har kishi ne ai ya ci a ce ya sakko ya yafe min, tun da ba ni ce na yi masa gorin ba. A rana ta shida sai ga shi ya zo gidanmu, babu zato babu tsammani, farinciki ya kama ni, amma na yi burus ban nuna ba, saboda ya ba ni haushi, sai ga shi bai ma neme ni ba, da Baba kawai ya yi magana ya yi tafiyarsa, hakan kuwa ya ƙara ɓata min rai, ga shi duk yadda na so na cire shi daga raina ya daina ba ni haushin na kasa.
Bayan ya tafi Baba yake faɗa min gobe na shirya za mu je inda Saddam yake, iyayen shi ma za su je a yi zama na ƙarshe, na ce to, a raina ina fatan Allah Ya sa ƙarshen wahalata kenan, don wallahi ni ake wahalarwa a wannan lamarin, na matsu na gan ni a ɗakina.
Washegari muka shirya, Isma'il ya zo ya ɗauke mu ni da Baba, ina gidan gaba Baba yana baya, da na gaishe ya amsa a daƙile, har muka je ba mu sake magana ba, a can muka tarar da mahaifin Sadam yana jiranmu, aka ba mu wajen zama, aka fito da Sadam, ina kallon shi na san ya sha wuya, don ga duka nan a jikinsa ɓaro-ɓaro, duk ya yi zuru-zuru, don kwanakin da ya yi bai yi shaye-shaye ba duk ya rasa nutsuwarsa, kuma wannan karon da alama ya yi laushi, sai dai yana ta ɓata rai, baban shi yana ganin shi ya fara salati, ya ce "Sadam, yanzu rayuwar da ka zaɓawa kanka kenan ko? Kai fa Musulmi ne ka san ƙaddara indai imaninka ya cika, kana da hankali kuwa za ka dinga bibiyar matar wani?"
Sai ya fara hawaye, yana sharewa da sauri, da alama dai bai so ya yi kukan ba fin ƙarfinsa hawayen ya yi, ya ce"Ka yi haƙuri Abba, su ma su yi haƙuri na bar ta in sha Allah".
Isma'il ya ce"A'a ban yarda, ƙarya yake yi, wannan yaron tantiri ne, a dai yi maganar da za ta saka na yarda ya bar matata har abada, saboda wallahi ya sake yunƙurin shiga gonata sai na ba shi mamaki".
Baban shi ya ce"Ka yi haƙuri Alhaji, shi wannan yaron ba lallai yana cikin hayyacinsa ba, ya shiga matsala ne, ya yi aure, matar ta shi ashe karuwa ce, kuma iyayen bogi ta nuna aka ɗaura aure, rana ɗaya ta bugar da shi da kayan maye, ta kwashe duka kuɗin account ɗin shi, yanzu case ma yana kotu don gidan da yake ciki ma ta siyar da shi, sannan ta zubar da ciki ta saka ɗan tayin a kwali ta ajiye masa, ya shiga tashin hankali sosai, shi ne ya kasa tawakkali ya fara shaye-shayen nan, kuma shi a kullum cewa yake alhakin Sayyada ne, shi ne yake so ta yake masa kuka a haukansa wai ta kashe aurenta ya aure ta, so ne ya ja hakan wallahi, yanzu gidan da ya ce ya bar mata shi kaɗai ne ya rage masa, amma ya ce shi ya riga ya bar mata, kuɗin hayan ɗari shida ne, don ba shi da kuɗi ne ma ya ɗauki dari uku ya ba ta ɗari uku, saboda na rufe ba shi kuɗi na dakatar da shi daga duk kasuwancina, saboda yanayin maye da yake ciki, mun san ya yi kuskure amma ina mai ba ku haƙuri a madadinsa in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, ni daga nan ma gidan gyaran hali zan kai shi a raba shi da wannan shaye-shayen".
Baba ya ce"To shikenan Allah Ya rufa asiri, amma lallai-lallai a sake gargaɗar shi, babu shi babu yarinyar nan, kuma batun gida ta yafe, ya riƙe abun shi, Allah Ya ba da ladan niyya".
Baba ya kalli Isma'il ya ce"Ka yi haƙuri, shikenan a bar batun".
Ya ce"To ya ba da account a mayar masa da kuÉ—insa".
Baban Saddam ya ce"Ai ya riga ya ba ta, babu damuwa a bar shi kawai, Allah Ya saka musu albarka".
Isma'il ya ce"Babu wata albarka, kuma ai ba rasawa ta yi ba, don haka ku ban account kawai".
Baban ya ba shi nashi, ya karɓi yawar Sayyada ta mayar masa da kuɗinsa, aka ce Saddam ya ba shi haƙuri, Sadam ya ce"Ka yi haƙuri in sha Allah ba zai sake faruwa ba, Allah Ya ba ku zaman lafiya".
Ba tare da ya kalli inda Sayyada ta ke ba ya ce"Ke ma ki yi haƙuri ki yafe min, cutarwar da na yi miki a haɗuwarmu tun farko har zuwa yanzu, na yaudare ki, na saka ki bijirewa iyayenki, sannan ni ne nake korar wanda ya fito neman aurenki da labarin abin da kika yi min kafin rabuwarmu, ni dai na yafe miki komai".
Na ji wani dumm! Na cika da mamakin wai shi ne yake korar manemana dama? Hawaye ya kawo idona kawai yadda na daɗe da zargin Anisa a raina ne ya faɗo min, ashe na cutar da ita, ashe masoyiyata ce ita, ƙoƙari take na samu miji na yi aure, amma shi ne har ta haɗa ni da mijin nunawa sa'a irin Isma'il ban daina fushi da ita ba, bisa zargin a baya ta cutar da ni, ashe duka Saddam ne, kai amma Saddam ya daɗe yana gana min azaba da sunan soyayya.
Na ce"Na yafe maka har zuciyata".
Na kalli Isma'il na ga ni yake yi wa kallo mai kama da harara.
Sannan aka yi nasiha aka ce a yafi juna, kowa ya yafe taron ya watse kowa ya kama gabansa.
Da muka dawo gida, Baba ya fita daga mota ni na ƙi fita ina jira mu tattauna, ya ce"Me kike jira?"
Na ce"Ka ƙara hakuri".
Ya ce"Ai na yi".
Na ce"To yaushe zan koma? Zaman wankan ya isa haka".
Ya ce"Lokacin da kika so".
Na ce"Wai kenan har yanzu fushi kake yi da ni? Ka yarda ina da laifi?"
Ya ce"Ba fushi ba ne, kishi ne, kishinki ne kamar ya fasa zuciyata, wannan yaron ya cuce ni fa, ba zan manta da wannan gorin da ya yi min ba".
Na ce"Don Allah ka yi haƙuri, kuma na yi maka alƙawarin zan mantar da kai wannan gorin a ranar da na dawo, kai da kake da ni har abada? Ka san tsayin lokacin da za mu shafe tare kafin mutuwar ɗayanmu? Don Allah ka manta".
Ya sauke numfashi ya ce"To gobe zan zo mu tafi ko?"
Na ce"To ka zo da yamma, saboda akwai abubuwan da zan yi".
Ya ce"Ok, Allah Ya kaimu".
Na fita, ya ja motar ya tafi, anjima kaɗan na ga alert ya turo min dubu ɗari uku, na tafi gidan Anisa, na dinga ba ta haƙuri har da kukana, na faɗa mata zargin da nake yi mata, ta ce ta yafe min kuma ta yi min uzuri, na ciro kuɗi ta raka ni kasuwa muka yi siyayya, muka wuni muna yin aikin kayan fulawa, wanda zan yi na tsarabar komawa ɗakina.
*Masoyan Ustaz next page naku ne, ina can ina fafutukar shawo kan Ruky baby ne*
08028966015
[17/11, 3:51 pm] Sadiya Abdulrazak: 47
USTAZ
Zamansu ƙalau da Rauda, suna gamsar da juna, duk da shi yana ta ƙoƙarin ragewa ne saboda kar ya ƙureta ta gaji ta rabu da shi ta shiga uku, don yanzu ya gama yarda idan ba Rakiya ya aura ba samun wacce za ta zauna da shi ta karbi larurar shi abu ne mai wuya, sai Rauda ɗin, siyasa ma ya yi wa kansa faɗa ya rage matsolancin sosai, Alhamdulillah yana wadata gidan da komai yanzu, tun da yana samu daidai gwargwado, idan ya yi tafiyar sati ɗaya ko biyu ya dawo kamar za su cinye juna shi da Rauda, shi yasa suke ƙara jin ƙaunar juna, a nasu ɓangaren dai komai daidai.
Ana haka kuma sai ga wata sabuwa ta ɓullo musu, Rakiya ce ta yi karatun ta nutsu, ta ga tun da dai ta rasa mijin aure ne zai hana ta yi maneji da Ustaz? Tun da yana ƙaryar shi hariji ne sai ta yi haƙuri da kishiyar, indai zai biya mata buƙata ranar kwananta, sai ta haƙura da fashin kwana ɗaya, tun da Hausawa sun ce maraina kaɗan zai haƙura da babu, za ta iya ƙin auren shi saboda yana mata, ta je ta auri mara matan kuma ta samu lusari ne, don haka ta faɗawa wacce aka bawa cigiya ta amince da auren, dama wata Hajiya Ladidi ce wacce ake yi wa laƙabi da mai dalilin aure.
Ustaz yana zaune ƙalau Umma ta kira shi ta ce ya zo tana son magana da shi, da daddare ya je, bayan sun gaisa take faɗa masa Rakiya ta ce ta amince da auren nan, don haka ya shirya a tura neman aure, Ustaz ya fara salati ya ce"Subhanallah, amma Umma gaskiya dai da an rabu da batunta, ni ina zaune lafiya da matata, kuma ban nemi komai na rasa ba, bi ma'ana dai ba na buƙatar ƙari".