← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 89

Sashe 56

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalina duk ba a kwance ba har aka gama yi min awo, tun ƙarfe takwas nake asibitin dai sha ɗaya na gama, na yi mamakin ganin har yanzu motar tana wajen, na sake zuwa na ƙwanƙwasa shiru ba a buɗe ba, sai na yi tunanin ko ya ajiye motar ne ya tafi wani wajen, na nemi waje na zauna a gefe da ƙudurin ko zan kai magriba sai na jira dawowar shi, ban can wajen sha biyu da mintuna sai ga wata mace ta zo ta tunkari motar, gabana ya faɗi da na gane kenan jiranta ya zauna yi shi yasa ya ƙi buɗe mini? Na tashi bisa shawarar zuciyata na ƙarasa wajen motar, daidai lokacin da ta shiga mazaunin direba ta zauna, zuciya ta raya min matarsa ce, duk da ban santa ba, ban kuma tabbatar ba, na ce"Safna".

Ta juyo ta kalle ni, nan take ta haÉ—e rai sosai, ta fito daga motar ta ce"Lafiya? Bashi ko tara?"

Na ce"Babu É—aya".

Na juya zan tafi, ta janyo hijjabina na dawo baya, ta ce"Uban me ya kawo ki asibitin nan, bibiyata kike yi?"

Na yi dauriya matuƙa ban sharara mata mari ba, na fizge hijjabina na ce"Ke ba ki kai wacce zan bibiye ki ba".

Ta yi dariyar rainin hankali ta ce"Amma mijina wanda yake bibiyata ya kai ko?"

Ban ce komai ba na bar wajen da sauri, ina ji tana ta zagina ko juyowa ban yi ba, zuciyata sai zafi take yi min, wani kishin da ya taso min ganga-ganga, kenan dai idan na fahimta ya bar mata motarsa ne? Ashe ni ce nake ta haukana shi yana can yana farantawa matarsa, na share hawaye da suka sakko min, na fita daga asibitin na hau adaidaitasahun na koma gida, na ci sa'a Mama ba ta yi min magana a kan daɗewata ba, ranar haka na wuni kamar mara laka, kawai na saddaƙar ni kaɗai nake son Sadam, shi matarsa yake so, a fili na furta "Allah ka yi min zaɓin alkhairi ka cire min ƙaunar wannan bawa naka mara adalci".

Tun daga ranar nake ƙoƙarin mantawa da shi, amma na kasa, dabara ɗaya na samu idan na fara tunanin shi sai na ɗakko Qur'ani na fara karatu, kuma Alhamdulillah ina samun samun sassauci sosai.

Ranar da zan koma asibiti haka na dinga fargaba da fatan Allah Ya sa kar na haɗu da Safna, a dole na saka niƙabi, kuma Allah Ya karɓi addu'ata ban ganta ba, amma na ga motar Sadam ɗin.

Haka rayuwa ta cigaba da miƙawa, cikina yana ƙara girma, har na shiga watan haihuwata, ina ta lissafin EDD ɗina, da Mama ta sanarwa Baba na shiga watan haihuwata, sai ya kira Ustaz a waya ya faɗa masa, Ustaz ya ce"Alhamdulillah, ma sha Allah, Allah Ya raba su lafiya, to Baba idan ta fara naƙuda sai a yi gaggawar sanar min, saboda na zo a yi komai a gabana, bi ma'ana shi yaron ko yarinyar idan an haifa kafin wasu mintoci akwai addu'a da nake so na fara yi masa, kafin ma a kai ga huɗuba, sannan me ake buƙata na kawo kafin haihuwa"

Baba ya ce"Ba a buƙatar komai, na faɗa maka ne don kana da hakkin sani, ban sani ba ko za ka tanadi kuɗin hakika da sauransu".

Ustaz ya ce"Za a samu in sha Allah, ai Baba yanzu Alhamdulillah ana samu daidai gwargwado, sai dai kuma ita Sayyada lambarta ba ta shiga idan an kira ta, ko za ka faÉ—a mata ina son magana da ita?"

Baba ya ce"Me kake so ka faÉ—a mata?"

Ya ce"Dama wai ina so mu yi shawara ne na kayan Baby da ale siya kafin haihuwa idan kuma kuÉ—in zan bayar sai na bayar".

Baba ya ce"Ba dole sai kun tattauna ba, ka yi komai iya ƙarfinka".

Ustaz ya ce"La ba'asa, a huta lafiya Baba".

Suka yi sallama, na sauke numfashi, na ji daÉ—i da Baba ya hana ya yi magana da ni, saboda ba zan ma iya ba, tsakani da Allah na tsani Ustaz ba kaÉ—an ba, har yanzu ina jin zafin shi.

Kwana biyu da yin wayar nan da shi, sai ga mahaifiyarsa da yayarsa sun zo gidanmu, aka gaisa a mutunce, suka ba da leda mai ɗauke da kayan Baby, duk kayan da za a buƙata kafin dai a san mace za a haifa ko namiji, muka yi godiya suka tafi suna Allah Ya raba lafiya.

Cikina ya yi nauyi sosai, har na wuce EDD ɗina da kwana uku, ƙafafuna duk sun kumbura, duk yadda Mama ba ta so na fita amma yanzu ita take cewa na dinga fita ko da daddare ne ina zagayawa, amma sam ba na iyawa, kunya nake ji a gan ni da ƙaton ciki, amma a cikin gida kam ina shan zirga-zirga, da safe idan na karya na gama gyara gida ba na zama, na yi ta zagaye kenan daga farkon gidan zuwa ƙarshen shi, na kai na dawo har sai na ji na gaji, sai na zauna na huta, na cigaba, haka zan ta yi har sai lokacin girkin rana ya yi sai na taya Mama, idan na ci na yi wanka na yi sallah na yi bacci, bayan la'asar zan cigaba har sai magriba ta kawo kai, sannan da daddare a ɗakina ma ba na zama zan ta yi har sai na fara jin bacci.

Wata rana na je awo na gama komai na fito na haɗu da Sadam a bakin ƙofar asibitin yana shirin shigowa, da alama shi ma bai tsammaci gani na ba, don na ga ya yi turus ya dakata da takun kamar yadda na dakata, muka shiga kallon kallo, zuciya ta raya min yanzu fa matarsa ya biyo saboda tsabar so, nan take haushi da kishi suka turnuƙe ni, na fizgi sagaggun ƙafafuna na fara jansu sharf-sharaf zuciyata na zafi, na yi zaton zai biyo ni mu tattauna, amma da na juyo sai na ga har ya shige, na sake jin wani rauni ya rufto min, da gaske Sadam ba ya sona, ina adaidaitasahu ina share ƙwalla, ina komawa gida kuma na fara jin alamun naƙuda, zuwa azhar ciwon ya fara kankama, Mama ta kira Baba ta faɗa masa, ya dawo gida muka tafi asibiti, sai bayan magriba na haifi ɗana namiji mai kama da baban shi, ina kallon fuskarsa a raina na ce'Allah Ya da kar ka yi halin mahaifinka'.

Ina ɗakin hutu ina shan shayi, na san dai an tafi da yaron waje, amma na yi zaton Baba aka Kai wa ya gan shi, ashe Ustaz ya zo tun kafin na sauka, sai ga shi ya shigo riƙe da yaron ya a murmushi, na haɗe rai, ya kalle ni ya ce"Sannu Assayyada, ya jikin naki?"

Zuciyar musulunci ce kawai ta sa na daure na ce"Da sauƙi".

Ya ce"Ma sha Allah, Allah Ya ƙara lafiya, na gode sosai Assayada, ashe ke ce za ki kawo min ɗana na farko? Alhamdulillah, wannan yaro ɗan gata ne, domin kuwa nan da wasu watanni za a yi masa ƙani ko ƙanwa, bi ma'ana yanzu haka matata tana da ciki a jikinta, kin san na yi aure kuwa?"

Na ce"Malam ka yi abin da ya kawo ka kawai ka ajiye shi ka tafi".

Ya ce"La ba'asa, Assayyada ba za ki canza hali ba ko? Ai kuwa ba fata nake yi miki ba za ki sha wahalar zaman aure, yanzu kin kammala iddarki Kenan na taya ki baƙinciki, sannan idan kin ga za ki koma ɗakinki ƙofa a buɗe take, duk da dai sai kin sha daga da matata, bi ma'ana Rauda tana sona tana kishina".

Na yi tsaki na kau da kai gefe, ya ajiye É—an yana cewa"Allah Ya raya Dawoud, bi ma'ana na saka masa sunan mahaifina".

A daren 'yan'uwan Ustaz sun zo asibitin sun ga É—a, Mama ta kwana da ni, washegari da safe aka sallame ni daga asibiti, muka koma gida Mama ta wanke mu tass ta gasa min jiki, sai ga Ustaz ya zo tare da babar shi da yar kula cike da naman kai mai romo da robar gurasa, ban yarda Ustaz ya gan ni ba, saboda har ga Allah ba na son ganin shi, duk da ta silar shi na samu cikar burina wato na haihu ni ma na samu gudan jinina.

Kwana uku da haihuwar, da daddare muna zaune da Mama ina cin tuwo ita kuma tana goye da Dawoud muka ji sallama a tsakar gida, gabana ya ba da rass, don ko bayan shekara ɗari muryar Sadam ba za ta ɓace min ba, muƙutt na haɗiye lomar tuwon da na saka a bakinaeba tare da na tauna ba, da alama ita Mama ba ta gane muryar ba, sai ta amsa sallamar tana tambayar wane ne?

"Mama Sadam ne, ina wuni". Ya faÉ—a kai tsaye.

Mama ta zaro ido ta ce"Saddam!?" Tana yi min kallon hukuma.

Jikina ya hau mazari, na fara in-ina da rawar baki na ce"Ban... Mama, wallahi ban san zai zo ba, ba ma waya na rantse da Allah".

Mama ta yi huci mai zafi ta tashi ta fita daga É—akin, ko kallon Saddam da ya rusuna yana gaishe ta ba ta yi ba, ta wuce shi, shi kuma kamar wanda aka yi masa iso ya shigo É—akin da nake
[02/11, 8:00 pm] Sadiya Abdulrazak: 34

Ya zauna yana kallona, na yunƙura zan tashi ya ce"Ina za ki je?"

Na koma na ce"Sadam mene ne hakan? Me ya kawo ka gidan nan?"

Ya ce"Da ke a waje kuma har a tambayi me ya kawo ni? Barka na zo, da kuma nunawa duniya ina jira ki kammala iddarki ne dama, ina fatan na wani É—an iska da ya riga ni ko?"

Na ce"Da ba ka zo yanzu ba, za a zargi akwai wata alaƙa tsakanina da kai bayan mutuwar aurena, sannan a ina ka san na haihu ma? Kuma ba ka tare da ni, da kana sona da za ka fahimce ni ba za ka ɗauki fushi da ni ba, ka nesanta kanka da ni, ni kuma a yanzu ba na buƙatarka ka bari Please ba yanzu ba".
Chapter 56 · 0% Book details