← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 89

Sashe 88

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A haka rayuwar gidan Ustaz ta cigaba da tafiya, duk yadda ya so ya yi sallar dare idan a ɗakin Rakiya yake ba ta barin shi, yana ji yana gani azumin Litinin da Alhamis ma idan a ɗakinta yake ba zai yiwu ya yi ba, saboda karya masa azumin take yi, idan ya ɗauki azumin, da safe yana bacci sai dai ya ji tana lalubar shi, dole azumin ya karye, idan yana ɗakin Rauda ne yake samun sassauci ya samu bacci, tun da ita awa uku ma ya ishe ta, sai dai da safe ma ta sake nema ko na minti talatin ne wataran ma ba ta nema, amma daren nan dai dole ne kawai sai ya yi, idan kwanan Rakiya ya zo gabansa har faɗuwa yake yi, shi bai ma taɓa ganin irinta ba, idan akwai na gaba da harija a halitta to sai dai a ba ta wannan sunan, da ya tsiri yi mata ƙaryar rashin lafiya sai ta ce ai jikinsa ne yake zazzaɓin ba abun ba, don haka ya yi kwanciyarsa ya bar mata aikin za ta iya, to shi Ustaz dama ba wai buƙatar ce ba ya yi ba, kawai yana so ne ya samu bacci ya ba wa gangar jiki hakkinta, amma ba gajiya ya yi ba, don haka abun ba ya yi wa Rakiya wahala, sai ta zama mijin shi matar, ta haye shi ta yi ta abu ɗaya, yau ma haka ce ta faru, tun ƙarfe takwas take ta abu ɗaya, ya baje a katifa ko motsi ba ta yi, bacci yana fizgar shi amma babu damar yi, ga shi washegari da asuba zai yi sammako saboda za su bar garin, zai yi tafiyar sati ɗaya, sanin da ya yi zai huta sosai a sati ɗayan ne ya sa ya rabu da ita take yin yadda ta so, to amma ya ga abun nata ba mai ƙarewa ba ne, tun da yanzu maganar ƙarfe ɗaya ake yi, a sanyaye ya ce"Ke Rakiya anya kuwa ke mutum ce?"

Ta dakata ta ce"Wannan wace irin tambaya ce? Hakkin nawa ne ba za ka ba ni ba ko yaya?"

Ya ce"Ai ke kakan hakki ma na ba ki, ko na ce kina karɓa, tun da ke ba kya jira ma a ba ki, yanzu dai ɗaga ni mu yi magana".

Ta ce"Ai wallahi sai kiran sallar asuba, tafiyar sati É—aya fa za ka yi ban da rashin tausayi ta ya za ka ce na bar ka? Ni wallahi da za ka yarda ma da na bika, ko a zauren wani gidan ne zan iya kwana indai za ka ba ni hakkina".

Takaici ya kama shi, kamar zai yi kuka ya ce"Rakiya ki É—aga ni haka tun da dai ba katako kika samu ba, ba kuma babyn roba ba ne ko na'ura".

Ta ce"Gaskiya sai dai ka yi haƙuri wallahi, na sati ɗaya na zan nema, kuma wallahi duk tsiya idan ka dawo a ɗakina za ka sauka don ba zan karɓi ragowa ba, ni dama shi yasa fa na ƙi aurenka tun farko, don wannan fashin kwana ɗayan ba ƙaramin cutata yake yi ba".

Ustaz ya tattaro ƙarfinsa ya wancakalar da ita, ya tashi da sauri ya sauka daga katifar, sai dai yana tashi tsaye ya zube rigijaa saboda ƙafafuwansa sun sage, ya fara furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifli khairan min ha".

Rakiya ta taho da sauri tan faɗin"Subhanallah! Shi yasa na so ka tsaya mu ƙarasa, mararka har yanzu da nauyinta shi ne dalilin faɗuwar".

Ustaz ya ce"Ke Rakiya bari na faÉ—a miki gaskiya, aurena da ke ba zai yiwu ba, bi ma'ana za ki koma gidanku nan ba da jimawa ba, dalili kuwa shi ne na gano cewa ke ba bil'adama ba ce, don haka ki yi ta kanki na yi ta kaina".

Nan take ta gigice ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yi haƙuri Malam Ashiru don Allah ka rufa min asiri, idan ka sake ni ina zan kama? Wallahi tun da nake yin aure ban taɓa ganin jarumi irinka ba, ka yi haƙuri don Allah, na yarda zan rage".

Ya ce"A'a wallahi Rakiya ki yi ta kanki na yi ta kaina kawai, tun da dai ni ba na'ura ba ne, ke ba alkhairi ba ce a tare da ni, kin hana ni sallar dare wacce na ta zame min jiki tun da kuruciyata, sai yanzu da ya kamata na ƙara ƙarfafa ibada za ki hana ni? Azumin nan kin hana ni yi, ga Ramadan yana tahowa to ya kike so na yi kenan? A'a Matata Raudatu ni ta ishe ni, gaskiya dole na san abun yi".

Ta dinga ba shi haƙuri, ya ce"Ba zan haƙura ba, tun da ke ba ki san zuru ba, awa nawa kika yi kina abu ɗaya? Kin mayar da ni mace ke ce namiji saboda tsabar raini, a wani lusari, ragu kike kallona, ni gaskiya ba zan ɓoye miki ba matuƙar aka cigaba a haka to wataran zan suma kina can kina hidima ba ki sani ba, to ke nan wa gari ya waya idan na mutu?"

Ta ce"Ni ya waya, wallahi ni gari ya waya, tun da na shaida ba zan samu kamarka ba, ka yi hakuri Malam, na yi alƙawari zan rage in sha Allah".

Ya yi banza da ita ya bar ɗakin, ya tafi ɗakin Rauda ya fara ƙwanƙwasawa, ta kira shi a waya ta tambaye shi shi yake bugawa? Ya ce shi ne, ta zo ta buɗe, yana shigowa ta rungume shi tana cewa"Alhamdulillah, dama na kasa bacci, ina tunanin yanzu ko yaya ne ba zan samu ba a daren nan? Ga shi idan ka tafi sai ka yi sati ɗaya, ashe kai ma hankalinka yana wajena, mu je don Allah ka taimake ni I will miss You".

Ustaz ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na guji masifa na tarar da bala'i, to ga ni, ga ni Rauda tunda ke ma kin zama abin da kika zama ki kai ni gadon ki yi min fyaɗe, to ni yanzu ko fyaɗen aka ce za a yi min ma Allah na tuba me za a samu? Babu komai fa waccen jarababbiyar ta ƙarar da ni tass, amma ga ni nan ai, tun da kar ki ga na tauye miki hakki". Ya kunce tazugen shi wandon ya zube a ƙasa.

Jikin Rauda ya yi sanyi, sai ta rungume shi ta fara kuka tana faɗin "Ai ga illar ƙara aure nan ka gani, muna zamanmu lafiya muna gamsar da juna amma ka auro wacce ta fi ƙarfinka, ni dai gaskiya ba zan iya ba, kullum haka kake zuwa ɗakina a gajiye, duk wani zumuɗi ka daina yi a kaina, idan ka ga ba za ka iya ba kawai ka sallami ɗaya a cikinmu, dama ai na san ba zai yiwu hariji ya auri harija sannan ni lafiyayyiya na zauna a tsakiyarku ba".

Ustaz ya ce"To Rauda ke ɗin ma ina kika ga lafiyar? Au ke yanzu jira kike yi wani ya faɗa miki ke harija ce? Da ba ki zama harija ba Rauda ai ke ma za ki dinga sassautawa kanki, ba wai kodayaushe ki ce kina buƙata ba, gaskiya idan na dawo daga tafiyar nan dole ku zauna mu san abun yi kawai, domin ba za ku hana ni neman halak ba, ni idan aka cigaba da tafiya a haka to wallahi ba zan ɓoye muku ba, za ku iya nema na ku rasa, na tafi can wani yankin na dinga ba da fatawa kawai, da rana na yi azumi da daddare sallah da karatun Qur'ani, ai ba dole ba ne kashe arnan, ke akwai ma arna na amana wanda ko a zamanin da ba a kashe su, to na ga wannan zamanin da arnan ma ake rayuwa, ba zan iya ba kowa ya yi ta kansa a to".

Rauda jikinta ya yi sanyi ta ce"Ka yi haƙuri".

Ta kai hannu za ta gyara masa wandon, ya matsa yana cewa"Innalillahi wato Rauda duk bayanin nan da na yi miki ta bayan kunne ya wuce?"

Ta ce"Ni fa gyara maka zan yi".

Ya ce"Ba na so".

Ya shiga banɗaki ya yi wanka, ya kwanta bacci ya ɗauke shi, ita ma ta yi baccin tana ji a ranta ko me za a yi ba za ta yarda a raba ta da mijinta ba, don ta ɗanɗana ba ta ji daɗi ba, to ita ma Rakiya a nata ɓangaren haka take rayawa, ita da Ustaz mutu-ka-raba, domin yanzu ta ga mijin zama.
[21/11, 11:08 am] Sadiya Abdulrazak: ƘARSHE
Chapter 88 · 0% Book details