← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 89

Sashe 86

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙa'ida idan ya dawo wacce ba ita ce da girki ba ɗakinta yake fara zuwa, idan aka gaisa sai ya je ɗakin mai girki, don haka yau ɗakin Sayyada ya kamata ya fara zuwa, amma da yake Hajiya Halima ta shirya abun yi, sai ta tare shi tun daga tsakar gida, tana share ƙwalla tana yi masa sannu da zuwa.

Hankalinsa ya fara tashi, shi sam ba ya so ya ga wani nashi a cikin damuwa, ya ce"Hajiya lafiya? Mene ne ya faru?"

Ta ce"Don Allah wannan zumunci da kuke son ƙullawa a bar shi, ba dole ba ne tun da matsala zai zama, yau matarku ta ci mutuncina, ta yi min gorin haihuwa saboda na je ɗaukar ɗan da ka ce nawa ne, ko ku da kuka ajiye ni ba ku yi min gorin haihuwa ba sai ita? Idan ba dama ni kawai zan tafi gidanmu, rashin haihuwa wani ciwo ne a zuciyata, ba zan yarda a dinga fama mini shi ba, iyayena suna sona, auren ana yin shi ne don a haihu, tun da ba zan haihu ba ni na haƙura, ba zai yiwu ƙanwar ƙanwata ta dinga cin mutuncina ba, ku gafarce ni mai martaba ni zan tafi". Ta rushe da kuka

Ya rungume ta a jikinsa yana buga bayanta a hankali, ransa ya yi matuƙar ɓaci, sai da ta tsagaita da kukan ya kama hannunta ya kai ta ɗaki, ya ce"Ki yi haƙuri Hajiyata, ina zuwa".

Ya fita ya yi sashen Sayyada.

Ina tsaye goye da Daddy wanda yake ta kuka na rigimar bacci, ya faɗo ɗakin, ina kallon shi na ga a fusace yake, gabana ya faɗi, kuma ban kawo komai ba sai ita ɗin, tun da ni dai yanzu ita ce ƙaddarata ta gidan aure, na ce"Sannu da zuwa".

Ya ɗaga min hannu ya ce"Dakata! Ki riƙe sannu da zuwanki matata ta yi min".

Na cigaba da zagaye a falon ina jijjiga É—ana.

Ya ce"Wato ke Sayyada nema kike ki zama fitina a cikin gidan nan? Duk yadda na so ku zauna lafiya kin ƙi".

Na ce"Don Allah me na yi? Ka dinga jin ta bakina kafin ya yanke min hukunci, Kodayake dama akuyata ta yi kuka a wajenka ai, me ta ce maka na yi?"

Ya ce"Kar ki sake ki yi min rashin kunya, saboda wulaƙanci abin naki har ya kai ki je ki ciwa matata mutunci, kuma saboda jahilci har ma da gorin haihuwa? Haihuwar ke kika ba wa kanki? Ko an faɗa miki Allah ba Ya sonta ne ke ya fi so da ya ba ki bai ba ta ba?"

Na ce"Wallahi ban yi mata gori ba, kuma ni ba jahila ba ce, ita ce jahila da ta manta za mu je madakata za a yi mana hisabi".

Ya zaburo kamar zai dake ni ya ce"Yi min shiru! Mara kunya kawai, ba dai taƙamarki yaron nan ba? Da shi kike ɗaga mata kai ai ko? To zan iya karɓar shi na ba ta, ta riƙe shi kuma har abada, ai ɗana ne ina da iko da shi ba ke kaɗai kika haife shi ba".

Na zauna na fashe da kuka mai tsanani, na kunce goyon na baje shi a kujera na ce"Ga shi nan ka ba ta shi tun yanzu".

Ai kuwa ya ɗauke shi ya fita, kukana ya tsananta, na yi iya yina, sannan na tafi ɗaki na haɗa jakar kayana na ɗauki kuɗin mota na fito, zan fita shi kuma ya zo tafiya masallaci, ya kalle ni rai a ɓace ya ce"Koma ɗakinki!"

Na ce"Gidanmu zan tafi saboda ba zan iya ba, ka zauna da matarka ita kaÉ—ai zai fi maka".

Ya ce"Ai dama ban ce ba za ki tafi ba, ko bari gobe da safe ko da asuba ne sai ki tafi, amma yau dai ba za ki bar gidan nan ba".

Na tsaya na ƙi komawa, a gabana suka tafi masallaci tare da mai gadin, na gwada buɗe ƙofar ta ƙi buɗewa don an kulle ta da mukulli, na juya na koma, sai kuwa na ga Hajiya tana leƙenmu ta windo, ta yi min wani makirin murmushi ta yi maganar fa ban jiyo me ta ce ba, saboda mun yi nesa, na koma ɗaki na zauna ina ta kuka, na kira Mama a waya na sanar da ita, sai kuwa ta ce ko me zai faru kar na sake na dawo gida da sunan yaji, ai dama ita rayuwa iya ruwa ne fid da kai, don haka na dan yadda zan yi da kishiyata.

Haka na haƙura, da ya dawo daga masallaci ya zo ya shiga ɗakin Abiy inda kayan yaron yake, ya ɗauki kayan shi ya fita, yana ta fushi kamar bai taɓa dariya ba, haka na kwana cike da damuwa, don ma na rage tsayin daren da sallah.

Washegari da safe wajen ƙarfe shida sai ga shi ya shigo da yaron a hannu, ya ajiye shi a gadon da nake kwance, ya ce"Ga shi nan, Hajiyar zazzaɓi take yi ne, amma tana jin sauƙi zan mayar mata da ɗanta, idan kuma za ki tafi to kar ki tafi da shi, ki faɗa min na zo na ɗauke shi".

Na yi banza da shi, ya ce"Magana nake yi miki".

Nan ma dai ban kula shi ba, ya fice daga ɗakin. Dama yau na ranar kwananta ne don haka ban sake ganin shi ba ma, washegari ma sai dare da ya dawo, shi ma ɗakinta ya fara sauka sai wajen ƙarfe goma ya zo ɗakina, lokacin har na yi shirin bacci, kishi ne ya hana ni baccin ina jira na ga zai zo ko zai kai mata kwanana ne?

Bai neme ni ba, ni ma na kama kaina ban sake zuwa É—akin shi ba, idan na gan shi dai ina gaishe shi, domin kuwa sai ranar kwanana ta zo ta wuce ban gan shi ba ma, zan bar masa abinci dai kuma na ga yana ci.

Sai da aka yi sati É—aya a haka, wataran kwanana ya zagayo sai ya fara yi min wannan plashing É—in, na kashe wayata, sai ga shi ya zo É—akin nawa, ya ce"Wato Sayyada gaba kike yi da ni ko?"

Na ce"Ni ba gaba nake yi ba, idan mun haÉ—u ai muna gaisawa ko?"

Ya ce"To amma ai da ba haka kike yi min ba, kin fi mu yi ta zama a haka kenan?"

Na ce"Tun da haka ka zaɓa ba".

Ya ce"To ya isa kar ki yi min rashin kunya, tashi mu je na duba ki".

Ban yi musu ba na tashi na bi shi, ya dinga ja na da fira na yi banza da shi, sai ya kama kan shi shi ma ya shiga neman abin da yake buƙata, ai kuwa na yi masa kwance tamkar satin farko na aurenmu, ran shi ya ɓaci sai haƙura ma ya yi ya ce na tafi ya fasa, ban tafin ba, na kunna wayata, na kunna recording ɗin da na so ya tsaya ya ji a ranar da abun ya faru ya ƙi, ai kuwa ya yi shiru yana saurara, yana ƙarewa na ɗauki wayata na tashi zan bar ɗakin, sai ya riƙo ni, ya ce"Sayyada dawo mu yi magana".

To har ga Allah ni ma na gaji da wannan zaman namu mara daÉ—i, don haka ban yi musu ba na dawo na zauna, ya ce"Da gaske wannan ba editing ba ne?"

Na ce"Idan kana kokonto ba sai ka yarda ba ai, da sannu lokaci zai tantance maka".

Jikinsa ya yi sanyi, ya gane muryar Hajiya tabbas, kuma abin da ya fi tsaya masa a rai wai har ta iya kiran sunan shi gatsal Isma'il babu mai martaba? Ya janyo ni jikinsa ya ce"Ki yi haƙuri Sayyada, ai ba ki faɗa min yadda aka yi ba".

Na ce"Ai ba ka ba ni dama ba".

Ya ce"Ki yafe min, kaidinku mata ya fi na shaiÉ—an".

Na ce"Na wasu matan dai".

Ya ce"Don Allah ki yi haƙuri, kuma na gode da ba ki biye min kin tafi ba, yanzu kam na tabbata ƙarya zazzaɓi ta yi don kar ta kula da yaron nan, lallai lamarin duniya da ban mamaki yake".

Na ce"Ka manta, ya wuce in sha Allah! Yanzu ka ba ni hakkina ba zan yi maka irin na É—azu ba".

Ya ce"Yi haƙuri sai gobe, jikina ya yi sanyi".

Na ce"Ai É—umamaka zan yi".

Ban hakura ba sai da na saka shi ya manta da komai a wannan daren, muka shirya kamar ba a yi ba.

08028966015
[21/11, 7:32 am] Sadiya Abdulrazak: 50

Washegari har ya tafi wajen aiki sai ya kira ni a waya ya ce na tura masa recording ɗin nan, na tura masa, ban san dai yadda suka ƙare ba, da daddare ya dawo tare da Abiy, washegari na ce ya kai ni gidansu, muka je muka wuni a can, ni dai tun da na zo gidan ban taɓa ganin ko sabga ake yi Hajiya Halima ta je gidansu Isma'il ba, abun har mamaki yake ba ni. Haka muka cigaba da rayuwa, sai Hajiya ta tsiri zuwa ɗakina, za ta zo ta zauna, ni dai daga gaisawa ba na ce mata komai, sannan ba ta cewa ma na ba ta ɗana, ban san dai me yake kawo ta ba, shi yasa nake zama na kafa na tsare, da aka kwana biyu ana yin haka sai ta daina zuwa, muna ta zaman lafiya da Mai martaba, sai idan ya so tsiyar shi sai ya ce dole na yi masa jam'u, ya fi yi min haka idan ya ga ina so ya bar ni fita unguwa, idan kuma ya so barkwnaci sai ya ce ni ma sarauniya ce, ya wuni yana yi min jam'u.
Chapter 86 · 0% Book details