← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce"Ba fa wannan ne maƙasudin zuwa gidan ba, kuma don mace tana shan wuyar laulayi babu kulawar miji ai ba za a ce a raba aure ba, ka samu mutum sama ta ka babu binciken me ya raba shi da tsohuwar matarsa ka wanke taka 'yar ka ba shi, to ga shi nan ai yana neman rayuwarta".

Baba ya bi ta da kallon neman ƙarin bayani, shi ma ƙarfin hali kawai yake yi, amma ramar Sayyada ta ba shi tsoro, ya zauna ya ce"Ban gane yana neman rayuwarta ba, na fa lura ke za ki ɗaurewa yarinyar nan ki hana ta zaman aure, wai idan an ce ta sake zama bazawara a karo na biyu mene ne ribarki ne?"

Mama ta ce"Mijinta hariji ne, ta yi iya ƙoƙarinta na ganin ta daure ta gaji, nawa Sayyada take? Ta yi ƙanƙanta da wannan juriyar ba za ta iya ba, cutarta yake yi".

Kunya ta kama ni, na sunkuyar da kai ina hawaye, tare da fargabar hukuncin da Baba zai yanke a kan lamarina.

Mama ta ɗora da faɗin"Ka san wane ne hariji, kai da kanka ka shige gaba ka kashe auren ƙanwarka Salamatu, kuma matsalar iri ɗaya ce da ta Sayyada, shin ƙullatar 'yarka da ka yi zai sa ka kasa ƙwatar mata 'yancinta? Wallahi ba za ta koma ba".

Ta ƙarasa kamar za ta yi kuka.

Baba ya zuba min ido kamar ba shi da abin cewa, kafin ya ce"Sayyada".

"Na'am" Na amsa da muryar kuka.

Ya ce"Ta nan kuma kika ɓullo? Kin rantse ba za ki yi zaman aure ba ko? To idan ma gidan tsohon mijinki kike hange ko aurenki ya mutu matuƙar ina raye kin gama aure da wannan yaron har abada, sai dai ko idan da rabo a tsakani rabon ya kashe ni sannan ku yi auren".

Na ce"Wallahi Baba babu tunanin komai a raina, da zuciya ɗaya na karɓi auren nan, amma ba zan iya jurewa ba".

Ya ce"Zan yi magana da shi, ni na san ba zai yi ƙarya ba, indai ya ce hakane kuma ya nuna halittarsa ce haka zan goyi bayan zamanki a gida kafin a san yadda za a yi, saɓanin haka kuma za ki bi shi ku tafi, kuma idan kika sake tada wata fitina a zamanku ba zan yafe miki ba".

Daga haka ya fita daga É—akin, na fashe da kuka Mama tana rarrashina.

Ya koma ya samu Malam Ashiru kansa a sukunye, gabansa faÉ—uwa kawai yake, idan aka ce ya rabu da Sayyada tabbas zai shiga tashin hankali, sai yaushe kuma zai samu wata matar? A sanyin nan da idan ya busa yake jin kamar ana daÉ—a zabura shi zai sha wuyar zaman gwauranci, Baba ya ce"Malam mene ne matsalar ne?"

Ya ce"A...ni dai a sanina babu wata matsala".

Baba ya ce"Ta ce kana da larurar da ba za ta iya zama da kai ba, hakane?"

Ya ce"Subhanallah! Wallahi Baba ba larura ba ce, itan ce dai nake tunanin tana da rauni, kuma hakan yana da nasaba da tata larurar".

Ya muskuta ya ce"Baba ni lafiyayye ne, ita kuma na kula tana da ciwon sanyi, kuma mun yi magana na fahimce ta, sai na ɗaga mata ƙafa ma, har na ce mata zan siya mata magani, yanzu ma na siya to ganin ta samu ciki ne ya sa na ce tun da maganin yana da ƙarfi ta dakata sai ta haihu, tsakani da Allah Baba a ce gabaɗaya a jingine raya sunnar saboda wannan?"

Baba ya ce"Ikon Allah, au wato yarinyar nan da gaske take ba za ta bi umarnina ba kenan".

Ya ce"A'a Baba a yi haƙuri, ba haka abun yake ba, wallahi Sayyada tana yi min biyayya kuma muna zaune lafiya sosai, ina sonta tana sona, matsalarta ɗaya ce, kawai ta wannan fannin ne, take ɗan tauye min hakkina, shi ɗin dai za ta gyara sai a samu sasanci in sha Allah".

Baba ya shiga gidan, Ustaz ya fara furta"Astagfirullah".

Yana shiga ya rufe Mama da faɗa yana cewa"To ai kin ga irinta, yarinya ta zo ta shirya miki ƙarya kin hau kai kin zauna babu bincike, ashe ita ce ma take gudunsa a shimfida tana wahalar da shi, mene ne auren don ubanki?" Ya karasa maganar yana daka min tsawa, na saki sabon kukan tausayin kaina.

Mama ta ce"Ai dole ta guje shi tun da ya fi ƙarfinta, kowa fa ya san wane ne hariji, ka tausayawa yarinyar nan, kar ta mutu garin ganin cewa sai ta yi zaman aure".

Ya kalle ni ya ce"Ke Sayyada ba na son ƙara jin magana irin wannan mara tushe ballantana makama, ya faɗa min gudunsa ma take , saboda ciwon sanyi da ya yi mata katutu, kuma ya nema mata magani, me zai yi wanda ya wuce wannan? Allah Ya rufa miki asiri kin samu miji yaro mai hankali shi ne za ki saka tunanin ɗan iskan tsohon mijinki a ranki ko?"

Kukana ya tsaya cak lokacin da Baba yake cewa"Maza ki tashi ki bi mijinki, ki koma É—akinki! Idan kika sake zuwa gidan nan da sunan yaji ko shirmen banza za ki ga yadda za mu kwashe".

Jikina ya ɗauki rawa, har bakina karkarwa yake yi, na kasa cewa komai sai kukan da nake yi kamar raina zai fita, ina ji Mama tana ta yi masa bayani ranta a ɓace, shi ma ya hau har sun fara fusata da mayar da martani mai zafi, na tashi na ja akwatin kayana ina ta kuka na fita daga ɗakin, Mama ta ce"Dawo Sayyada, babu inda za ki je, duk matakin zai ɗauka sai dai ya ɗauka, me yasa maza duka halinsu ɗaya ne, ba kwa yi mana adalci".

Ko juyowa ban yi ba, sai da na kai zauren da yake a zaune a kan itace, na tsaya ina tsananta kukana.

Ya taso yana "Subhanallah! Assayyada, me ya yi zafi haka, don Allah ki bari, ki yi haƙuri aure ibada ne, kuma dama raya sunna sai an daure, mene ne auren idan ba shi ba? Yi haƙuri mu je zan gyara kin ji?"

Ya fita, na bi bayansa, ya tada babu dinsa na hau muka tafi, na tsaya da kukan, amma jikina bai daina rawa ba, kamar zazzaɓi zai kama ni ma, zuciyata kuwa kamar gasata ake yi da wuta, ji nake dama na faɗo daga babu ɗin nan na mutu na huta, ba don dai cikin jikina ba, wanda na ƙwallafa ran na haife shi.

Yana ta tasbihi har muka ƙarasa gida, bayan mun shiga ya ya zauna yana ta ba ni haƙuri da faɗin"Assayyada na san na ɗan fi ƙarfinki, amma ke ma fa da naki laifin, bi ma'ana kin kasa buɗe zuciyarki ki karɓe ni ki yarda cewa ke ma za ki iya zama yadda nake, inda kin yi niyya da tuni kin zama irina, kin ga da an wuce wajen, yanzu tun da ciki ne da ke, kuma tun da har kika iya zuwa gida da wannan lamari mai girma na san kin kai ƙarshe ne, ki zaɓa a cikin sau ukun da muke yi ko huɗu wanne kike ganin za a soke? Ni kuna zan yi iya ƙoƙarina na ga daure an yi minus one, amma ban da na dare, domin shi ne lokacin da na fi samun nutsuwa".

Na ce"Babu wani lokaci da za a rage, ka ƙara ma, ka dawwama kana taka ta don Allah, idan na mutu ai dai ba za ka taki gawata ba ko?"

Ya ce"Subhanallah! Wato ainafin Assayyada har yanzu ba ki gama sanin darajar miji da aure ba, inda kina da sani da ba ki yi wa mijinki wannan gatsali ba, amma dai la ba'asa na yafe miki, kuma ni fa duk wannan abun ina yi ne don na ga na ba ki cikakken hakkinki ban bar wani gurbin da za ki ji kewa ba, amma tun da hakane la ba'asa, idan don ta ni ne ni fa zan iya haƙura ma na zuge tazugena, to kawai ina tuna cewa sunna ne, kuma shi ne auren, sannan jihadi ne, na sha faɗa miki tamkar ana yaƙi ne, ana kashe arna guda saba'in, shin ba kya kwaɗayin ladan da za ki samu ne?"

Ban ce komai ba, har ya ƙaraci surutunsa, ya ce"Yunwa nake ji, me za ki dafa mana yanzu?"

Nan ma dai ban kula shi ba, ya ce"Subhanallah! Wato Assayyada da a ce kin san girman hukuncin matar da ba ta bin umarnin mijinta da tuni kin doƙa kin fara roƙona gafara, duk da dai ko ma ba ki roƙa ba ni na yafe miki ma".

Na ce"Ballantana ma ba zan roƙa ba, kar ka yafe ɗin, idan ka ga dama kar ka ɗaga min kafar na shiga aljanna, kai ba malami ba ne, mai son zuciya ne, mai ci da addini, Allah yana kallo yana sane, in sha Allah zan ta kai ƙararka wajen shi, shi ne zai bi mini hakkina".

Na fice daga falon, na yi alwala na shiga É—akin gado na yi sallah na canza kaya na kwanta.

Ina jin shi a kitchen, sannan ya zo ya kawo min abinci ya ce na tashi na ci, ban san ma me ya dafa ba, don ko kallonsa ban yi ba, haka ya gaji da yi min nasiha ya fita da abincinsa, ina ga dai ta sha jinin jikinsa domin kuwa haka muka kwana ƙalau bai neme ni ba, da asuba ma bai kula ni ba, da safe sai na lura kamar ma wani kaffa-kaffa yake yi da ni, fuskarsa babu yabo babu fallasa, ba wai fushi yake yi da ni ba, na yi kwance na ƙi yin abin karyawa, sai shi ya dama koko, ya fita ya siyo waina, ya ci ya rage min, bayan ya fita na dafa farar taliya na ƙara na ci, to me waina guda uku za ta yi min da koko rabin kofi?
Chapter 31 · 0% Book details