Sashe 84
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Takaici da kunya ya sa na kashe kiran, na yi masa text massage na ce kar ma ya zo goben don na zan koma ba, na kashe wayata, sai dai kuma murmushi nake yi ina juyi cike da kewar tashi, tsakani da Allah ji nake kamar na janyo goben na gan ni a gidana, cikin É—akinsa, kan gadonsa, sannan cikin jikin shi.
Washegari da safe na je gidan kitso, aka yarfa min shi mai kyau, aka yi min jan lalle, na gama shirya komai na kayana, Mama ma ta gama ba ni abin da za ta ba ni, har mun yi sallama da Baba da zai fita, saboda ina zaton Isma'il zai zo É—aukata kafin magriba, amma sai na ji shiru har an idar da magriba, ga shi yau É—in gabaÉ—aya ma bai kira ni ba, ni ma ban kira shi ba, Mama ta ce"To tafiyar taku ashe sai dare".
Na ce"E, ba mamaki yana hanya".
Aka idar da sallar isha'i shiru bai zo ba, na shiga É—aki na kira shi a waya, ya É—auka yana faÉ—in"'Yan mata ya aka yi ne?"
Na ce"Sai ƙarfe nawa za ka zo ne? Tun rana muka shirya shiru".
Ya ce"Ikon Allah, to ke Sayyada kin manta yadda muka yi da ke jiya, kika ce ba ki yi kewata ba, na ce zan bar ki sai wani satin kika ce kin ji, shi ne na bari sai wani satin É—in".
Haushi ya kama ni, na ce"To shikenan, Allah Ya kaimu, ka bari ma sai wata shekarar".
Na ajiye wayar ina zaton wasa yake yi min yanzu zai zo, amma sai na ji shiru har ƙarfe goma ta yi, raina duk ya ɓaci, Mama ta ce"Ke Sayyada wannan mijin naki anya zai zo yau kuwa?"
Na ce"Ya ce sai gobe, wai zazzaɓi yake yi".
Ta ce"Subhanallah, Allah Ya sawaƙe".
Na amsa da amin.
Can wajen sha biyu na kira shi, bai ɗauka ba, haka na yi kwanan ɓacin rai.
Washegari da ya kira ni na ƙi ɗauka, tun yamma na shirya bai zo ba, ganin an idar da sallar isha'i gabana ya fara faɗuwa, na ce to mutumin nan ko da gaske yake ne? Idan don ta ni ce zan iya rabuwa da shi har zuwa satin da ya ce, to amma ba na so Mama ta zargi ba mu shirya ba, don haka na kira shi, na yi sa'a ya ɗauka, na gaishe shi ya amsa yana faɗin"Hajiya Sayyada zaman gida daɗi, ya daren?"
Na ɓata rai kamar yana kallona na ce"Na gode da abin da kake yi mini".
Kamar bai san me nake nufi ba ya ce"Au wai kati da na saka miki? Haba ai babu komai, hakkina ne".
Na ce"Kenan so kake ka nunawa iyayena ba ka huce ba shi yasa ba za ka zo mu tafi ba ko?"
Ya yi 'yar dariya ya ce"Ban da rigima irin taki ke fa kika ce sai shekara, ni fa har ba fara lissafi, ke har na yi wa Hajiyata albishir É—in za ta same ni babu sharing da ke na shekara É—aya, sai murna take yi, har ma ta ce za ta zo ta kawo miki kyauta har gida".
Na ce"Ni dai don Allah ka zo mu tafi, ba na son haka".
Ya ce"Kin yi kewata?"
Na yi shiru raina yana ƙara ɓaci.
Ya ce"Wallahi sai kin ce na yi kewarku mai martaba sannan zan zo mu tafi, idan ba haka ba sai kin yi sati cif".
Na ƙi magana, kamar na yanke kiran, sai dai na san indai na sake kwana yau a gida dole iyayena su ce da matsala.
Ya ce"Shikanan sai da safe, Hajiya tana jirana zan yi mata tausa".
Kamar zan yi kuka na ce"Na yi kewarku mai martaba".
Ya ce"Da gaske? Kuma sosai?"
Na katse wayar.
Ƙarfe tara saura sai ga sallamar shi, na sauke ajiyar zuciya, Abiy ya yi bacci don haka Mama ta ce mu rabu da shi, daga baya a kawo shi, na goya Daddy ya ɗaukar mana kayan namu muka shiga mota muka tafi.
Mun fara tafiya ya kunna rediyon motar, kawai sai ji na yi muryata tana ta maimaita 'Na yi kewarku mai martaba' Ya dinga dariya yana cewa"Ai na ji kin yi kewata, ki haƙura ki yi shiru haka".
Shi kuwa recording sai yi yake, takaici ya hana ni magana, na ji kamar zan yi kuka, tabbas wannan tsiyar da Saddam ya yi min ta saka farashin jan ajina ya ruguje rugu-rugu, bai kashe ba har sai da muka ƙarasa gidan.
Mun fita daga motar, ya ce na shiga mu gaisa da Hajiya don ta san na dawo.
Na ce"Amma idan ka faÉ—a mata ma ai ya wadatar, kuma ita ya kamata ta zo ta yi min sannu da zuwa".
Ya ce"A'a ba ki so gaskiya ba, ko ma dai hakan ne, ni na ba ki umarnin ki je ki gaishe ta".
Ban yi musu ba muka shiga, tana ganinmu ta taso da fara'arta ta tare ni kamar za ta rungume tana faÉ—in"Oyoyo Daddy, É—ana ya dawo, sannunku da dawowa, kunto min shi na gan shi".
Na kunto shi na ba ta.
Ta shiga ririta shi tana faÉ—in"Ma sha Allah, yaro ya yi wayo, wallahi har mafarkinsa nake yi, sai dai idan ban kwanta ba".
Sai kuma ta fara kuka.
Isma'il ya ce"Yi haƙuri Hajiya, mene ne kuma abun kuka?"
Ta ce"Kukan farinciki ne wallahi, ashe zan ga jininku mai martaba? To ni dai ba ni da rabon ganin nawa, don Allah ku taimaka ku sa yaran nan su kalle ni kamar uwa, su ce min Umma ko zan ji sanyi a raina, jinsa nake kamar É—ana".
Ta rushe da kuka.
Ya tashi ya koma kusa da ita ya rungume, kishi ya motsa min, na tashi ina faÉ—in"Ni dai bacci nake ji, sai da safe".
Na ƙarasa sashena, na buɗe na shiga, ko'ina fess yake, don yana gyarawa, na shiga ɗakina na yi wanka, na fito ina shiryawa sai ga shi da yaron, ya zauna a bakin gadon yana faɗin"Wallahi yau Hajiya ta ba ni tausayi, sai da ta saka ni hawaye, Ya Allah duk macen da ba ta haihu ba take nema, Allah Ya ba ta haihuwar yara masu albarka".
Na ce"Abun da tausayi kam, Allah Ya ba ta wani rabon madadin yaran".
Ya ce"Amin" A ransa kuma yana ayyana dole idan Sayyada ta ƙara haihuwa ya bawa Hajiya ɗan ta shayar da shi ita ma ta samu mai kiranta uwa.
Ya tashi yana cewa"To ni zan wuce, ina jiranki idan kin gama".
Zai tafi da É—an, na ce"Ajiye shi, zan canza masa pampers".
Ya ajiye shi ya tafi, yana fita na murzawa ƙofata key, a fili na furta "Ba dai ni ce na yi kewarka ba? Kuma har za ka rungumi matarka a gabana? Da ni kake zancen".
08028966015
[19/11, 3:46 pm] Sadiya Abdulrazak: 49
Na gama komai na kwanta na yi mana addu'a ni da ɗana. Mai martaba yana can yana jirana, da ya ji shirun ya yi yawa sai ya fara yi min plashing, yana ta yi babu ƙaƙƙautawa, ni kuwa na kashe wayar, sai ga shi yana buga ƙofata tare da kirana da murya mai sanyi "Sayyada, Sayyadata".
Na yi shiru kamar ban ji ba.
"BuÉ—e mana Sayyada, da wani sabon salon kika dawo kenan ko? Ba za ki buÉ—e ba?"
Na yi ƙirmisisi, ya sanyaya murya ya ce"Wani abun ne ya faru? Buɗe mu yi magana kin ji".
Na ki buɗewa, har dai ya fusata "Ke ba magana nake yi miki ba? Umarni nake ba ki ba lallaɓa ki ba, ki buɗe ƙofar nan!".
Sai ma na yi juyi ba ni da niyyar buÉ—ewar.
Ya ce"Shikanan, na tafi wajen matata, ai gida biyu maganin gobara".
Wani abu ya daki zuciyata, na tashi zaune, ni fa ko me za mu yi ba na so ya dinga bari wani yana fahimtar halin da muke ciki, ina jin ƙarar buɗe falon na sauka daga gadon da sauri na fita da ɗan guduna, har ya fice na bi shi, ya yi kamar bai gan ni ba ya nufi sashen Hajiya, na ce"To ba ga shi na buɗe ba?"
Ya ce"Ba na buƙata".
Na yi gudu na riƙe shi ƙam, ina faɗin"Ba na son haka, ai na buɗe ko?"
Ya ce"Sayyada kar ki ga na sake miki fa ki ɗauka na janye batun sai kin lallaɓa ni".
Na ce"Na ji, mu je sai na lallaɓa ka ɗin".
Ya tsaya yana yi min kallo mai kama da harara, na kalli gefe ina ɓata rai, ganin ba zai ce komai ba sai na ja hannunsa muka fara tafiya, muka koma ɗakin, na rufe na wuce da shi ɗakinsa, muka shiga, na zauna a bakin gado ina ɓata rai, sai ya yi murmushi ya zauna a kusa da ni yana cewa "Sayyadata sarkin kishi, ashe shi yasa aka ce mai mata biyu ɗan gata, yanzu da ke kaɗai ce yau sai abin da na gani ko?"
Na ce"Ni fa kawai idan ka san za ka dinga naniƙar matarka to ka daina ja na wajenta na gani".
Ya ce"Inyee, au don na taɓa matata shi ne matsalar dama? To ke yanzu da kika janyo ni ɗaki ba don ki taɓa ni ba ne? Yau ga ikon Allah ki samu kace da mijinta ki shigo tsakiya ita ba ta yi kishi da ke ba, sai ke ce za ki yi kishi da ita?"
Na ce"Idan ta yi É—in ai ba faÉ—a maka za ta yi ba".
Ya jinjina kai "Na lura da wani rashin kunya kika dawo, wanda kika daina yi a baya, don haka ki yi ke kaÉ—ai, kin ga tafiyata, mun tafi wajen matarmu ta kula da mu".
Ya yi hanyar fita na riƙo shi, ya haɗe rai "Sake ni, ba za mu iya wannan kumburin da kike yi mana ba, ba za mu ɗauka ba".
Na ce"To ka yi haƙuri na daina".
Ya ce"Ki yi jam'u da kirari tukuna".
Na ce"Ku yi haƙuri ranku ya daɗe".
Ya ce"Ki yi min kirari idan ba haka ba ko ban tafi ba na juya miki baya, ko na zuge tazugena don na lura abin da kike yiwa kenan".
Na ce"Na ji a zuge É—in".
Ya ce"Ok".