← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 89

Sashe 21

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka sha firarmu cikin nishaɗi ya tafi, ina shiga kuwa na faɗawa Umma saƙonsa, na yi murna sosai, don ana so a ga na yi aure ina ɗakina, a ranar na yi ta jiransa ya zo online mu yi fira kamar yadda muka saba kafin mu yi bacci sai na ji shiru bai yi min magana ba, na duba na gan shi online, na yi masa sallama amma har bacci ya fara kama ni bai duba ba, raina ya ɓaci, jira nake gobe ya kira ni na ji dalili, sai na yi masa daru sosai kafin ya shawo kaina.

Abun mamaki washe gari tun safe nake jiran wayarsa shiru bai kira ni ba, na wuni suƙuƙu ina tunanin dalilinsa, ga shi ina ganinsa online har yana status ballantana na ce ba lafiya ba, haushi na ji sosai, shi yasa ni ma na ƙi kiransa, haka muka sake kwana bai neme ni ba, sai ranar Lahadi da asuba na gaida Baba yake ce min na tambaye shi ƙarfe nawa masu tambayar za su zo, kuma wace amsa za a ba su ina son shi?

Kaina a ƙasa na ce"To ban dai sani amma zan tambaye shi ɗin".

Ya sake cewa"Kina son shi?"

Na ce"E Baba".

Ya ce"To ma sha Allah, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi".

Na tashi na koma ɗaki, sai na yi masa text massage na ce"Assalamu alaikum, Barka da safiya, Baba ya ce na tambaye ka ƙarfe nawa za su zo?"

Babu jimawa ya dawo min da amsa ya ce"Ki yi haƙuri Sayyada, sun fasa zuwa".

Gabana ya faÉ—i, na rubuta masa,"Me yasa?"

Ya dawo min da amsa"Saboda na fasa aurenki".

Hannuna ya É—auki rawa, na saki wayar zuciyata tana bugu, nan take na shiga firgici, sai ga kiransa, na É—auka da sauri da rawar murya na ce"Alhaji ba na son irin wannan wasan".

Ya ce"Sayyada kina tunanin son da kike yi mini ya fi wanda nake yi miki ne? Ina son ki sosai, idan haka ne me yasa zan yi wasa da wannan maganar mara daÉ—i? Da gaske na fasa aurenki".

Kamar zan yi kuka na ce"Me yasa? Me na yi maka don Allah?"

Ya ce"Shawara mahaifiyata ce, kin san kuma ba za ta ba ni gurguwar shawara ba, shi yasa ko tambayarta dalili ba na yi, amma wannan karon na san dalilin ma".

Na ce"Me na yi mata?"

Ya ce"Ba ita kika yi wa ba, kanki kika yiwa".

Na yi tsam ina tunanin manufarsa, ya ce"Na so ki ba tare da sanin ainahin wace ce ke ba, sai yanzu kawai na samu labarin wace ce ke, ban san kin yi rayuwar zina da tsohon mijinki kafin aurenku ba, da ke da Anisa ce min kuka yi zumunci ne kawai ya sa kike zaune a gidan yayan babanki, ashe Babanki sallama ki ya yi ya ma kore ki daga gidansa, sannan kuma duk macen da za ta iya cakawa mijinta wuƙa ba matar aure ba ce, inda na san duka wannan da ba zan saka ki ko a ƙofar zuciyata ba ne, ina sonki Sayyada amma za mu rabu dole, ko Mama ba ta ba ni shawara ba ni ma ba zan iya auren irinki ba, tsira da rai ya fi tsira da dukiya, bis salam".

Ya kashe wayar, haka na daskare da wayar liƙe a kunnena, bugun numfashina sai hawa da sauka yake, abubuwa suka shiga dawowa kwanyata, na saka kaina a cinya na fashe da kuka mai ƙarfi, kukan da har Umma da Baba sai da suka jiyo, Umma ta taho da sauri tana tambayata dalili, na ce"Wai ya fasa, Umma ya ce ya fasa aurena, wai ya ji labarin mahaifina yana fushi da ni ya sallama ni na shiga uku!".

Na sake rushewa da kuka, Suna rarrashina kamar suna lakaɗa min duka na ƙi dakatawa da kukan, sai da na yi mai isata, sannan Baba ya zauna ya dinga yi mini nasiha da son nuna min hakan shi ya fi alkhairi, na dage da neman zaɓin Allah kawai, zai kawo wanda zai aure ni ko da ya ji labarin abin da na aikata.

08028966015
[06/10, 6:18 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN KU YI MANA ADALCI NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, IDAN KINA JIN DAƊIN KARANTA SHI NI MA KI YI MIN ADALCI KI BIYA NI KUƊIN KARATUNA.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

Shaidar biya ta nan
08028966015

14

A ranar dai na shiga tashin hankali sosai, sai na ji kamar ma sai yanzu ne na fara son Alhaji Shamsi, na rasa yadda zan yi, na dinga kiran shi ba ya ɗauka, ƙarshe ma na daina samunsa, da alama ya yi blocking ɗina har ta whatsApp, ranar Juma'a da na je gida Mama ta dinga ba ni haƙuri, da nuna min wannan shi ne illar abin da na aikata, zina tana da rabo mai girma, sannan ga illar biyewa sharrin zuciya, yanzu zai yi wuya wani ya ji na cakawa mijina wuƙa ya yarda ya aure ni, na riga na yi wa kaina baƙin fenti, ranar na ci kuka na gode Allah, Baba ba ya nan, ban tafi ba har dare ina jiransa, da ya dawo na gaishe shi ya amsa babu walwala, na fara roƙonsa ya yafe min, ya ɗaga min hannu kafin ya nuna min hanyar fita a fusace ya ce"Sayyada tashi ki bar gidan nan, kar ki sake neman yafiyata, na faɗa miki ba zan yafe miki ba sai ranar da na ga gawarki, kuma idan kina da wani wanda kike so bayan wanda ya fasa ɗin, ki tsayar da shi ki yi aure, wannan umarni ne na ba ki, wanda idan kika cika zan iya duba yiwuwar yafe miki ko kuma na tsaya a kan bakana".

Komai nawa ya tsaya cak, da gaske idan na yi aure Baba zai iya yafe min? Idan kuwa hakane ya zama dole na yi aure, domin yanzu ba ni da babban buri sai ganin Baba ya yafe min mun dawo rayuwa kamar baya, a raunane na ce"In sha Allah zan samu wani, Baba ku taya ni addu'a Allah ya ba ni na gari".

Bai amsa ba, na fice daga gidan ina waiwayensa.

Tun daga ranar na sakawa raina son aure, na fara soyayya da Sulaiman wannan saurayin mai adaidaitasahun, wanda na ce zai ajiye ni a gidan haya, yanzu na sauke farashi ji nake ko a kango zai ajiye ni zan aure shi indai Baba zai yafe min, mun kai wata biyar muna soyayya, yana ta tara tara kuɗin auren, ya ce kullum dubu ɗaya yake ajiyewa, sannan ya samu ya haɗa dubu ɗari da hamsin, zai kawo kuɗin aurena, wannan ɗari da hamsin ɗin a ciki akwai sadaki da kuma dukiyar aure, zuwa lokacin na koyawa kaina son Sulaiman, burina a yi auren kawai, duk da ina tunanin fuskantar ƙalubale ko daga wajen mahaifiyarsa ne, nahaifinsu ya rasu, kuma shi Sulaiman ɗin ne mai riƙe da gidan nasu, mahaifiyarsa da ƙannensa uku mata ɗaya namiji, yanzu zai yi aure, shi ma hidimar gidansa ta hau kansa, ko yaya ne idan ya aure ni dole zai iya ragewa gidansu wata hidimar, tun da samun nasa ba ƙaruwa zai yi ba, da yawa haka tana faruwa, kuma laifin matar da ta aura ake gani, ba a duba nauyi ne ya ƙaru damu bai ƙaru ba, dole za a ga hakan, sai a ce mace ce ta mallake shi, ta hana shi hidimtawa iyayensa, sai ƙiyayya ta shigo ciki a takurawa yarinya a hana ta zama lafiya a gidan mijinta, ina jiyewa kaina wannan abun.

Wani lokacin sai na dinga tunanin shin shi Sulaiman ba shi da masaniyar wannan abubuwa da na aikata? Saboda ban ga alamar hakan ba ko da wasa, haka aka kawo kuɗin aurena, aka saka rana sati huɗu masu zuwa, ya ce min zai fara fafutukar neman haya tun yanzu, tun da aka saka ranar na ji shiru babu alamar Sulaiman ya ji labarin nan nawa mara kyau, sai zuciyata mara adalci ta ɗarsa min zargin Anisa, kawai na fara tunanin baƙinciki take yi min shi yasa ta faɗawa Alhaji Shamsi wannan tabon nawa, wata zuciyar ta ce min idan ba ta sona da shi tun farko me yasa za ta haɗa ni da shi? Muguwar zuciyar ta bawa kyakkyawar amsa da faɗin so take ta tozarta ki, so take a hankali kowa ya sani, ko kuma ta ga ya fi mijinta kuɗi shi ne take yi miki hassada, wallahi kawai sai na yarda da zuciyata, ba sai na ɗauki fushi da Anisa ba, dama ita ce abokiyar shawarata ko chatting, na yi mugun jan baya da ita, ko gidan ta zo na yi ta haɗe rai kenan, tun tana ja na a jiki har ta gane akwai wata a ƙasa, takanas ta zaunar da ni ta tambaye ni me ta yi min, ba ce babu komai kawai yanayi ne, da Umma ma ta fuskanci akwai wani abu ita ma ta zaunar da ni ta tambaye ni ko akwai laifin da Anisa ta yi min? Na ce babu, haka suka rabu da ni ina ta fushi da ita, shi yasa nake ƙara son Sulaiman, har alla-alla nake a yi auren ta mutu da baƙinciki tun da dai hassada take yi min, da baƙinciki, ƙila zamana a gidansu ne ma yake ƙona mata rai, oh mutum sai a bar shi.

Aurenmu ya rage sati ɗaya, Sulaiman ya zo zance, ya kira ni ya ce yana ƙofar gida, na fita, sai na gan shi a birkice ba kamar yadda na saba ganinsa ba, na ce"Yaya Sulaiman lafiya?"

Ya haɗe gira ya ce"Sayyada da gaske kin yi wata rayuwa kafin aurenki da wanda kika aura? Da gaske kin caka masa wuƙa?"

Na ji kalamansa kamar saukar guduna, gabana ya ba da rass, na kasa cewa komai, ya ce"Shirunki yana nufin tabbatar min?"

Na gyɗa masa kai alamar e, sannan na ce"Amma wallahi ƙaddara ce, komai ya faru ba da son raina ba ne, don Allah ka yi mini uzuri Yaya Sulaiman, ni mutum ce kamar kowa, zan iya yin kuskure".

Ya ce"Hmm, Sayyada kenan amma dai na yi mamaki sosai wallahi, ban taɓa zaton za ki aikata ba, ashe ke sumumu kasau ce? Micijin sari ka noƙe ce ke?"
Chapter 21 · 0% Book details