Sashe 2
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina kallon shi har ya shiga motarsa, waya kare a kunnensa, mai gadi ya buÉ—e masa gate ya bar gidan.
Da baya da baya na koma na zauna a kujera, na fashe da kuka, kukan kewa, ina kewar haihuwa da son ganin yarana, a wannan karon na shirya fito na fito da Sadam indai a kan haihuwa ne, ko ya bar ni na haihu ko kuma na haƙura da auren bakiɗaya, ai ana cewa mace ta yi haƙuri ta jure baƙinciki namiji ne saboda tunanin makomar yaranta, to ni kuma babu yaran ballantana na ce zamansu nake yi, na kai kamar minti ashirin a zaune kafin na tashi, na ɗauki jakar tawa na share hawaye na kama hanyar fita tsakar gidan, a bakin gate din na tsaya na gaishe da dattijon mai gadin, ya amsa yana mayar min da gaisuwar,ganin ba shi da niyyar yunƙurawa ta buɗe min yasa na ce"Baba zan fita ne".
Ya ɗan diririce kafin ya ce"A! Amma...Hajiya cikin girmamawa nake sanar da ke cewar Alhaji ya ce kar na sake bari ki fita, ki yi haƙuri, a gafarce ni,umarni ne daga sama".
Na ce"Don Allah ka buÉ—e min, ba ni da lafiya ne, asibiti zan je, kuma ba zan bari ya ga laifinka ba wallahi".
Cikin damuwa ya ce"A dai yi haƙuri Hajiya, a kan aikina nake".
Huci kawai na yi na juya na koma cikin gidan da gudu, kitchen na nufa don na gama yanke hukuncin da nake ganin shi ne mafitata a halin yanzu, wuƙa na zaro sabuwa dal na cire ta daga gidanta, zuciya tana ƙara zuga ni da ingiza ni na aikata kawai, tare da gudunmawar tunawa da irin tauye ni ɗin da aka yi aka cutar da ni, don haka na ji dole na ƙwatarwa kaina 'yanci.
08028966015
[20/09, 5:22 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 1
Buɗe damtsen hannuna na yi, na ajiye wuƙar na fara matsa hannun nawa don jin yadda zaman implant ɗin yake, na ci alwashin yau ba zai kwana a hannuna ba, ko da kuwa zan mutu ne wajen azabar cire shi, na ɗora wuƙar a daidai wajen zan yanka hannun, tsoro da tausayi kaina suka kama ni, zuciyata ta ce mini 'A'a fa Sayyada wannan kasada ce, idan kika yanka kanki jini ya ɓalle miki komai zai iya faruwa, ƙila azaba ta sa ki kasa fita daga ɗakin ma ballantana ki nemi agajin Baba mai gadi, shikenan sai ki mutu a banza burin Sadam ya cika, ya ji daɗin auren shi'.
Wata zuciyar kuma ta shiga zuga ni da faɗin'Babu abin da zai faru, ki daure kawai ki yanka ki zare tsinke, ya zo ya same miki cikin jini dole hankalinsa zai tashi ya san tura ta kai ki bango, ƙila silar haka ya fara yi miki adalci.
Na dawo falo na zauna da wuƙar a hannu, na yi zuru ina tunanin na yi ko kar na yi? Na san dole akwai zafi, kuma yanzu safiya ce, awa nawa zan yi a cikin azabar nan? Sai dab da magriba yake dawowa fa, na daɗe ina ƙullawa da kuncewa kafin na bar shi a kan zan yanka ɗin, amma sai na ji dawowar shi gidan, yadda ba zan sha wuya sosai ba, da haka na mayar da wuƙar, na fara gyaran gidan, na gama na nemi waje na kwanta ina ta tunanin rayuwa, zuciyata cike da kewa, sai a yanzu ne da Sadam ya canza min hali ya juya min baya kaɗaici yake damuna, kaɗaicin haihuwa da na abokin shawara ko ƙawa.
Wayata na ɗakko na kira mahaifiyata muka gaisa, mun jima muna fira, amma na kasa faɗa mata damuwata, na san idan na faɗa mata planing na yi a duk tsayin shekaru ukun nan da aurenmu ya yi, shi yasa ban samu ciki ba za ta ga laifina sosai, kuma za ta yi min faɗa, musamman ganin yadda ta fi kowa nuna damuwa a kan rashin samun cikina, bayan mun gama na kira Babana, shi ma suka gaisa, sannan na kira ƙanwata Salma ita ma mun daɗe muna fira, ita dai Salma kamar ita ta tsarawa kanta, ba ta da wata matsala a gidan aurenta, kullum cikin yabon mijinta take yi, ga kuma ɗansu mai shekara ɗaya abun sha'awa, daga nan na kira Anisa, ƙawata kuma 'yar'uwarta, yau sai na ji kamar na bayyana mata damuwata, da kuma abin da nake shirin aikatawa ko za ta ba ta shawara, amma kuma ba na son a ga laifinta, don ni kaina sai yanzu nake raina wayona, na yi nadamar biyewa daɗin bakin namiji, kodayake umarni ma zan ce, tun da a lokacin ba na iya tsallake umarninsa shiyasa na amince da tsarinsa.
Ƙalau na gabatar da wunin ranar, na yi girki da yamma na ci, amma iya cikina, dab da zai dawo gidan na ɗakko wuƙar na zo falo na zauna, har da saka riga mara hannu don na ji daɗin gabatar da aikina, idan na tuna azabar da zan yi wa kaina sai hawaye ya ƙwace min, dab da magriba na ji ƙarar buɗe masa gate, na ɗauki wuƙar da sauri na runtse ido zuciya na ƙara zuga ni, na luma ta a daidai saman inda tsinken yake na yanka da ƙarfi, nan take kuwa na saki wuƙar ta faɗi, na ƙwalla ƙarar azaba ina fashewa da kuka, babu jira jini ya wanke min hannu, duk yadda na so na zaro tsinken haƙura na yi, saboda zafin da nake ji ba zai bari na taɓa wajen yankan ba, kwanciya na yi a wajen ina kuka riƙe da hannun.
Shi kuma kamar ya san tana neman taimakonsa, ya nemi waje ya zauna a baranda, Safna ta kira shi yana hanya ya ce mata idan ya ƙarasa zai kira ta, Safna ƙawarsa ce wacce ita ta maye gurbin Sayyada a yanzu ta fannin neman shawara da tattauna muhimman batutuwa, uwa-uba kuma matar da zai aura, sun shaƙu sosai, a asibitin da take aiki suka haɗu, lokacin ya shiga ganin likita, yanzu ma fira kawai suke yi tana jaddada masa yau a gidansu zai ci abincin dare, ya tabbatar mata da zai halarta, daga nan suka cigaba da fira.
Ina can kwance ina kukan azaba, shiru bai shigo ɗakin ba, ga shi ba na so ya gane ina nadamar yanka hannun nawa ballantana neman taimakonsa, sai da ya gama wayarsa a tsanake ya shigo ɗakin, kukana ne ya fara sauka a kunnensa, kafin ya gan ni riƙe da hannu jikina ya wanke da jini, zuciyarsa ta doka, ya saki wayar hannunsa da sauri ya ƙarasa inda nake yana cewa"Sayyada! Ke mene ne ya same ki?"
Ban ce komai ba sai kukana da ya tsananta, yana ganin wuƙar tsoro ya ƙara kama shi, da ƙarfi ya ce"Me ya same ki!? Kar ki ce mini yanka hannunki kika yi".
Cikin kuka na ce"Na gaji, wallahi yau ba zan kwana da tsinken cutarwar nan a jikina ba, cire shi zan yi, ko da zan mutu, indai kai a tsarinka ba ka son haihuwa da ni har abada to sai dai yau ka sake ni, na gama planing har abada".
Na kai hannu zan ɗauki wuƙar, ya riga ni ɗauka, duk ya firgice ya ce"Kin fara shaye-shaye ne Sayyada? Ko taɓin hankali kika samu?"
Duk da a raina na san ƙarya nake yi ba iya sake saka wuƙar zan yi a jikina ba, amma haka na daure na yunƙura da nufin ƙwacewa ina cewa"Ka ba ni! Ka ba ni na ƙarasa aikina Sadam, kuma ka sake ni na gaji da zama da kai".
A raunane ya ce"Ki yi haƙuri don Allah, mu ke na kai ki asibiti, jininki yana ta zuba fa".
Da ƙarfin hali na ce"Babu inda zan je, na fi so na mutu".
Ya rasa ma ta ina zai fara, ya tuna idan ya kaita asibiti za a zargi wani abu, don haka ya kira likitansu a waya ya sanar da shi abin da yake faruwa, ya ce ya kawo ta asibitin shi yanzu zai je ya same su, ya ajiye wayar yana cewa"Sayyada tashi mu je asibiti kin ji, za a cire miki shikenan".
Da ƙyar ya lallaɓa ni na yarda mu je asibitin, sai da na ga ran shi ya fara ɓaci, na ji tsoron ya yi zuciya ya rabu da ni, a mota muna tafiya yake cewa"Haba Sayyada ba ki kyauta min ba sam, wannan ai kin tona mana asiri, me yasa ba za ki faɗa min ke dole kin gaji da planing ɗin ba?"
Takaici kamar na buge bakinsa, da wane yaren yake nufin na nuna masa gajiyawata ya gane idan ba wannan fa na yi yanzu ba? Ban ce komai ba har muka ƙarasa asibitin, da yake asibiti ne mai zaman kansa kuma yana da hanya nan take aka shiga ba ni taimako ba tare da bin diddigin abin da ya faru ba.
Likitan sai nasiha yake mini bayan an gama yi mini É—inkin, ina ta hawaye, ya saka min ruwa, ya kalli Sadam ya ce"Zan yi mata allurar da za ta samu bacci".
Ya ce"Don Allah mu je gida ka yi mata".
Ya ce"A'a ba zan sallame ta a yau ba fa, a ƙalla ta yi kwana uku sai ku koma gidan na cigaba da zuwa ina duba ta, amma yanzu dai ba zan yarda ku tafi gida ba, kuma yana da kyau ta yi bacci".
Sadam ya shiga damuwa, ya ce"To tsaya mu yi magana da ita kafin allurar, la ba mu waje don Allah".
"Ok" kawai ya ce ya bar É—akin.
Ya zauna a gefen gadon yana kallona, kallon ma na kasa fassara shi, amma kamar ba na tausayi ba ne, sai dai kuma fuskarsa babu ɓacin rai sosai, ya ce"Amma wallahi ke daƙiƙiya ce, ban da hauka ta ya za ki aikata wannan shiryen? Yanzu idan 'yan'uwa suka ji uban me kike so mu ce musu? Yanzu da aka ba ki gado wa za a kira ya yi jinyarki?"
Na ce"To ai ba na shakkar kowa ya ji abin da ya faru, tun da dai na rabu da tsinken nan shikenan, idan ma zancen ya fito kai ne da kunya, kai ne za a zaga a ce ka cutar da ni".