← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 89

Sashe 48

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na shiga ɗakin har da saka sakata, saboda kawai gani nake yana shiga ɗakin Mama za ta faɗa masa, shi kuma shigowa ɗakina kawai zai yi ya rufe ni da duka, amma sai na ji shiru duk da haka ban nutsu ba, ga wayata da Mama ta karɓe, na tabbata Saddam zai neme ni.

Da gaske na yi nadama ba a iya fatar baki na faÉ—awa Mama ba, sai yanzu ma na ga wautata, na dinga istigfari, na yi niyyar zan haihu ko da ba zan sake samun wani mijin aure ba har abada, zan zauna na raini É—ana ko 'yata.

USTAZ

Tun da yana son ya tsira da mutincinsa sai ya haƙura da zuwa gidan su Sayyada, a ransa ya ce kuɗin zogalensa ma ya huta.

Yau ya je zance gidansu Rauda, yana ta ɗari-ɗari yana ganin matsayinsa bai kai ba, ita kuwa sai nan-nan take yi da shi, Allah ne ya ɗora mata soyayyar shi, sai da ta gaida da kowa na gidan, suna zaune a ɗakin baƙi yana ci abinci, yana yi mata wa'azin rashin amfanin cin abinci mai yawa, ba tare da ya ankara da yadda yake ta komawa cikinsa abincin ba, bayan ta gama cin abinci ta ce"To yanzu dai da gaske ka shirya auren ko? Don na san Abba yana dawowa idan ya ji ka fara zuwa zai ce to ka fito".

Ustaz ya kalli Rauda, ba wata kyakkyawa ba ce, amma 'yar gayu ce, hutu da gayu suna magana a jikinta, fatar nan luwai-luwai ko ba taɓa ta ya san za ta yi laushi, baƙa sai sheƙi take yi, ga ta da cikar halitta, don a wannan zaman da suke yi ma daurewa kawai yake yi, domin ya san tilas ya yi wankan tsarki idan ya koma gida, ta ce"Ka yi shiru kana ta kallona".

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To ai Raudatu ni tunanina ɗaya, kin ga fa ni talaka ne, ta yaya zan fara ajiye ki a gidana wanda zai kasance tamkar kurkuku a gareki? Ina nufin saboda ƙanƙantarsa da kuma ƙarancin kayan more rayuwa".

Ta yi murmushi ta ce"Malam ni ai kai nake so ba wasu kayan more rayuwa ba, indai za ka aure ni ka ba ni kulawa da soyayya ai ko a daji zan zauna".

Ustaz ya ce"Ai kuwa indai soyayya ce an zo wajen, za ki ga kulawa gaskiya, ina ga ma har sai ta yi miki yawa".

Ta ce"Dama kulawa tana yawa ne?"

Ya ce"To ni dai haka matan da na aura suke cewa, su na dame su, kuma na ga sai kana son mace da kuma sanin darajarta ne zai saka ka dinga yawan don kasancewa da ita? Ba haka ba ne Malama Rauda?"

Ta ce"Hakane mana, ai kuwa ba su da hankali, to ni yanzu idan an yi auren sai ka haɗa duka da kulawar da ka yi niyyar ba su, ka ba ni, Ni kam ko ba za ka dinga fita aiki ba sai zama tare da ni ina buƙatar hakan".

Ya ce"Alhamdulillah, to yanzu ya kenan?"

Ta ce"Duk yadda ka ce".

Ya ce"Zan je na fara tara abin da ya samu sai a san ko wata nawa za a saka ranar ko?"

Ta ce"Ni fa zan iya yafe maka lefen ma, ko kuma na ba ka kuÉ—in ka yi don kar ya zama abun magana".

Ustaz ya ce"Lala-lala, wannan ba zai faru ba, zan yi iya ƙarfina bi izininllah".

Suka cigaba da fira, sai da ya ji yana neman rasa nutsuwarsa gabadaya sannan ya yi mata sallama ya tafi, ransa fess yana ta hango yadda daren farkonsu zai kasance idan Allah Ya yi.

08028966015
[27/10, 8:06 pm] Sadiya Abdulrazak: 29

Kai tsaye gidan iyayen shi ya wuce, ya yi musu bayanin aure zai yi, ga kalar wacce zai aura kuma, babar shi ta fara faɗa tana nuna masa Rauda fa ba sa'ar auren shi ba ce, yana ta nuna mata ai ba za a samu matsala ba tun da ita ta ce tana son shi, ta ce"aAnya kuwa Ashiru? Har yaushe aka yi na Sayyada ka manta? Aure biyu duk ba ka yi dace ba, ya kamata ka haƙura ko kuma ka fara bincikawa ka ji mai irin larurrka, yanzu za a fara ƙirga maka aure fa, ana cewa auri saki ne da kai, nan gaba sai ka ga ka ƙi auruwa".

Ya ce"Zan faÉ—a mata in sha Allah".

Ta ce"Ni dai wallahi don ka dage ne Ashiru, amma yaran masu hannu da shunin nan idan suka auri talaka yawanci ana samun matsala, sai ka ga ta zama ita ce mijin ita ce mai tsara komai".

Ya ce"Umma ita fa Rauda ba ta da wannan halin, tana da kyakkyawar zuciya, na faɗa miki fa silar wa'azina da ta ji yasa ta kamu da sona, tana da tsoron Allah, tana da gudun duniya, in sha Allah ba za ta min irin wannan halin ba, kuma ai an ce tuwon girma miyarsa nama, don haka dole zan saki aljihu na dinga wadatata da kwatankwacin irin abin da take ci a gidansu, duk da ba zai yiwu na iya sak na gidansu ba, amma zan ƙoƙarta".

Ƙarshe dai da ta gaji ta ce Allah Ya ba da zaman lafiya.

Bayan kwana biyu mahaifin Rauda ya kira Ustaz, ya je gabansa sai faɗuwa yake yi, suka gaisa a mutunce, da alama yana da kirki, ba shi da halin raina arziƙin talaka, ya ce"Malam Ashir ko?"

Ustaz ya ce"E Abba, haka sunan yake".

Ya ce"Rauda ta sanar da ni kun sasanta kanku, kuma na yi nawa binciken a kanka, bincike ya tabbatar da aurenka biyu, babu É—a ko É—aya, hakane?"

Ustaz ya ce"Hakane, ita ta biyun ba a daɗe da rabuwa ba ma, don a yanzu haka ma zancen da ake yi, ba ta gama idda ba, to ka san ita iddar macen da ta kasance mai ciki bi ma'ana juna biyu shi ne ta haihu, ko yanzu aka sake ta bi ma'ana aure ya mutu, bayan minti ɗaya sai Allah Ya kawo haihuwa to fa ta kammala iddarta, kamar yadda ko cikin jikinta na kwana ɗaya ne, idan aure ya mutu sai ta haihu za ta gama idda, bi ma'ana sai ta yi wata tara, to hakan ne ya faru da ita tsohuwar matata Assayyada, ni ban san ma ta samu rabon ba, sai bayan an yi shi ɗalaƙin bi ma'ana sakin, sannan sai ciki ya bayyana, yanzu haka dai ina tunanin ya cika wata biyu, ka ga kenan ba ta kammala iddarta ba, wannan bayanin na yi ne domin gyara ko ƙara maka sani a kan maganar da ka ji a gari ta cewar ba ni da ɗa, bi ma'ana na haska maka ba wai haihuwa ce ba na yi ba, yanzu haka ɗana yana nan yana rayuwa a cikin tsohuwar matata, rabon ne dai a nesa shi yasa matar ta farko ba ta samu ba".

Abba ya ce"Ma sha Allah, Allah Ya raba lafiya".

Ustaz ya amsa da amin.

Abba ya ce"To amma ina son jin dalilin mutuwar auren naka, tun da duk bincike ya nuna ba a wani yi dogon zama ba".

Ustaz ya gyara zama ya ce"To Abba shi lamari na aure rai ne da shi, Allah ne shaidata duk macen da zan aura ina aurenta ne da zuciyata ɗaya, da kuma yaƙinin zan rayu da ita har ƙarshen rayuwata, amma sai dai kana taka Allah na tashi, ta Allah ita ce gaskiya, tsakani da Allah ba ni da wata matsala, kawai dai rashin dace ne, ita ta farkon ta raina samuna ne, ita kuma ta biyun nan dama ba auren soyayya ba ne, mahaifinta ne ya ba ni ita, to ashe ba ta sona, ta ƙi kwantar da hankalinta, ƙarshe dai shi mahaifin nata da kansa ma ya ce sai na sake ta, wallahi Abba ban so haka ba, don sai da suka kai ni kotu ma sannan na yi sakin nan, to ka ji dalili".

Abba ya yi shiru yana nazari, kafin ya ce"Mene ne sana'arka?"

Ustaza ya ce"A kasuwa nake, 'yan shadda, kuma ni ma yaron shago ne, amma dai Alhamdulillah ni babban yaro ne, kuma ana samu daidai gwargwado".

Abba ya ce"Ma sha Allah! To ni dai ba na yi wa yarana dole, ba na kuma auren haɗi, kowacce ina ba ta dama ta nemo wanda take so da kanta, domin a samu zaman lafiya bayan auren, Rauda ta ce kai ta zaɓa, ta ce ta ji ta gani za ta aureka, saboda haka ka shirya?"

Ustaz ya ce"E to, ba na ce na shirya ba ko ban shirya ba, a zahiri na shirya ko a yau ma idan ta kama za a ɗaura aure, to amma sauran hidindumu ne dai za su ɗan ja lokaci, kasancewata mai ƙaramin ƙarfi kuma zan auri buduruwa irin Rauda, dole akwai shiri na musamman".

Abba ya ce"Ta faɗa min ba ka da ƙarfi, kuma kai take so na kuɗinka ba, saboda haka indai akwai sadaki ka kawo kawai a ɗaura aure, sauran kayan duka ba wajibi ba ne".

Ustaz ya ji kamar ya tashi ya kama rawa don daÉ—i, ya ce"Alhamdulillah, ma sha Allah, na gode sosai Abba Allah Ya saka da alkhairi".

Abba ya ce"Babu komai, sannan har gidanka an nuna min, sai dai gaskiya gidan nan ya yi wa Rauda ƙanƙanta, ba wai na raina maka ba ne, amma idan ka duba inda aka haife ta ta girma, bai kamata a ce ta koma rayuwa a ƙaramin gida irin wannan ba, tabbas za ta takura".

Ustaz ya sunkuyar da kai ya ce"Hakane Abba, dama har da wannan tunanin ma ya sa na nuna mata ba mu dace da juna ba".
Chapter 48 · 0% Book details