← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 89

Sashe 53

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ya dawo gidan yake haɗiyar yawu, saboda sai a lokacin take yin pepper soup ɗin, yana so ya ci ga shi babu dama, ta gama ta shiga ɗaki za ta yi wanka, ya lallaɓa ya ɗauki guda ɗaya ya fita tsakar gida ya ci ya tauna ƙashin, sannan ya dawo falon, haka ta cinye tass a gabansa ko tayi ba ta yi masa ba, sai da ta je ta kwanta ya shiga kitchen ɗin ya lashe romon ya cinye ƙashin, a ransa yana faɗin Allah Ya isa, na cuci kaina Allah Ya ba ni ikon jurewa.

Da safe ma haka ya sha shayi da madara kaÉ—an, ita kuwa sabon gwangwanin ta buÉ—e ta zuba don ranta, takaici ya ishi Ustaz, sai da ta koma É—aki shi kuma ya shiga kitchen É—in don yin wanke-wanke ya haÉ—a wani shayin ya zuba kayan shayi wadatattu ya shanye, daga ranar kuma yake yin haka.

Aurensu yana yin wata ɗaya Babanta ya kira shi, ya faɗa masa ya sama masa gurbi a wani shagonsa, na siyar da kayan electronics, don haka idan ya shirya sai ya fara zuwa, Ustaz ya kamu da farinciki ya ce a shirye yake, ya dinga jero godiya, Abba ya ce"Babu komai Malam ai yi wa kai ne wannan, fatana dai ka kasance mai riƙe amana, idan na samu yadda nake so daga gare ka in sha Allah gaba zan ɗora ka a harkar shigo mana da kaya daga waje na zaman shago ba".

Ustaz ya dinga godiya daɗi kamar ya kashe shi, har ya fara hango shi ya zama babban attajiri, ai shirinsa na farko shi ne ƙara aure, don biyun sai ta fi daɗi

Yayinda ake yi wa Ustaz wannan albishir ita kuma Rauda tana zaune a falo suna waya da ƙawarta Zainab, faɗa mata take yi ita fa har yanzu an yi wata da auren nan lamarin babu canji, ta gaji ba za ta iya jurewa ba.

Zainab ta ce"Ko dai ke raguwa ce Rauda? Ni wallahi da zan samu ma mijina ya dawo kamar haka da na ji daÉ—i".

Rauda ta ce"Ba za ki gane ba ne Zee, ni dai gaskiya na gaji, dama fa sai da ya faÉ—a min shi hariji ne, ni ai ban san haka harijin yake ba, gabaÉ—aya na daina sha'awar sex É—in ma".

Zainab ta miƙe tsaye kamar Rauda tana kallonta ta ce"Hariji? Da gaske? Wai kina nufin ba minti biyar take yi ba zuwa goma?"

Rauda ta ce"Haba Zainab idan minti goma ne har kya ji kanmu? ko ashirin ma ai zan jure, sai ga na ture shi kawai, idan don ta shi ne ya kwana yana yi fa, wajen nan kullum sai na yi masa gashi sau uku ina dalili?"

Zainab ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Rauda kina cikin masifa da bala'i, kin san wane ne hariji kuwa?"

Gaban Rauda ya ba da rass, ta ce"Kamar ya bala'i?"

Zainab ta ce"To ai gara ma bala'i ke duk wani jafa'in duniyar nan kawai ma ki ce kina ciki, kin san kuwa akwai ƙanwata wacce muke 'yar wa da 'yar ƙani yanzu haka ta haukace silar auren hariji? To wata ƙawar maƙociyata ita ƙarshe ma mutuwa ta yi, mai kuɗi ne ta aure shi, ashe hariji ne, ya tisa ta a gaba, ta gudu gida iyayenta suka kora ta, ke abu yana gaba matar nan har ya kusa haɗe mata gabanta da bayanta, abu ya zama kamar ƙofar gari amma duk da haka bai saurara mata ba, wani dare yana cikin yin abun ya ji ta daina numfashi, sai da ya gama abunsa ya lura ta mutu".

Rauda ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".

Zainab ta ce"Ai Innalillahi tukunna ma, wallahi duk wacce ta auri Hariji kuma ta ce dole sai ta zauna da shi to fa ɗayn biyu ne zai faru, ko dai ya kashe ta, ko kuma ya mayar da ita harija ita ma abun ya daina isarta, kuma wallahi yawanci ƙarshe mutuwa ake yi, mutuwa za ki yi saboda kullum cikin huƙatar abun kike, idan kuma ya riga ki mutuwa ki kasa zaman aure, duk wanda kika aura ya gan ki a haka sakinki zai yi, don ba zai yarda ki kashe shi ba".

Rauda ta shiga tashin hankali, ta ce"Na shiga Zainab ya zan yi?"

Ta ce"Tabbas kin shiga uku wallahi, kuma kin yi kuskuren zama da shi har wata ɗaya, har ma mutum ya ce miki shi hariji ne kuma ki yarda ki aure shi? Lallai kin yi ganganci, Allah Ya ji ƙanki".

Rauda ta ce"Yanzu mene ne abun yi ya zan yi?"

Zainab ta ce"Tattara kayanki za ki yi ki tafi gidanmu ko sanar da su halin da ake ciki, idan kuma kin ga za ki iya ga wajen nan, sai mu ce Allah Ya kyauta makwanci".

Rauda ta ce"Amma fa ina son shi".

Zainab ta ce"A haf, To wallahi ya mayar da ke harija, kin ga sai anjima". Ta katse kiran.

Rauda ta zauna ta fara hawaye tana auna maganganun Zainab, tabbas da wannan abun sai a kashe mace wallahi, kenan ana nufin a haka za a rayu dama ba zai rage ba? Ai kuwa da sake, tana son shi amma hakan ba zai sa ta bari ya lahantata ba, don haka ta murɗa key a ƙofar kafin ya dawo.

08028966015
[31/10, 5:26 pm] Sadiya Abdulrazak: 32

Ustaz ya dawo gida da farincin samun aiki, dayake da mukullinsa yake buÉ—e gidan, ya buÉ—e ya shiga, ya shiga É—akin da sallamar shi, ya yi zaton har ta yi bacci, don haka ya rufe ko'ina ya kashe kayan kallo yana mita da faÉ—in"Allah Ya haÉ—a ni da shagalalliya, ba za ta daina kallon nanaye ba, kaico".

Ya nufi ɗakin nasu, ya tura ƙofar ya ji ta a rufe, ya fara ƙwanƙwasawa yana mamaki, Rauda ta yi banza da shi, ya leƙa ta windo ya hango ta a kan gadon ta juya baya kamar mai bacci, ya fara kiranta "Rauda, Rauda".

Ta yi banza da shi, kiran duniyar nan ta ƙi ko motsi, abun ya na shi mamaki don ya san tana ji, tun da a jikin window ya tsaya, kuka gadon babu nisa da windon, ya yi ƙwafa ransa duk ya ɓaci ya nufi kitchen, ya zuba abinci ya ci har da haɗa shayi, ya ɗan zauna a falon a ƙoƙarinsa na nuna mata fushinsa, ya yi zaton za ta zo ta buɗe ta nemi ya shigo ɗakin, idan ma wasa take yi masa ya yi mata bayanin miji ba abun wasa ba ne, ba ya son irin wannan wasan, sai ya ji shiru har goma ta wuce, ga shi lamarin jikinsa ya fara kankama taimakonta kawai yake buƙata, a dole ya tashi ya koma ɗakin ya cigaba da kiranta, ƙarshe ya kira wayarta, ta dinga ringing tana kusa da ita amma ta ƙi ɗauka, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, dabara ta faɗo masa ya ɗakko ruwa pure water ya ɓula ledar, ya zura ta windon saitin da take kwance ya fara jiƙata, ta tashi zauna tana ɓata rai ta ce"Malam lafiya mene ne haka?"

Ya hangame baki da mamaki ya ce"Rauda, shin kin makance ne ko magagin bacci ne bai sake ki ba? Bi ma'ana ba a hayyacinki kike ba?Ban gane lafiya ba, ai ke zan tambaya lafiya?"

Ta ce"Wallahi ba zan sake kwana ɗaki ɗaya da kai ba, don haka ka koma inda ka fito, don wallahi ba za ka kashe min rayuwa ba kwanana bai ƙare ba".

Ustaz ya ji wani tashin hankali ya ruguzo masa, ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Raudatu me kike nufi, yi min da larabci ko zan fi ganewa, bi ma'ana ban gane wannan yaren da kika yi min ba".

Ta ce"Kar Allah Ya sa ka gane".

Ya ce"Subhanallah, Ya Allah ka shaida na yafewa matata Rauda, sai dai ya za ta yi da hakkina da take shirin É—auka?".

Ya cigaba da buga ƙofar ya ce"Rauda buɗe mu yi magana ko za mu fahimci juna, babu kyau haramun ne ka dinga hora mutum da laifin da bai san ya yi ba, ki yi mini bayani me na yi miki?"

Ta ce"Kai hariji ne, kuma cutata kake yi, nema kake ma ka kashe ni, don haka ba zan iya ba, ba zan iya zama da hariji ba, a san abun yi kawai".

Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hana Rauda, idan kika yi min haka ba ki yi min adalci ba wallahi".

Ta kwanta ta juya masa baya, ya dafe kai kamar zai kurma ihu don takaici, ya ce"Raudata yi haƙuri daure kin ji ki buɗe min, in sha Allah za mu fahimci juna, idan kin gaji ne sai a duba a yi minus, a rage tun da dai ba zai yiwu a daina gabaɗaya ba ko?"

Ta yi banza da shi, ya ce"To Rauda a matsayina na mijinki ina nemanki, bi ma'ana ina buƙatar ki ba ni hakkina na aure, bi ma'ana a raya sunna, kuma kin san hukuncin macen da mijinta ya neme ta ta ƙi ba shi haɗin kai, idan na yafe miki ya za ki yi da tsinuwar mala'iku?"

Rauda dai ko motsi ba ta sake yi ba, ya dinga yi, ya yi wa'azi ya yi magiya, har bacci ya ɗauke ta da gaske, shi kuma ya gaji da tsayuwa, a dole ya koma wani ɗakin ya kwanta, sai dai ya kasa bacci sai da ya yi istimna'i, ga kuma fargaba da ta addabe shi, yanzu idan Rauda ma ta guje shi anya kuwa zai sake auruwa? Kuma babban tashin hankalinsa yanzu idan ta gudu ya matsayin aikinsa da babanta ya ba shi? Kar fa ya ƙwace abunsa, ai kuwa da sake, dole ya lallaɓata a yi minus, idan ya so ta dinga na shi na daren ma kawai ya haƙura, don ya sha wahalar zaman gwauranci bayan ya rabu da Sayyada, ba zai so ya maimaita ba.
Chapter 53 · 0% Book details