Sashe 59
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na fizge na ce"Kai ka ji haka".
Na fita daga motar na tafi, ko sallama bai yi min ba, saboda yanayin da yake ciki, na koma gida jikina a mace, ko da ya riƙe hannuna ban ji wani abu ba, sannan shigar shi wannan yanayin bai sa ni ma na ji sha'awar kasancewa da shi ba, ni tun bayan rabuwa da Ustaz ma ban ƙara jin sha'awar sex ba, shi yasa nake tunanin kawai ya kashe min sha'awa ne.
Ina son Sadam, ina fargabar wataran shaiɗan ya saka shi abin da ba zan so ba, alƙawari ba yi na bar saɓawa Allah ta hanyar zina, ba na fatan na sake aikatawa, don haka na fara shakkar haɗuwarmu da shi.
Duk yadda zuciya take faɗa min Sadam ba masoyi ba ne tun da ba ya son ɗana, haka na dinga ba ta uzurin kishi ne ya ja haka, kuma sai da so ake kishi, sannan ba dole ba ne don kana son uwa ka so ɗanta. Mun cigaba da soyayya ta waya, amma na daure zuciyata ban sake bari mun haɗu da shi ba, idan zan kai Abiy allura ba na faɗa masa, da ya tuhume ni na ce masa na daina kai shi saboda tana saka shi kuka, sai ya fara neman mu haɗu a wani wajen, nan ma na dinga fizgewa na nuna masa kwata-kwata ba na fita ko'ina, duk nacinsa na ƙi yarda mu haɗu, a shirina sai na yaye ɗana, na shirya auren, sai ya fara zuwa idan Allah Ya da iyaye sun amince da wuri sai a saka rana kadan a yi auren kowa ya huta.
Mun yi wata uku ba mu haÉ—u da shi ba, wanda ya yi daidai da watannin É—ana shida, ni kaina ina son ganin shi, amma ba na son kusancinmu, wataran da daddare bayan sallar isha'i duka muna tsakar gida har da Baba kawai sai ga yaro wai ana sallama da Sayyada, gabana ya ba da rass, duk da ban ma kawo Saddam ba ne, Mama ta kalle ni, Baba kuwa ya cigaba da cin abincinsa, ganin na yi shiru kuma ba ni da niyyar motsawa Baba ya ce"Sayyada ba da ke ake sallama ba?".
Na ce"Baba ai ban san ko wane ne ba".
Mama ta ce da dan aiken"Je ka tambayo wane ne".
Gabana ya shiga dukan tara-tara, ga Mama sai kallon tuhuma take yi min, na sunkuyar da kai ina wasa da hannun Abiy da ke zaune a kusa da ni, yaron ya dawo ya ce"Ya ce wai Isma'il ne".
Baba ya ce"Ka ce tana zuwa".
Sannan ya ce"Wa kuma kika samo?"
Na ce"Wallahi ban san shi ba, ba na kula kowa kuma ban haÉ—u da kowa ba".
Ya ce"Ai ba laifi ba ne, ki je ki gani".
Na shiga ɗaki na sako hijjabi na fita, Abiy yana miƙo min hannu ban ɗauke shi ba, Mama ta ɗauke shi, ina fita ƙofar gidan tun kafin na gan shi na ji ƙamshin turarensa, gabana ya tsananta faɗuwa, na ƙarasa inda yake zaune a babur na ce"Sadam, me ya kawo ka?"
Ya ce"Babu sallama ballantana gaisuwa?"
Na ce"Don Allah me yasa ka zo? Baba ma yana nan fa".
Ya ce"Sayyada har yaushe za mu kai muna ɓoye soyayyar nan ne?"
Na ce"Amma ai na faÉ—a maka sai na yaye É—ana zan yi aure".
Ya ce"Yanzu ya dace mu fito da soyayyar, sai a fara gwagwarmayar kafin ki yaye, kin ga zuwa lokacin kowa ya gaji ya sakar mana, kina yayewa sai batun auren kawai".
Na ce"A'a don Allah ka daina cewa haka, gaskiya ba yanzu ba, ban shirya ba tukuna".
Bai kula maganata ba, sai ƙure ni da kallo da ya yi, ya ce"Duk kin rame, yaro ya zuƙe ki sai yaushe za ki yaye shi?"
Kamar zan yi kuka na ce"Ka tafi Sadam don Allah".
Ya ce"Ba zan tafi ba, kuma yanzu ma na fara zuwa".
Na ce"Za ka ja min matsala".
Ya ce"To a ina za mu haÉ—u?"
Na ce"Nan da sati biyu zan je asibiti sai mu haÉ—u".
Ya ce"Kin yi alƙawarin za ki sanar da ni mu haɗu?"
Na ce"Wallahi na yi".
Ya ce"KuÉ—in hayar gidanki na ajiye miki ko na turo miki?"
Na ce"Ban gane ba".
Ya ce"Ok idan mun yi waya zan yi miki bayani, yanzu na tafi ba kya son ganina ko?"
Na ce"Ba haka ba ne, amma tsoro nake ji shiyasa".
Ya ce"Ok, sai anjima, i love You".
Ya ce"Ba za ki mayar min ba?"
Na ce"Ni dai ka tafi".
Ya ce"Ai kuwa ba ki so na tafi ba, wallahi sai kin faÉ—s zan tafi".
Yana rufe baki na ce"I love You".
Ya buga babur ɗin ya tafi, na dafe ƙirji, ina lumshe ido, na yi 'yan sakanni a haka sannan na shiga gida.
Ina shiga Mama ta ce"Wane ne shi? Kuma daga ina?"
Na ce"Wani ne, ban san daga inda yake ba".
Ta ce"To me ya kawo shi?"
Na ce"Na faÉ—a masa ba aure zan yi yanzu ba, sai na yaye".
Na shige É—aki ban jira wata tambayar ba.
Wajen goma na dare Sadam ya kira ni, muka gaisa na ce"Ka je gida lafiya"
Ya ce"Lafiya lau, kin ga alert?"
Na ce"A'a, layin da nake ganin alert É—in yanzu babu".
Ya ce"Ok na saka miki kuÉ—inki, dubu É—ari shida".
Na ce"Ni fa ban gane ba, wai da gaske ka bar min gidanka?"
Ya ce"In sha Allah! Ko yanzu kike so zan kawo miki takardun gidan, idan kin shirya a canza sunan zuwa naki".
Na ce"A'a, amma Sadam a kan me za ka ba ni gida?"
Ya ce"Saboda kin cancanta ne".
Na ce"Kyautar ta yi nauyi, na zai yiwu ba".
Ya ce"A bar zancen, yanzu ni a wane matsayi kika ajiye ni? A wace Larabar nake Sayyadata?"
Na ce"A cikin zuciyata kake".
Ya ce"Kuma na zo kika kore ni? Duk na rikice".
Na ce"Tsoro nake, amma in sha Allah da na yaye yaron nan komai zai daidaita".
Ya ce"Zan fara ƙirgen kwanaki har zuwa sati biyun".
Na ce"In sha Allah za mu haÉ—u, ai kamar yau ne".
Na ce"Ina matarka ne, ko ba ka gida?"
Ya ce"Ina gida mana, ga ta kusa da ni ma yanzu ta biyo ni É—akin".
Kishi ya kama ni na ce"To sai anjima".
Ya ce"A kan me? Ba fa yau muka fara waya da ke a gabanta ba".
Na ce"Kuma ba ta damuw?"
Ya ce"To idan ma ta damu ya za ta yi? Ko za ta hana ni ne?"
Na ce"A'a".
Muka taɓa fira muka yi sallama, ina jin bai kyautawa matarsa ba, ta wani fannin kuma daɗi nake ji, tun da ita ma kafin aurensu haka take yi min ai.
Tsakanin ni da shi ban san wanda ya fi wani zumuÉ—in cikar sati biyun ba, da ranar ta zo na yi kwalliya na tafi asibiti, bayan na gama kamar yadda na saba na fito na tarar da shi, na buÉ—e motarsa na shiga muka fara tafiya, a daidai inda muka saba tsayawa ya faka motar, ya kalle ni ya ce"Sayyadata".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Kina azabtar da ni sosai fa, na gaji da wannan jiran, da kin cire cikin da tuni yanzu kina gidana".
Na ce"Haka Allah Ya tsara".
Daidai nan adaidaitasahu ta ƙaraso wajen motar, Safna ta fito da sauri kamar za ta kifa, ta shiga ƙwanƙwasawa babu ƙaƙƙautawa, gaban Sayyada ya faɗi, Sadam yana kallon glass ɗin ya ga Safna shi ma gabansa ya faɗi, ɓacin rai ya lulluɓe shi, Safna ta buɗe murfin motar ta fizgo Sayyada, har Abiy ya gwara kanshi, amma dai ba ta fito da ita ba, Sadam ya fita daga motar, ya wanke Safna da mari ya ce"Ba ki da hankali? Ni sa'anki ne da za ki dinga bibiyata?"
Ta fara kuka ta ce"An bibiye ka É—in, munafukan banza da wofi, ashe a nan kuke haÉ—uwa? Uban me kuke yi a mota?"
Ya ce"Ubanki muke yi da kaza-kazanki, ki shige ki tafi gida ko ranki ya yi mummunan ɓaci".
Ta ce"Ba zan tafi ba! Ka daɗe ba ka ɓata min rai ba, munafiki kawai, dama tun da aurenta kake bibiyarta, to wallahi indai ka ce za ka dawo da ita sai an yi bala'in da ba ka taɓa gani ba".
Ya ce"To ki fara yi tun yanzu, don Sayyada kamar na aure ta, kuma a kanta zan iya rabuwa da ke, don ta fi ki amfani a wajena".
Ina motar ina kuka, ganin mutane sun fara taruwa na ji tsoro kar wanda ya san ni ya zo wajen a kai labari gida na shiga uku, ga shi ko niƙabi ban saka ba, don haka na fito daga motar ɗauke da ɗana, Saddam ya ce"Ki koma ki zauna".
Na ce"Ka rabu da ni gida zan tafi".
Ya ce"Ni ma gidan zan mayar da ke".
Na girgiza masa kai alamar a'a, na fara tafiya, duk yadda ya so ya tsayar da ni na ƙi tsayawa, na hau adaidaitasahun ya ja muka tafi, ya shiga motarsa shi ma rai a ɓace, ya bar Safna tsaye a wajen tana cigaba da zagina, kafin ita ma ta shiga adaidaitasahun ta bi bayana.
Ban san tana biye da ni ba sai na sauka a ƙofar gida, na ita ma ta fito daga adaidaitasahun, gabana ya yi mummunar faɗuwa, na ce"Me kika biyo ni ki yi min? Indai mijinki ne na rabu da shi, na bar miki".
Ta ce"Uwarki da ubanki na zo yi wa gargaÉ—i ai ba ke ba, don su ne sa'annin yina".
Hankalina ya tashi kamar zan yi kuka na ce"Don Allah ki yi haƙuri, wallahi na rabu da shi indai Saddam ne".
Ta bangaje ni ta shiga cikin gidan, na mara mata ina kukan nadamar fita a yau ɗin ma bakiɗaya, Mama ta miƙe tsaye a razane ganinmu wujiga-wujiga ta ce"Sayyada lafiya?"
Safna ta ce"Zuwa na yi na yi muku gargaÉ—i na farko kuma na karshe a kan mijina, ki raba kwartuwar 'yarki da bibiyar mijina, idan ba haka ba komai zai iya faruwa".
Mama ta ce"Ban gane ba me kike nufi?"