Sashe 41
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce"Subhanallah, Assayyada ni fa mijinki ne, ina da ikon taɓa ki, a yanzu haka ma ina da ikon da zan yi miki umarnin ki shige mu tafi gidana, idan kika bijire kuma ki shiga halaka, ko jiya mawuyacin halin da na shiga kina da zunubi mai girma, kuma sai Allah Ya tambaye ki, amma saboda adalci irin nawa sai na yafe miki, saboda haka ki bi a sannu, ina ta ƙoƙarin mu sasanta kina ta botsarewa, don Allah komai ya wuce Assayyada, za a dinga yin sau ɗaya kamar yadda kike so, zan jure ko da zan cutu".
Na ce"Gaskiya daga yau idan ka san ba ka da abin da za ka faɗa min kar ka sake zuwa wajena, don ba zan sake fitowa ba, kai na yaro ba ne da zan yi ta nuna maka gabas kana cewa yamma ce, aurenka na ce na gama shi, ni da komawa baƙin gidanka har abada".
Ya ce"Subhanallah, Assayyada..."
Na katse shi da faÉ—in"Kawai ka sake ni ta laluma tun ana ganin sauran mutuncin juna, ba sai an je kotu ba ka kunyata, indai za ka yi wa kanka adalci la san ka cuce ni, kuma zamanmu bai halatta na tun da akwai cutarwa a ciki".
Na shige gida, yana ta kirana ban dawo ba, ya gaji da tsayuwarsa ya tafi fa ledarsa.
Ina shiga na ga Mama tsaye a tsakar gidan, fuskarta da alamun damuwa ta ce"Ni Sayyada ko dai kina son mijinki ne? Idan komawa za ki yi ki yi bayani ba za a tauye ki ba, sai dai idan ya kashe ki mu ce Allah Ya ji ƙanki".
Na ce"Wallahi Mama ba na son shi, ai ke kika ce na fita".
Ta ce"Kuma da kike tsayawa kina sauraron shi ba a haka zai dinga kalaman da zai ribace ki ki koma ba? Hmm shikenan, idan za ki koma É—akinki babu wanda zai hana ki Sayyada".
Na shige ɗaki raina har ya fara ɓaci, kuma tun daga ranar na yi alƙawarin Ustaz ba zai ƙara ganina ba, a ranar da daddare da ya zo na ƙi fita, Mama ba ta ce min komai ba, kafin na kwanta bacci ya kira ni ban ɗauka ba, ya dinga jero min saƙonni na roƙo da nuni da yadda yake kewata, tun ina karantawa har na gaji na kashe wayar.
Tun daga nan fa kullum sai ya zo amma ba na fita, da ya dame ni da waya na saka shi a blacklist, watarana muna zaune ni da Mama a tsakar gida bayan sallar magriba sai ga sallamar shi, babu neman izini ya faÉ—o cikin gidan, Mama ta shiga laluben hijjabi, ni kuma na shige É—akinta da gudu, Mama ta ce masa"Lafiya dai ko?"
Ya ce"Lafiya ƙalau, dama Mama a kan maganata ce da Sayyada, ni na san a baya na yi laifi, na yarda ban kyauta ba, na yi abin da zai sa Sayyada ta ƙi ni, amma wallahi yanzu na canza, zan gyara halina, duk yadda ta tsara zaman haka za mu yi, don Allah ki taimake ni Mama ki saka baki, bi ma'ana ta yarda ta dawo mu zauna, darajar mace ɗakin mijinta fa".
Mama ta ce"Malam aure na mutum biyu ne, tun da ta ce ba ta yi kawai ka haƙura, ka cutar da yarinyar nan, cutar da idan muka yi ƙararka sai an bi mata hakkinta, amma muka rabu da kai, sannan ba mu hana ka biko ba, muka ba ka dama, sharaɗin dai ɗaya ne ita da kanta ta zaɓa zama da kai ko rabuwa, saboda kar a shiga hakkinta, don haka duk wanda ta zaɓa haka za mu bi".
Ya ce"Na fahimta Mama, amma dayake yanzu ta daina fitowa idan na zo, kuma ta daina ɗaga wayata sai ya zamana ba ni da wata hanya da zan iya cigaba da yaƙin bikon, wannan shirun nata yana azabtar da ni, ban san a wani matsayi ta ajiye ni ba".
Mama ta ce"To hakan yana nufin ba ta yarda da bikon ba kenan, don haka ka yi wa kanka adalci ka sake ta tun kafin a É—aga maganar zuwa gaba".
Ya ce"Subhanallah! Wallahi ba na jin zan iya jure rabuwa da ita, to idan na sake ta na auri wa?"
Mama ta ce"Wannan kuma ya rage naka".
Ta tashi ta shiga É—akin da nake, muka zauna jigum-jigum, ya shiga kirana da murya mai rauni, "Assayyada, Assayyada".
Ko kallon ƙofar fita daga ɗakin ban yi ba, haka ya zauna sai da aka yi kiran sallar isha'i ya fita daga gidan, da ya idar ya dawo ya yi zaune a ƙofar gida, sai da Baba ya dawo ya gan shi, ya tashi da sauri ya durƙusa yana gaishe shi, Baba ya ɓata rai kafin ya amsa, ya ce"Malam Ashiru lafiya dai ko?"
Ustaz ya ce"A lafiya lau Baba, kuma dama ba domin da matata a gidan ba ba za a dinga ganin yawan zuwana haka ba, Baba da za a tausaya a ba ni ita mu tafi da zuwan nawa zai taƙaita, wallahi zan canza".
Baba ya ce"Ita take zaune da kai, kuma na ba ka dama ka yi bikonta, ban tilasta ka sake ta ba, tun da kana ganin ka gama bikon da za ka iya, a yau ba sai gobe ba zan zaunar da ita na ji ra'ayinta na ƙarshe a kan batun aurenku, idan ta ce ta haƙura ku cigaba da zama, ni da kaina zan kira ka ka ɗauke ta ku tafi, kamar yadda idan ta ce ba za ta iya cigaba da zaman nan ba, da kaina zan nema mata takardarta, idan ka ƙi ta laluma zan ɗauki matakin shari'a don ba a kanka aka fara kashe auren hariji ba".
Daga haka Baba ya shiga gida, ya bar Ustaz gumi yana keto masa, ya rasa yadda zai yi, da me zai ji? Kullum sai ya sha baƙar wuya kafin ya damu bacci, azumi ma idan ya ɗauka karyewa yake yi, saboda yadda ya sa jarabar son kasancewa da Sayyada a ransa,duk ya firgice kana kallonsa za ka san ba ya cikin nutsuwarsa, ga kwandon zunubi da yake ta kwasa duk dare, saboda ba ya iya bacci sai ya biyawa kansa buƙata, sai dai yana yi yana fatan Allah Ya yafe masa.
Da ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya fita ya nemi wayar abokinsa ya daka lambar Sayyada, tana shiga ta É—auka, ya ce"Assalamu alaikum ya Assayyada".
Tana jin muryarsa ta kashe wayar, ya dinga kira ta ƙi ɗauka, haka ya haƙura ya koma gida, kwanciya ya yi a kujera yana ta tunanin irin zaman da suka yi da ita, sai yanzu ma ya gane yana sonta ba iya sha'awarta yake ji ba, da ya san haka za ta faru da ya yi haƙuri ya rage yawan buƙatarsa a kanta, da tuni yanzu suna tare, ko sau ɗaya ya samu a kullum ai ya rage zafi, gaskiyar masu iya magana da suka ce maraina kaɗan zai haƙura da babu, shi kam ya ga zahiri, bai ankara ba ya ji hawaye suna sakko masa, a fili ya ce"Ya Allah ga bawanka Ashir, Allah Ya taimake ni ka karkato da zuciyar baiwarka Sayyada gare ni, Allah ba zan iya ba ka iya min da iyawarka, Allah ka yi ikonka a kan lamarin nan, idan kuma zaman ya zo ƙarshe ka ba ni madadinta wacce ta fi ta juriya cikin gaggawa".
Dabara ta faɗo masa, ya ɗauki waya ya kunna data, ya nemi lambarta, cikin sa'a ya ga ba ta yi blocking ɗinsa ba, da sauri ya fara yi mata voice, ya ce"Assalamu alaikum, Assayyadata dama so yana zama ƙiyayya? Ban san mace mai neman albarka da gamawa da duniya lafiya tana gudun mijinta har haka ba, ina sonki Sayyada, kuma na ce na gane kuskurena, zan gyara wallahi, idan ma kin ce ba kullum za a dinga lamarin nan ba ni zan jure, bi ma'ana idan an yi yau gobe sai a huta, don Allah ki duba halin da zan shiga, kar ki bari a raba mu, sanyi ne zai shigo, ina azabtuwa ina kuma kwasar zunubi da yawa, don Allah ki gwada ba ni dama, Baba ya ce zai tambaye ki, daure ba don halina ba ki taimake ni ki ce kin yafe min, sannan shi ma ɓangaren cefanen zan gyara, ko busasshen kifi ne za a daure a dinga siya, irin bandar nan ai yana da tsoka sosai, ni dama ɗan abin da nake samu a kasuwar ne babu yawa, sannan kuma ana lallaɓa rayuwa saboda gujewa almubazzaranci da kuma ƙoƙarin zama zuhudu, tun da duniyar ma nawa take? Ki yi haƙuri kin ji, zuciya da gangar jiki na kewarki, daga mai mijinki har abada".
Lokacin ina kallace-kallacena a tiktok na ga shigowar saƙon shi, shaf na manta ban yi blocking ɗinsa ta WhatsApp ba, na duba na saurara, muryarsa sai rawa take a voice ɗin, kamar ma kuka yake yi, ko kaɗan ban ji tausayinsa ba, sai ma ƙara tsanarsa da na yi, sakamakon tunawa da irin zaman da muka yi da shi, wanda sai a yanzu ne ma nake ganin ƙoƙarina da wautata da na iya wannan dogon zaman da shi, na danna masa block, ina ajiye wayar dai ga kiran Baba daga tsakar gida, gabana ya faɗi, na tashi na fita na tarar da su zaune tare da Mama, da alama abinci ya gama ci, na zauna a gefe na sunkuyar da kai, saboda jikina ya ba ni maganar Ustaz zai yi min, ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am Baba".
Ya ce"Ya kuke ciki da batun mijinki ne? Kun gama magana ko har yanzu ba ku gama samun matsaya ba?"
Na ce"Baba mun gama, na faÉ—a masa ba zan koma ba".
Baba ya ce"To ma sha Allah, in sha Allah daga yanzu zan fara iya yi na don ganin an yi abin da ya kamata an wuce wajen, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Ya ce da Mama"Sai ku saka ranar da za ku je ku kwashe kaya".
Mama ta ce"Kuma tun yanzu ba a yi sakin ba?"