← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 89

Sashe 36

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kaina na san ba ni da ni'ima sosai, rabona da shan wani abu da sunan gyara jikina tun kafin na tare, tun da na san wa na aura na ga cewar shan magani ba nawa ba ne, duk da na san cewar yawan ni'imar zai kawo min sassauci, idan ya daɗe yana abu ɗaya, kuma wasu suna cewa idan ni'ima ta yi yawa namiji yana saurin samun gamsuwa, amma ina baƙicikin ya ji daɗik ya sa ina jin ba zan taɓa shan wani abu ba, na san sarai a buɗe nake, irin buɗewar da nake buƙatar matsi duk da ban taɓa haihuwa ba, to amma idan na gyara ma ai na yi banza, tun da lokaci ƙalilan zan sake buɗewa.

Na sha wahala sosai, zafin abun kawai nake ji, gani nake ko Allah Ya raba ni da shi kafin na mutu, to idan na yi wani auren sha'awata ba za ta dawo ba, saboda ya kashe ta murus, yau duk yadda na gaji ban ture shi ba, zuciyata dai tana ta zafi kamar zan mutu, sai da ya gama don kansa, lokacin gari ya waye, sannan ya koma gefe, a bazata na ji maganarsa ya ce"Allah wadaran naka ya lalace".

Na yi mamakin maganar, amma na shanye mamakin, na sauka daga gadon, da na yi wanka, kaya kawai na koma na ɗauka a ɗakin na koma falo na kwanta, ina jin kaina yana ciwo, da alama ya saba da kin yin girkina, yana yin wanka ya shiga kitchen, sarai na san gas ya ƙare, ina sane ban faɗa masa ba, babu jimawa sai ga shi ya shigo yana muzurai yana faɗin"Assayada, wai da me kike taƙama ne? Shin ba kya tunanin zuwan yaumu tubulas sara'ir? Idan mutuwa ta riske ki a wannan baƙin halin da kike nunawa mijinki me za ki ce da Allah?"

Zuwa yanzu maganganunsa sun daina firgita ni, don haka ko kallonsa ban yi ba, ya ɗora da faɗin"La ba'asa, na gano dalilin, wato ainafin kuskure na yi babba da ban ajiye miki gawayi ba, na bar ki har yanzu kina girki da gas, duk ƙoƙarin nan da na yi banki gani ba sai kin ƙure ni? A ce gas din ya ƙare ƙi ƙi sanar da ni sai yanzu da nake shirin na dafa abin da zan sakawa bakin salati na tafi neman halal?"

Sai ya koma É—akin gadon, ya dawo É—auke da wayarsa yana cewa"La budda laifina ne".

Ya zauna a kujerar nesa da ni, ya yi danne-danne a wayar ya kar a kunne, babu jimawa na ji yana"Assalamu alaikum, Baba barka da safiya".

Gabana ya ba da rass, suka gaisa, ya ce"Wato Baba dama wani lamari ne yake faruwa a nan gidan namu, tun da Sayyada ta dawo daga asibiti sau ɗaya ta yi girki a gidan nan, shi ma ina kyautata zaton ta yi ne saboda ta ga kifi a cikin cefanen, to Baba a ce Shikenan ko ba ni da kuɗi sai na siyo kifi kullum za ta yi girki? Ta daina girki ta daina gaishe ni, dau na yi mata magana sau dubu ba za ta kalle ni ba, rayuwar aure za ta yiwu a haka? Duk haƙurina Sayyada ta fara kai ni bango, don Allah Baba idan kun isa da ita s daure a yi mata magana ko za ta ji, duk da dai ni na yafe mata ma".

Ban ji me Baba yake cewa ba, amma na ji Ustaz yana ta ba shi haƙuri yana ce masa ai ya yafe min, amma dai a yi min magana.

Ya gama wayar ya kalle ni ya ce"To bari mu ga kina jin maganar iyayenki ko kuwa rafkanar ta ki ta saka har iyayen ma ba su da wannan tasirin?"

Ya fita ya bar ɗakin, na san wayata a kashe take, kuma ina sane yanzu Baba yana can yana kirana, amma na ƙi kunna wayar, sai ga Ustaz ya dawo ya miƙo min wayar, na karɓa na kara a kunne na yi sallama, na gaishe shi, ya amsa ya dora da faɗin"Sayyada me yake damunki ne?"

Na ce"Baba babu komai".

Ya ce"To wani sabon wulaƙancin ne kika tsiro da shi haka wanda za ki dinga mayar da mijinki ba a bakin komai ba?"

Na yi shiru, ya ce "Ba magana nake yi miki ba? Ko wani laifin ya yi miki?"

Na ce"Bai yi min komai ba".

Ya ce"To akan me kika canza kika tsiro da wannan wulaƙanci?"

Na ce"A yi haƙuri Baba, zan gyara".

Ya ce"Maza ki ba shi haƙuri, kuma kar na sake jin irin wannan ƙorafin daga mijinki, don kina zubar da ƙimar gidanmu ne".

Na ce"To, a yi haƙuri".

Na miƙa masa wayar ina kallon gefe na ce"Ka yi haƙuri".

Ya ce"Subhanallah! Assayyada anya kuwa kina tuna sai na ɗaga ƙafata za ki shiga aljanna? A hala za ki ba ni haƙuri ba za ki duƙursa ba? Ni fa mijinki ne? Gaskiya da gyara a lamarinki, sai kuma na yi zancen ƙara aure ki ce za ki tada kishi, shiriritar banza kenan, yanzu kin ji maganar tasa ko kuwa da saura?"

Na ce"Na ji".

Ya fita daga gidan, sai ga shi ya dawo da leda, shayi ne ya siyo shi a leda ƙulli biyu, sai biredi kamar wanda ya saba siya, ya zuba nashi a kofi ya bar min sauran, na ce"Ka haɗa ka shanye ni ba sha zan yi ba".

Ya ce"Hmm! Assayyadda kenan".

Ya gama abinda zai yi ya fita kasuwa, sai lokacin ma tashi na zubo ruwan zafina dake cikin fulas na haɗa shayi na sha, na share gidan, na fita na siyo maganin ciwon kai, na yi cefanena, wajen sha biyu na rana sai ga shi ya zo da murhun gawayi, da kuma gawayin ƙulli biyu, da taliya leda ɗaya sai kayan miya, ya ce"Ga wannan, ina ga gas ɗin nan sai ki matsar da shi gefe, saboda halin rayuwa, a koma amfani da gawayi kawai".

Ban ce komai ba, na kunna gawayin, zan fara gyara kayan miya ya kwala min kira, kamar na yi banza da shi, sai kuma na tuna umarnin Baba zan bi ba nashi ba, don haka na je, na tarar da shi babu kaya, yana miƙo min hannu, na kau da kai ban yi magana ba, kuma ban ƙarasa ba, ya ce"Taho mana Assayyadda, gafin gawayin ya kama, sai a toshe wani wajen".

Na kasa yin ko taku É—aya ballantana na je, sai shi ne ya zo ya ja ni zuwa gadon, duk azabar da nake ji haka na daure ban hana shi ba, fata nake yi wahala ta kashe ni kawai, kiran sallar sha biyu da rabi ne ya cece ni, ya fara faÉ—in "Subhanallah! Ba kya tuna min kin kunna gawayi?"

Ya fita yana cewa"La haula wa la ƙuwwata illa billah, kin ga yanzu ga shi an yi asarar rabin gawayin, wato ainafin ya fara zama toka".

Ya fito daga banɗakin, ni ma na shiga, ina fitowa na ɗauki ɗayan ƙullin gawayin zan ƙara, daidai sanda ya fito daga ɗaki, ya ce"Lala-lala, kul Assayyadda, wannan ai na gobe ne, ki fifita ki ɗora a haka, ai tun da taliya ce tana saurin dahuwa".

Na ajiye, na gyara kayan miya, na É—ora tukunyar, ya ce"To sai ki kula wajen tsayar da sanwar, taliyar za ki dafa biyu bisa uku ne, bi ma'ana ki raba ta gida uku, sai a ajiye kashi É—aya gobe da safe idan Allah Ya sa muna cikin rayayyu kuma lafiyayyu sai mu dafa mu karya da ita".

Ya tafi masallaci, yana dawowa ya shuga ɗaki ya kwanta, ban shiga ɗakin ba sai da na gama dafawa, kamar yadda na yi zato bacci ne ya kwashe shi, ko wannan rashin samun wadataccen baccin ba zai bar shi ya yi ƙiba ba, na ajiye masa abincin, ban tashe shi ba, na yi alwala na tada sallah, na idar ina zaune a sallayar ya farka, ya fara ƙorafin me ya sa ban tashe shi ba, ya ce na zo mu ci abincin, nan ma ban kalle shi ba, ya cinye tass sannan ta hau tambaya ta gida ukun na raba? Ban ba shi amsa ba, ya fice daga gidan yana cewa"Allahu yahdiki Assayyadda".

Dab da magriba na fita bakin titi na siyo tsire da yogurt, na ci na ƙoshi, da daddare da ya dawo na ba shi sauran taliyarsa, ya cinye tass, ga shi dai daga rana zuwa dare shi kaɗai ya cinye leda ɗaya, amma saboda son zuciya ya ce mu biyu ma ba za mu ci leda ɗaya ba, bai gaji ba da daren ma ana yin sallar isha'i ya ja ni zuwa ɗaki, yana cewa"Ɗan karatun ma kin daina kin watsar, tun da irin wannan karatun kawai kike so ai sai mu yi ta yi".

Tun daga ranar nake yin girki safe da rana, wataran na yi nawa da ban, wataran kuma na siyo nama na yi miya idan na yi girkin sai na ci nawa da miyata, yawan ciwon kai da nake yi yana damuna, yanzu har na gaji da shan maganin, sai na ji ya yi tsanani sosai nake sha, na kashe wayata, don ba iya media ba duka duniyar ma kawai ji nake ta ishe ni, ga ciwon ƙirji da nake ji kaɗan-kaɗan, duk da ba ni da ulser, ni kaina na san ina buƙatar ganin likita, idan na yi tunanin zuwa asibiti sai na ga me na zan je na yi? Ni da so nake ma na mutu? Sai na fasa zuwa, a yanzu tsakanina da Ustaz ya ba ni umarni ne kawai na aiwatar, sai na yi kwana uku cif ban furta masa kalma ɗaya ba, ban da karatun sallah fa ba na buɗe baki da nufin yin magana, abincin ma na rage ci, ba na wani sha'awar cin komai, ina ci ne don maganin yunwa.
Chapter 36 · 0% Book details