← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 89

Sashe 4

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ƙarfe ɗaya na dare na farka, na bi ɗakin da nake da kallo, zuciyata ta fara zafi, ƙwalla ta zubo min, tunawa da duk ni na ja wa kaina kasancewata a nan ɗin, na kalli hannu na da ke naɗe da bandeji, yana yi min zafi har yanzu, hawaye ya sakko min, cikin wayam yunwa nake ji, fitsarin da nake ji da kuma tunanin ban yi sallar magriba ba da isha'i ba, ya sa na yunƙura na tashi zaune, gabana ya faɗi ganin wata kwance a ƙasan gadon, tsoro kuma ya ɗan kama ni, duk da na yi tunanin Sadam ne ya aiko ta, to amma wace ce? Na san dai ƙanwarsa Amna ko mutuwa zan yi ba za ta zo ta zauna da ni ba, saboda tsanar da ta yi min, kuma ban da ita ba shi da wata ƙanwa, sannan ba zai iya zuwa ya faɗa a gidanmu ba ballantana na ce ko Khadija aka ba shi, wannan ma babba ce ta fi Khadija ƙanwata, da wannan saƙe-saƙen na yi hanyar banɗaki, sai kuma idona ta sauka a kan wayata, na ɗauka na buɗe ta, da text massage na fara cin karo, wanda ke ɗauke da cewar "Ki duba na ajiye miki saƙo a whatsApp mai muhimmanci".

Da sauri na kunna data na shiga whatsApp ɗin, hannuna har rawa yake yi, saƙon da na gani da baƙuwar lambar na fara buɗewa, na danna vedios ɗin, wanda take ba shi abinci a ba ki na fara gani, ina karanta maganar kuma hankalina ya ƙara tashi, wallahi saura kaɗan fitsarin da nake ya kufce min, da sauri na ƙarasa banɗakin riƙe da wayar ina jin kamar na saka kuka, kafin na yi alwala sai da na karasa kallon sauran, tabbas na gane kitchen dina, ga kuma falona, kuma shikenan ba ni da damar sake kallon vedion ballantana na kafa shaida da shi, zargina ya zama gaskiya, yau dai ta tabbata mijina yana neman mata, kamar yana jira na bar gidan? Na fashe da kuka sosai, ina alwala ina kukan, sai da na fito daga banɗakin na share hawayen, na ajiye wayar a gadon na shiga tashin wacce take baccin.

"Baiwar Allah" Na faɗa ina taɓa ƙafarta, ta farka ta yaye fuskarta daga lulluɓar, gabana ya faɗi ganin ban santa ba, ban taɓa ganinta ba, za ta girmi tun a kallo ɗaya.

Safna ta ce"Anti Sayyada sannu, kin tashi ashe".

Na ce"Yawwa, amma wace ce ke?"

Ta ce"Ƙanwar Yaya Sadam ce, zuwa ya yi gidan ya ɗakko ni zan kula da ke".

Na ce"Na gode, ara min hijjabin zan yi sallah".

Ta É—akko jaka tana cewa "Ai ya haÉ—o miki ma da hijjabi a cikin kayanki".

Na karɓa na saka, ta tashi ta ba ni sallayar na tada sallah, kafin na idar ta haɗa mini shayi, ta zuba min macaroni da kazar, zuciyata zafi take yi min, shi yasa na ɗaga hannu na daɗe ina ta addu'a Allah Ya sassauta mini abin da nake ji, har sai da na ji mai ciwon ya dame ni da zafi, sannan na sauke, ta kalle ni ta ce"Sannu Anti Sayyada ga abinci".

Yunwa nake ji don haka na yunƙura zan ɗauka, amma da na tuna wai wata ce ta dafa abincin sai na koma na zauna, ƙwalla ta kawo idona na ce"Ya sunanki ke ɗin? Kuma ban san ki a 'yan'uwan shi ba".

Ta yi murmushi ta ce"Sunana Hafsa, kuma ni da babar shi da babata uwa É—aya uba É—aya suke, ina yawan zuwa gidan ai, don dai ba kya zuwa ne sosai, su ma kuma 'yan gidan ban ga suna zuwa gidan naku ba shiyasa ba za ki san ni ba".

Na ce"Ok, amma wannan abincin daga ina aka same shi?"

Ta ce"E to, ni dai ya kawo ne kawai".

Na ji sam ba zan iya ci ba, ba zan iya cin abin da karuwarsa ta dafa ba, duk da yunwar da nake ji haka na ƙi ci, na sha iya shayin, na ci ayaba, ta ba ni magani na sha na koma na kwanta ina jin zuciyata tana yi min nauyi.

Sadam ya daɗe yana cutata, ya daɗe yana ƙuntata mini, tun kafin ya aure ni yake gana min azaba, sai yaushe ne zan fara morar garɗin soyayya wai? Bayan aurenmu na yi zaton shikenan ni da baƙinciki sai hange daga nesa, ashe zaman yana can a gaba, zuciyata dai ta dinga zuga ni a kan na bar asibitin nan kawai na tafi na je na rutsa shi da karuwar a yi wacce za a yi, ba tare da dogon tunani ba na tashi, na sauka daga gadon, na zura hijjabi, Safna ta kalle ni ta ce"Anti ina za ki je?"

Na ce"Gida zan tafi, ni na ji sauƙi".

Sai ta tashi da sauri ta ce"A'a don Allah ki yi haƙuri ki zauna har sai an sallame ki, kuma yanzu dare ya yi ma".

Tsaki kawai na yi, na buɗe ƙofar na fita, da gudu ita ma ta fito ta shiga ofishin likitocin, ta sanar da su, sai ga likitan ya fito da saurinsa ya taddo ni ya ce"Madam ya haka, mene ne ya faru?"

Na ce"Ka sallame ni kawai ni a gida zan kwana".

Ya ce"Ki yi haƙuri ba zai yiwu na sallame ki yau ba, sai dai ko zuwa gobe, kin ga dare ya yi ai".

Sai kawai na fara hawaye, sai yanzu ma na yi tunanin ba zan samu abun hawa ba ai, ya ce"Ki yi haƙuri ki koma pls".

Safna ta kama hannuna tana ba ni haƙuri ita ma, ta ja ni sai na bi ta muka koma ɗakin, baccin da ban koma ba kenan, na ga tsayin daren sosai, na yi kuka na ƙoshi, na kuma tuna abubuwa da dama wanda a yanzu nake ndamar aikata su.

Da asuba Safna tana yin sallah ta ce za ta tafi gida, za ta dawo min da abinci, na yi mata godiya, da ta fita tsayawa ta yi ta kira Sadam a waya ta faɗa masa ta bar asibitin, ya kamata shi ya je, ya ce"Na gode sosai Baby, amma fa ni ba zan fita yanzu ba gaskiya, sai zan tafi aiki sai na leƙa ta".

Ta ce"Amma fa ya kamata ka je da wuri, don jiyan ma cewa ta yi ba za ta kwana a asibiti ba da ƙyar ta haƙura, likitan ya ce yau zai sallame ta".

Ya ce"Au haka ma za ta yi? Ai da ya bar ta ta dawo ɗin, ta zauna idan hannun ya riɓe aka yanke kin ga ni ba zan zauna da musaka ba ai".

Safna ta yi dariya ta ce"Ba ma zai faru ba, ka je dai don Allah, sai ka kai mata abincin kari, jiya shayi kawai ta sha".

Ya ce"Gaskiya ni za ta takura ni, bacci bai ishe ni ba, ina ta tunanin ya kika kwana".

Ta ce"Ya na kwana ko dai ya matarka ta kwana?"

Ya ce"Wallahi ke nake tunani, an É—ora miki nauyin da ba naki ba, ga shi ina fargabar kar ta gano wace ce ke a samu matsala".

Ta yi dariya ta ce"Idan ma aka gane ba na jin za a samu matsala ai na ga Antin tawa tana da haƙuri".

Ya ce"Za ki jira na zo na É—auke ki?"

Ta ce"A'a zan tafi a adaidaitasahu, zan yo muku girkin kai da ita sai na dawo".

Ya ce"Me zai hana ki zo ki yi a nan gidan namu? Please".

Ta ce"To bari na zo É—in".

Ta ɗan jima a tsaye kafin ta samu adaidaitasahu ta hau, ta kama hanyar gidan Sadam, da ta ƙarasa kiransa ta yi ya zo ya buɗe mata, suka ƙara gaisawa, ta shiga kitchen da sauri, ya bi bayanta yana jin yadda yanayinsa yake canzawa, sai dai yana ta ƙoƙarin dannewa, kayan ciki ta gyara ta ɗora sannan ta ɗora shayi, ta ɗakko doya tana firewa, shi kuma yana ta kallonta fa burgewa, ji yake ina ma a ce an yi auren matarsa ce, da babu abin da zai hana shi rungume ta ko zai ji sassaucin yadda sha'awarta take gigita shi, amma babu dama, a gaskiya bai taɓa gwada yi mata ko maganar batsa ba, bai sani ba ko za ta amince da romance, ya dinga sauke numfarfashi, yana amsa mata firar da take yi masa da e, ac, har dai ta ce"Beb ko ba ka da lafiya ne?"

Ya ce"Lafiya ba lau ba".

Ta ce"Mene ne yake damunka?"

Ya ce"Ke ce, kewarki ce za ta kassara ni".

Ta ce"Kewa kuma? Ba gamu a tare ba?"

Ya ce"Ba irin wannan kasancewar ba ai, zan so wacce ta fi wannan kusanci".

Ta yi murmushi ta ce"Ni dai ban gane ba, kuma ba na so na na gane, pls mu bar zancen".

"Ok" Kawai ya ce, ya tashi ya bar kitchen ɗin, ta bi shi da kallon tausayi cikin shauƙin so da ƙauna.

Har ta kammala komai bai dawo kitchen É—in ba, ta zuba wanda za a kai wa Sayyada, ta zuba masa na shi ta fito falon, ta same shi kwance a kujera, ta ajiye tana cewa"Na yi zaton ma ka yi wanka kana karyawa sai dai kawai ka tafi kai mata?"

Ya sauke numfashi ya ce"Yanzu zan yi, za ki taya ni ko?"

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ta ce"Ka ci abincin".

Ya ce"Ki zo mu ci mana".

Ta girgiza kai alamar a'a.

Ya ce"Don Allah zauna mu ci, ya min yawa ma ai".

Ta zauna suna ci suna kallon soyayya da murmushi, har wanke-wanke ta yi ta gyara komai tsaf, ta juyo za ta bar kitchen É—in, ta gan shi tsaye ya tare hanya, kuma ba kamar É—azu ba da yake da jallabiya a jikinsa, yanzu gajeren wando ne kawai a jikinsa, da alamar kuma daga wanka ya fito, tsoro ya kama ta, kafin ta yi magana ya ce"Safna can I give you a huge? Please my wife to be".

SAYYADA
Chapter 4 · 0% Book details