← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 89

Sashe 25

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi bai turo ba, kamar wanda aka maƙale jikinmu da gum, amma a wannan karon ya saurara ya ce"Subhanallah! Haka ya ke Assayyada, shin kin san ɗumbin ladan dake ɗanfare da wannan ibada kuwa? Ba ki san cewa ana sakawa a rai tamkar mutum ya shiga filin yaƙi ba ne yana kashe arna? Kin san dai yaƙi da arna jahadi ne babba ko? Daure ya ke matata mu ƙarasa raya wannan dare mai albarka da tarihi a gare mu".

Na ce"Na gaji sosai, don Allah ka rabu da ni haka a bar wa gobe komai".

Ya ce"La ba'asa, amma dai... Kodayake na yi miki uzuri tun da akwai gajiyar taro a tare da ke, na yafe miki".

Ya matsa gefe yana cewa"Sannu, na gode sosai Assayada, da asuba ma ƙarasa idan kin huta".

So na yi na yi bacci a yadda nake É—in, amma ya yi min dole na je na yi wanka, na kwanta bacci ya É—auke ni, don ban ma ji fitowarsa daga wanka ba.

Na yi mamakin ganin yana sallar dare da na farka, na kuma ji daɗi da bai tashe ni ba, saboda har ga Allah ba zan iya ba, ƙarfina ya kusa ƙarewa, da asuba ya tashe ni na yi sallah, kafin ya dawo daga masallaci na koma gado bacci ya fara fizga ta, sautin muryarsa ne ya wartsakar da ni kamar munafuki yake cewa"Assayyada kin huta mu ƙarasa yaƙin? Babu fa'idar barin arnan nan fa".

08028066015
[08/10, 4:40 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, KU YI MIN ADALCI KU BIYA NI HAKKINA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015

16

Gabana ya faÉ—i da jin furucinsa, ni fa a yadda nake jin kaina nan da jibi ma ba zai samu ba, ya rage kayan jikinsa ya hau gadon yana cewa"Assayyada kin huta?"

Kamar zan yi kuka na ce"A'a".

Ya janyo ni jikinsa yana cewa"Haba, haba Assayyadata, ni fa jiya ma kin ba ni mamaki, har na fara tunanin anya kuwa irin larurarmu É—aya? Ki ka ce ke ma..."

Bai ƙarasa ba na ce"Ni ba harija ba ce, ban san abin naka ya yi tsanani haka, don Allah ka tausaya min".

Ya ce"Subhanallah!".

Sai ya yi shiru na É—an lokaci, kafin ya ce"To yanzu dai tun da ba kya so ba zan matsa miki ba, idan don ta ni ne ki bar ni a wahale, to amma sai dai wannan laifi ba ni kika yi wa, da Allah kike, bi ma'ana yanzu za ki shiga sahun matan da mala'ikun Allah za su dinga tsine musu, ba za su gushe suna tsine miki ba har sai lokacin da na aminta da ke, bi ma'ana na yafe miki".

Na ji ya kashe min jiki da wannan wa'azin, na san shi tun muna islamiyya, amma ina tuna wahalar da na sha daren jira, sannan idan zai yi min adalci ai bai kamata ya yi fushi da ni ba.

Ya yi gyaran murya ya ce"Assayyada shin za ki iya jure tsinuwar mala'iku? Yau ko wani bawan Allah ne ko wani malami ya saka sunanki a gaba yana tsinewa ya za ki ji? Ballantana kuma a ce mala'iku wanda ba sa saɓawa Allah sai bautarsa, wa iyazubillah! Sayyada ki duba lamarin".

Na fara hawaye na ce"Don Allah ka yafe min to, ka aminta da ni, da daddare zan ba ka in sha Allah!".

Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Subhanallah! Assayyada da dai za ki taimaka ɗin, kin ga jiya ma daga ƙarshe kamar korata kika yi, sai dai na dubi Allah na yafe miki, tausaya ni ma ki yi min adalci mana"

Na ce"To shikenan".

Haka ya ɗora daga inda ya tsaya, ina ta hawaye, sai da gari ya waye tangararan, shi ma ga ni ya yi sautin kukan nawa yana ƙaruwa ne, ya ƙyale ni, amma duk wannan sadaukarwa da na yi masa sai cewa ya ce"La ba'asa Ya Assayyada, amma dai ki shirya kafin na dawo daga kasuwa".

A raina na ce'ba sai ka same ni a É—akin naka ba?'

A fili kuma ko kallonsa ban yi ba, na kasa tashi, har ya yi wanka ya fito, ya ce"Na lura kamar jikinki babu ƙwari ko? Bari na dafa mana shayin".

Ban kula shi ba, saboda lokaci É—aya na fara jin haushinsa, ya shiga kitchen, ya kunna gas don a cike aka kawo shi gidan, ya dafo shayin, a falo ya karya, sannan ya shirya zai tafi kasuwa duk ina kwance, ya shigo É—akin ya zauna ya fara yi mini nasiha a kan zama da janaba, ya É—ora da faÉ—in"Da kin san matsalolin zama da janaba da ko da rarrafe kin shiga banÉ—aki kin yi wanka".

Na ce"Na ji, zan tashi".

Ya ce"La ba'asa, bari na tafi kasuwa, ga abincinki can a falo, wajen sha biyu haka zan dawo gidan, zan kawo miki abin da za a dafa da rana".

Na ce"To a dawo lafiya".

Ya tsaya yana kallona ,irin kallon nan mai cike da sha'awa, na kau da kai ina ɓata rai, ya sauke numfashi ya ce"La ba'asa, amma yana da kyau mu zauna da ke mu yi karatun muhimmancin ba wa miji cikakken hakkinsa".

Na ce"Au yanzu ban gamsar da kai ba kenan?"

Ya ce"La la la la, ni ban ce ba, kin dai yi iya yinki amma akwai gyara a lamarinki Assayada".

Ya fita daga É—akin yana cewa"Sai na dawo, don Allah ki tashi ki samu tsarki".

Na sake cewa"A dawo lafiya".

Na tashi bayan ya fita, na saka sakata a ƙofar gidan, na shiga banɗaki na yi wanka, sannan na yi na sabulu ma, na fito na shirya, na shiga falo, cikin ƙaramin kofi mai murfi na hangi shayin nawa a can ƙasan kofi, ga kuma guntun biredin da ya rage min, shayin ma har ya yi sanyi, kuma ba zan ƙoshi ba, takaici ya kama ni ban san sanda na fashe da kuka ba, na tuna gidan Sadam, komai na abinci ga shi nan danƙam a store, sai wanda na ga dama da shi zan karya, na haɗa shayi mai matuƙar kauri, yau ga ni a gidan aurena da abu a gabana kamar an ci an ragewa almajira, yunwa nake ji, don haka na ci, na shiga kitchen na ga farantin sauran kazar jiya, ashe bai cinye ba, na ɗauka na cinye, na gyara gidan na kwanta, tunawa da na yi ba lallai ya ƙyale ni ba yau ma, ga kuma wajen nan ya ɗaure min duk babu daɗi, na dafa ruwan zafi na shiga na zauna, na ɗan ji daɗi a jikina, na kwanta bacci ya ɗauke ni, bugun gida ne ya tashe ni, na je na buɗe idona cike da bacci, shi ɗin ne ya dawo da leda a hannunsa, ya shigo da babur ɗin, yana cewa"Ya subhanah! Haba Assayyadata ban yi zaton haka daga gare ki ba".

Na ce"Me na yi?"

Ya ce"Ta ya za ki zo ki buɗe ƙofa kai tsaye ba tare da kin san ko wane ne ba? Ai ya kamata ki fara saka hijjabi yadda ko an samu matsala wani bai ga jikinki ba".

Na ce"Yi haƙuri, zan dinga sakawa".

Ya yi murmushi ya ce"Ko ke fa".

Na ce"Sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa".

Muka shiga falon, ya ce ga wannan sai a dafa ko, amma kafin nan, zan so a ce kin taimake ni, bi ma'ana mu ɗan keɓe ko na 'yan mintuna ne".

Gabana ya faɗi na ce"Mu keɓe kuma? Ka manta ka yi fa safen nan?"

Ya ce"Ban manta ba, ai a baya na faɗa miki nakan yi kira a ƙalla sau biyar ne a rana, shi ma fa saboda al'amuran rayuwa ne, tun da dai ai ba don shi kaɗai aka halicce mu ba".

Ya tashi ya dawo kusa da ni yana naniƙata, da muryar kuka na ce"Don Allah ka yi haƙuri, gaskiya na gaji, ba zan iya ba".

Ya ce"Subhanallah! Ya Allah ina nemawa matata Assayyada yafiyarka, Allah na yafe mata, ban yi fushi da ita ba".

Na fara shassheƙar kuka, ya marairaice ya ce"Don Allah ki tausaya min, na kasa zaman kasuwar, ni azabar Allah ma na fi jiye miki, ba halin da zan shiga ba".

Na ce"To, amma don Allah ka dinga yi min adalci, idan aka cigaba da tafiya a haka zan cutu".

Ya ce"Za ki saba in sha Allah, Allah Ya yi miki albarka".

Da Allah Ya taimake ni yanzu dai bai wuce minti ashirin ba, na yakice shi da ƙyar, ƙafafuna har harɗewa suke yi, jikina duka ciwo don ma dai ba shi da ƙiba, na yi wanka, na shiga kitchen don ɗora girki, amma na kasa komai na zauna na fara kuka.

Ya shigo bayan ya yi wanka ya ce"Subhanallah! Assayyada lafiya? Mene ne ya saka ki kuka?"

Na share hawayen na ce"Babu komai".

Na janyo ledar ina cewa"Me zan dafa?"

Ya ce"Ki yi macaroni da miya, akwai sauran kazar jiya sai ki saka a cikin miyar".

Ban kula shi ba saboda takaici, ya ce"Hanzarta, na ci na koma kasuwa".

Ya koma É—aki ya kwanta bacci ya É—auke shi.

Na dafa macaronin leda ɗaya da miyar jajjage, na zuba na zauna na ci a kitchen ɗin, na sha ruwa, sai yanzu na ƙoshi tun da na zo gidan, na zuba na shi a faranti na zuba ruwa a kofi na kai masa, na same shi yana bacci, a raina na ce'Ai dole ka yi bacci mana, jarababbe kawai'.

Kamar na tashe shi, sai kuma na rabu da shi, na zauna ina ɓata rai, sai ga shi ringing ɗin wayarsa ya tashe shi, ya tashi a firgice yana cewa"Subhanallah" Sannan ya karanto addu'a tashi daga bacci, ya ɗauki wayar yana cewa ga shi nan zuwa, yana gamawa ya kalle ni ya ce"Assayyada me ya hana ki tashe ni? Zan koma kasuwa fa"

Na ce"Ai na san kana buƙatar baccin shiyasa".

Ya ce"Ai akwai lamuran da suka fi baccin a daidai wannan lokacin".

Ban ce komai ba, ya fita ya kuskure baki, ya dawo, ya ja abincin, ya ce"Bisimillah, matso mu ci".

Na ce"Na ci nawa".

Ya ce"To kuma kin ci naki kika ciko min faranti har haka? Wannan ai ya yi min yawa".
Chapter 25 · 0% Book details