← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 89

Sashe 81

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ustaz ya ce"Habawa ai ba ko fi ni uzurin nan ba, to amma kin san yana da kyau bawa ya fara da tuna mahaliccinsa, kasancewar na saba sallar dare, ga kuma yau biyu ta haɗu, kar na je na kasa haƙuri ya zamana ban yi sallar ba, shi yasa na ce bari na fara yi, bi ma'ana ba sai na yi ta tsakiyar daren ba, amma dai kar ki ce na shiga hakkinki".

Ta sake shi ta ce"To ka yi, amma don Allah ka yi raka'a biyu, wallahi na gaji".

Ya ce"Kar ki damu, indai ni ne ai naki ne har sai kin ture".

Ta haye katifar ta kwanta, yana idarwa ya kashe hasken ɗakin ya je gare ta, idan ka shiga ɗakin dai ka yi zaton wasu mayunwatan zakuna ne aka haɗa su suke gabza gumurzu, tsakani da Allah Ustaz abun ya yi masa sugar, a cikin matansa dama Rauda ce kawai take yin gyara, ita ma kuma baya-baya ba kamar irin wannan da Rakiya ta yi ba, lallai yau ya tabbata biyu ta haɗu, domin kuwa tun ƙarfe tara ake abu ba ta ce masa ta gaji ba har ƙarfe ɗaya, don gamsuwa bai yi gamsuwar da zai ce wai ya gaji ba, sai dai fa ya fara jin bacci, don haka ya ce mata"Ruƙayya yaya, ba ki gaji ba?"

Ta ce"Kai haba wace irin gajiya? Ai ni sai yanzu ma na san an fara lamarin, ƙara dai ko awa biyu ne mu ga abin da hali zai yi".

Domin kar ta ga rauninsa sai ya ƙara zage damtse, bayan minti talatin ya ce"Ruƙayya yanzu fa?"

Ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kar dai guduwa na yi ban tsira ba? Wai me kake nufi ne Malam Ashiru? Ba dai ka gaji ba? Yau ga mugun abu ni Rakiya".

Ustaz ya ce"Ba fa gajiya na yi ba Ruƙayya, to amma ba za mu yi bacci ba? Gaskiya bacci nake ji wallahi, amma don gajiya ko gamsuwa nima duk ban yi ba, amma wai dama da sai a bawa gangar jiki hakkinta, bi ma'ana bacci".

Rakiya ta ce"Tsakani da Allah yau babu lissafin bacci a jadawalin rayuwata, ka rufa min asiri mu cigaba, don wallahi idan ka bar ni yanzu to har gara ma ba ka yi ba".

Ya ce"Ke Ruƙayya, Ya Subhanallah, yanzu fa awa huɗu da rabi kenan, to ko goɗiya ce aka tisa ta a gaba zuwa yanzu ai kuwa sai dai ta ce ba ta ƙoshi ba, ba dai ta ce ba a taɓa ta ba".

Ta ce"Ni dai ka yi haƙuri ka cigaba, don gaskiya baccin nan sai dai ka haƙura gobe ka fanshe".

Ustaz ya cigaba da yaƙi, sai dai fa da gaske bacci yake ji, kuma ya gaji, gajiya ta gangar jiki ba wai ta kashe arna ba, da ƙarfe uku ta yi alarm ɗin wayarsa ya buga ya miƙe da sauri ya ce"Kin ji alarm, da yake ina yin sallah a daidai lokacin nan, bari na yi ko raka'a biyu ce sai kuma na kwanta, wallahi bacci idona har ruwa yake yi".

Rakiya ta miƙe ta ruƙo shi ta ce"Ka rufa min asiri Malam, wallahi idan ka bar ni haka haukata ni za ka yi, ya ina yabonka sallah za ka kasa alwala? Daure munƙarasa ladanmu".

Ustaz ya ce"La ba'asa, Shikanan mu je, amma dai abun akwai shiga hakki, bi ma'ana yau na shiga hakkin idanuna, ban yi bacci ba har gari zai waye".

Da suka koma da ƙyar ya samu ya ƙwaci kansa ƙarfe huɗu, ko wanka bai yi ba bacci ya rafke shi, da alarm ya tashe shi sallar asuba da ƙyar ya tashi, ya yi wanka ya tafi masallaci, da ya dawo ya tarar tana bacci a sallaya, hakan ya ba shi tabbacin ta tashi ta yi sallah, ya koma katifar ya cigaba da bacci.

Can cikin bacci ya ji ana shafa shi, ya razana ya buÉ—e ido, ya ga gari ya waye sosai, ya yi ido huÉ—u da Rakiya haihuwar uwarta, ya ce"To Allah Ya yi dare gari ya waye kenan".

Ta ce"Ƙwarai kuwa, ka fi shayi kuma za mu dosa".

Ya tashi zaune ya ce"Wallahi ki saka kayanki idan za ki saka, domin ni nan ba moruwa zan yi ba".

Ta ce"Ban gane ba za ka moru ba, anya kuwa kai hariji ne?"

Takaici ya kama shi jin za ta mayar da shi rago, ya ce"Cikakke ma kuwa, amma ki tuna da rabona da abinci tun jiya da safe, ko kazar ba ki bari mun ci ba kika farmake ni, hana Ya ke Ruƙayya a dinga sara ana duban bakin gatari mana".

Ita ma yunwar take ji, amma wannan abu ya fiye mata abinci, shi yasa ta fara neman shi, ta tsaya tana kallon jikinsa tana haÉ—iyar yawu, gabansa ya faÉ—i, a ransa ya ce'Shikenan Umma ta haÉ—a ni da me gani har hanji, Allah ka dubi bawanka'.

Ta fitar da ƙaramin gas ɗinta waje, ta dafa musu shayi, suka ci da biredi, sannan suka ci kazar, ya ce"To ma sha Allah, Alhamdulillah, bari na je mu gaisa da ita Raudatu daga can kuma zan wuce wajen aiki".

Ta ce"Haba Malam ya muka yi da kai? Yanzu fa ƙarfe tara, ƙila ma bacci take yi".

Ya ce"A'a idan ta tashi da asuba ba ta komawa bacci".

Ta ce"Ko dai ka gaji ne"

Shi kam ba ya so ta raina shi ta dinga cewa ya gaji, don haka ya ce"Wai me kika mayar da ni ne? Jiyan ma fa gajiyar É—aurin aure ce, da kuma bacci da nake ji, amma yau za ki sha mamaki".

Zai fita ta tare ƙofar ta ce"Na rantse da Allah da ka ƙi ba ni wannan ka fi shayin gara ka hana ni kuɗin cefane".

Ustaz ya ce"To fa! Wata sabuwa".

Haka ya haƙura aka shiga fagen yaƙi, ƙarfe goma da rabi ya ƙwaci kansa, don Rauda sai kiran wayar shi take.

Ya yi wa Rakiya sallama, wacce ta biyo shi har tsakar gidan, ba ta daina shafa shi ba shi kuwa sai mazewa yake, kamar tana shafa dutse, ya ce mata zai yi aiken kayan abinci da cefane, sai da ta ga shigar shi É—akin Rauda sannan ta koma É—aki ta kwanta ta fara bacci.

Ustaz yana shiga ya ga Rauda ta cika ta batse, ya maze suka gaisa, ta ce"Ai na yi zaton ba za ma ka fita aikin ba yau".

Ya ce"A haba, zan fita mana, bacci ne ya ci ƙarfina".

Ta ce"Dole ya ci ƙarfinka ai, tun da jiya ba ka runtsa ba, ka samu abin da ba na baka".

Ya ce"Haba Rauda, wallahi kina ba ni, sai fa kin yi haƙuri Rauda a hankali za ki saba ai".

Ta kanta a jikinsa ta ce"Jiya na kasa bacci saboda kewarka, gaskiya ina buƙatarka, taso mu je ɗaki".

Gabansa ya ba da rass, ya ce"Haba dai Raudata, kin san dai yau ba ranar kwananki ba ce, sai fa na yi kwanaki uku zan dawo nan, ki daure kin ji? Kamar yau ne".

Ta ce"Gaskiya Ni dai a'a".

Ya ce"To ai kuma ba zai yiwu ba tun da ba ke ce da girki ba".

Ta ce"Amma ai ba haramun ba ne ko?"

Ya ce"E to...amma dai da kin daure ɗin, idan na yi haka tamkar cin fuska ne a gare ta, bi ma'ana ita Ruƙayya ɗin".

Ta saki baki"Au kana so ka nuna min a jiyan kawai har ka fara sonta kenan ko? Tun da ga shi ba ka so ka yi mata cin fuska".

Sai ta yi fushi ta yi ɗakinta, a ranta kuwa fata take yi ya biyo ta rarrashi, ta saka shi dole ya ba ta hakkinta, shi kuwa Ustaz sai ya yi wa kansa ƙiyamul laili ya fice daga ɗakin da sauri, ya bar gidan yana mitar za su mayar da shi inji".

08028966015
[18/11, 10:52 am] Sadiya Abdulrazak: 48

A wajen aikin ma yana ta tunanin ita Rakiya wace ce ita a nau'in harijai? Bacci sam bai ishe shi ba, haka dai yake ta daurewa, wajen sha biyu da rabi ya kira Rauda a waya, ya ce don Allah ta zubawa Rakiya abinci kafin ya kawo mata yanzu, ta ce ba za ta bayar ba har da rantsuwarta, ga shi babu yaron da zai aika, kuma fargabar komawa gidan yake yi, duk da a yanzu yana jin zai iya yi, to amma ita fa Rakiya abin da za a duba ba ta san zuru ba, yanzu idan ya je ta damƙe shi ya san sai marina, don haks ya ƙi zuwa, sai wajen ƙarfe ɗaya ya aika mata da kayan abincin, amma ya sa a sayi dafaffe a kai mata, bai sani ba ko tana can tana jin yunwa.

Rakiya bayan fitarsa ta gyara ɗakinta ta fito tsakar gida ta share tass, ta je ta ci gaba da baccinta, ba ta ma farka ba ballantana ta ji yunwar, sai da ɗan aiken ya zo kawo kayan, ta ci abincin ta yi sallah, ta yi miƙa, sai ta ji ai kawai so take ta ji mijinta a kusa da ita, ta ɗauki waya ta kira shi, suka gaisa ta ce"Me za a dafa maka da rana?"

Ya ce"A'a ni ba sai na dawo ba".

Ta ce"Haba don Allah, kenan haka za ka zauna da yunwa?"

Ya ce"Ai siya nake na ci, kar ki damu babu komai".

Ta ce"Amma dai zan yi kewarka gaskiya ka dawo da wuri".

Ya ce"In sha Allah".

Ya kashe yana hararar wayar, a ransa ya ce'Wannan akwai jaraba.

Da yamma ya koma gidan, Rakiya tana jin ƙara buɗe gida ta gane shi ne, tun da ba ta ji alamun Rauda ta fita ba, ta fito tsakar gidan, yana shigowa ta ruga da gudu ta tare shi, Ustaz ya fara murmushin yaƙe, sai dai shi ma nan take ya ji lamura sun fara canza masa, abubuwa suka motsa, ta ja shi suka tafi ɗaki, ita Rauda tun da ta ji dawowar shi ta yi zaton wajenta zai fara zuwa ya ga lafiyarta, amma sai ta ji shiru,don da suka damƙi juna da ƙyar ya yakice ta, shi ma don uzurin sallah ne yasa ta haƙura, ta ce"Don Allah ana idarwa ka dawo".

Ya ce"Ai ba sai kin faÉ—a ba".
Chapter 81 · 0% Book details