Sashe 61
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce"Sayyada idan kin yarda ni ubanki ne, to daga yau na raba ki da Sadam, kuma na haramta miki fita ko'ina, ko ƙofar gida ban yarda ki fita ba, kina yaye yaron nan zan samo miki mijin da ya dace da ke ki yi aure, idan kika taka dokata dama tun kafin na ji labari ki tabbatar kin haɗa kayanki kin bar gidan nan, don haɗuwata da ke ba za ta yi miki daɗi ba".
Na tashi na shiga ɗakin, na hau gyara kayana ina kuka, haka na yi wunin ƙungi, Mama ta ɗauke min wuta, da daddare sai ga yaro wai ana sallama da Sayyada injiSadam, ga shi Baba yana nan, ya tashi ya fita, ban san dai ya suka yi ba, amma na tabbata ba magana me daɗi zai faɗa masa ba.
Babu ta inda nake jin sassauci, na rasa ya zan yi, sati ɗayan da na yi na Sadam ba waya sai na ji kamar ba na raye, ni kaɗai na san uƙubar da nake ji a zuciyata, haka na fara gudanar da sabuwar rayuwa mai cike da kewar Sadam, cikin zuciyata kuwa na ƙudurce zan rayu babu aure, matuƙar Baba ba zai yi min auren dole ba, duk wanda ya kawo min zan ce bai yi min ba har ya haƙura ya daina kawowa.
Da zaman kaɗaici ya ishe ni, wataran na roƙi Baba na ce don Allah ya siya min rediyo, ya siyo min 'yar madaidaiciya, na dinga saurara, daga wannan tashar na koma wancen.
USTAZ
A kwana a tashi lokacin haihuwar Rauda ya yi, haihuwar ta zo mata da sauƙi, don da asuba ma sun kashe arna, kuma da safe wajen ƙarfe sha ɗaya ta haifi ɗanta namiji, Ustaz ya saki aljihu daidai ƙarfinsa, duk da abin da aka yi mata daga gidansu ya fi wanda ya yi, ya siya tinkiya babba, babanta kuma ya aiko da rago, aka haɗa aka yanka.
Wannan shiga jegon da Rauda ta yi shi ya canzawa Ustaz lissafi, ya so ƙwarai ta zauna ta yi wanka a gidansa, amma iyayenta suka ce sai ta tafi gida, shi kuma ba zai iya yin musu da su ba, shi yasa ya haƙura, amma yana cutuwa, haka yake shan juyi a gado kafin bacci ya ɗauke shi, don ma dai kullum sai ya je gidan, kuma yana ɗan taɓa jikinta.
A wannan gaɓar ya fara tunanin ya kamata ya ƙara aure tun yanzu, ba dole sai ya jira ya yi kuɗin da yake fata ba, tun da yanzu ma Alhamdulillah yana da halin riƙe mata biyun, don haka ya samu wata ƙanwar abokinsa ya fara kula ta, kuma aka yi sa'a ta amince tana son shi, dama ba a daɗe da fasa aurenta ba, Rauda tana can tana zaman wankan jego, shi kuma yana nan yana soyewa da budurwarsa Zulaiha, sam ba shi da niyyar faɗa mata larurarsa saboda yana ganin ai tun da su biyu ne za a samu sassauci, idan yau ya gajiyar da ita gobe ba ya ɗakinta sai ta huta, a ganinsa duk rakin mace ba za ta yi ƙorafi ba.
Rauda ta dawo gidan da sati biyu, Ustaz ya je takanas ya samu mahaifinta da zancen yana sha'awar ƙara aure, ya ɗora da faɗin"Shawara ce dai nake nema, a matsayinka na uba a gare ni Daddy, duk yadda ka ce zan ɗauki shawararka".
Daddy ya ce"Malam Ashir ko da ni ne na haife ka ba ni da hurumin saka ko hana ka a fannin ƙara aure, a dai ra'ayina kenan, mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo, idan kana bukatar ƙara aurenka ai ba na jin sai ka yi shawara da wani, abu ɗaya dai shi ne ku tattauna da ita Rauda, idan ta amince Alhamdulillah, idan kuma ba ta amince ba sai a yi abin da ya dace".
Ya ce"In sha Allahu ma za ta amince Daddy, kuma ni wallahi ba ta gaza min ba, to kawai dai dama can ina da ra'ayi shi ne yasa".
Daddy ya ce"Babu komai Allah Ya zaɓa mafi alkhairi".
Suka yi sallama ya tafi, haka ya dinga jinjina yadda zai fuskance ta da batun, ya dai daure ya zaunar da ita ya fara yi mata fira cikin jimami na yadda 'yan mata manya da ƙanana, da zawarawa da iyayen marayu suka yawaita a gari babu aure, babu mashinshini, ya ce"Wato abun akwai ainahin taɓa zuciya, da kuma tausayawa, auren irin waɗan nan matan zai iya zama jihadi mai girma".
Rauda sam ba ta fuskanci inda zancen nasa ya dosa ba, ta ce"Hakane, Allah Ya ba su mazaje na gari".
Ya ce"Amin".
Suka É—an yi shiru, sannan ya ce"Raudatu".
Ta ce"Na'am".
Ya ce"Shin za ki iya taimakawa al'umma ta hanyar kwantar da hankalinki idan na auri É—aya daga cikin waÉ—an nan matan?"
Gabanta ya ba da rass, ta ƙanƙance ido ta ce"Me kake nufi?"
Ya ce"Ina nufin na gano wata yarinya, bi ma'ana mun sasanta, in sha Allah zan aure ta".
A fusace ta ce"Tabdijan, ai kuwa uban kuturu ma ya yi kaɗan, na rantse da Allah ba zan taɓa zama da kishiya ba har abada, ashe watan rabuwa da ni ya tsaya maka kenan".
Ya ce"Ya subhanallah , subhanallah, Rauda ki yi gaggawar faÉ—in Astagfirullah, domin ina jiye miki azabar Allah, duk da ni fa na yafe miki".
A fusace ta ce"Kar ka yafe É—in, ka daÉ—e ba ka yafe ba, ma yaudari kawai, ashe maza duka haka kuke? To wallahi ba da ni za a cigaba da wannan zaman ba, dole sai ka sake ni a yau É—in nan".
Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Rauda don Allah zauna mu fahimci juna kin ji, idan ba kya son ganin ta sai na raba muku gida ma".
Ta yi tsaki ta bar falon, ta shiga É—aki ta saka sakata, haka suka kwana a É—aki da ban da ban, Ustaz hankalinsa ya tashi, saboda yana son Rauda ko don juriyar da take yi da shi, bai shirya rabuwa da ita ba, uwa-uba yana tsoron kar su rabu ubanta ya ba shi jan kati, shi yasa duk ya firgice.
Washegari da sassafe ta haɗa kayanta, lokacin yana bacci ta fice daga gidan, ta ƙarasa gida tana kuka da faɗin sai dai ya sake ta, ran mahaifiyarta ya ɓaci sosai, ta hau faɗa da zagin Ustaz tana ce masa butulu, Daddy ya taka mata burki ya ce ai ƙarin aure ba haramun ba ne, sai dai babu wanda zai yi wa Rauda dole, idan ta ga ba za ta iya zama da kishiya ba to shi zai saka ya sake ta, kuma tun da ba ita ce ta ba shi aiki ba kar ta sake ce masa butulu.
Sanda Ustaz ya fahimci Rauda ba ta gidan ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba, ko wanka bai tsaya yi ba, ballantana ya nemi abinci, hala ya tafi gidansu da jallabiya, ya durƙusa a gaban Daddy yana ba shi haƙuri, Daddy ya ce"Wannan ba komai ba ne Malam Ashir, tun da ta ce ba za ta iya zaman ba ina ba ka shawara ka sake ta".
Ustaz gabansa ya faɗi ya ce"Amma Daddy ba zan so lalacewar alaƙarmu ba, yanzu shikenan sai na daina aiki a ƙarƙashinka ko?"
Ya ce"Sam, haka ba zai faru ba, alaƙarka da matarka ce kawai za ta katse, amma batun aiki yanzu ma muka fara, kamar yadda na yi maka alƙawari, wani watan in sha Allah za ka je Cotonou ma, na yarda da amanarka saboda haka idan ka ga na bar aiki da kai to kai ne ka buƙaci hakan".
Ya ce"Ba zan ma buƙata ba Daddy, Allah Ya saka da alkhairi".
Ya ce"Amin, yanzu yaya kenan? Za ka ba ni takardarta ko kuma a hannunta za ka ba ta?"
Ustaz ya ce"Daddy don Allah a yi haƙuri a ba ni lokaci na gana da ita tukunna, in sha Allah zan lallaɓata ta amince".
Ya ce"To Allah Ya zaba muku abin da yake alkhairi".
Ustaz ya amsa da Amin, ya tashi ya shiga nufi falon.
08028966015
[05/11, 8:20 pm] Sadiya Abdulrazak: 37
Ya daÉ—e a falon kafin ya samu Rauda ta fito, ya gyara zama ya ce"Sannu da fitowa Hajiyata".
Ta ɓata rai ta zauna kamar ba ita ba.
Ya ce"Ma sha Allah! To na zo ne dama a kan maganarmu, na yi mamakin yadda kika iya tafiya ba tare da sanina, kin manta hukuncin matar da ta fita ba tare da izinin mijinta ba? Duk taku É—aya fa da kika yi mala'ilu tsine miki suke yi, idan don ta ni ne na yafe miki, to amma ya za ki yi da hukuncin da Allah Ya tanadarwa macen da ta fita ba tare da izini ba?"
Ta ce"Ka faÉ—i abin da ya kawo ka kawai, tun da ka yafe min sauran tsakanina da mahaliccina ne ai, Allah gafurur rahim ne".
Ya ce"Hmm, to la ba'asa, yanzu ya ake ciki? Sulhu khair, Rauda ki nutsu mu yi sulhu".
Ta ce"Wallahi ba ka ɗakko hanyar sulhu ba, maslaharka ɗaya ce kawai ka sake ni, ba zan taɓa iya zama da kishiya ba".
Ya ce"To ga shi ni kuma ba zan fasa auren da na yi niyya ba, tun da ai taimakon wani jihadi ne".
Ta ce"To sai ka sake ni".
Ya ce"Ba zan sake ki ba, tun da ni ba butulu ba ne".
Ta ce"Ai kuwa wallahi ya zama dole ka sake ni, don ni ba zan zauna da kishiya, kuma ban da butulcin mata nawa ka aura kuka rabu? Kuma na san duk hatijancinka ne ya raba ku, amma ni na jure saboda ina sonka da kuma tausayin aure-auren da kake yi, shi ne za ka ce za ka ƙara aure, to ka je ka yi, la auri wacce kake tunanin za ta iya da kai, ni kam na gama zaman aure da kai".