← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 89

Sashe 12

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabana ya faɗi, na nutsu tsam ina ta auna kalamansa a raina, ya ce"Kin ga ba mu san da wane yanayi cikin zai zo ba, ƙila ki yi ta laulayi duk ki rame ki fita a hayyacinki kuma kin san idon danginki yana kanmu, yanzu sai a fara yi miki dariya ana zaton wahala kike sha a gidan, amma idan kika huta kika yi ƙiba muka sha soyayyarmu idan haihuwar ta zo ma sai mun fi marmarinta, amma ya kika gani?"

Na ce"Amma anya babu matsala kuwa? Ni a ra'ayina ko haihuwa É—aya ce na yi kafin planing".

Ya ce"To ni dai ga yadda na tsara mana, idan kuma ke ce mijin ni matar sai ki yi naki tsarin".

Ya janye jikinsa ya juya min baya, hawaye ya sakko min, Allah Ya jarabce ni da ƙin son ganin Sadam yana fushi da ni, a raunane na ce"Ni fa ban ce ban yarda ba, amma kamar wata nawa za mu yi planing ɗin?"

Ya ce"Shekara É—aya ma ya isa, indai kika bi umarnina Sayyada za ki ji daÉ—in zama da ni wallahi, na faÉ—a miki babu wata mace a waje da za ta sake ba ni sha'awa ballantana ma har na aure ta, saboda ni ma ina sane samun irinki sai an tona".

Ya ce"Kin amince?"

Na ce"Na amince, ina sonka mijina, so ne ya sa na aure ka, kuma zan yi ta maka biyayya a kodayaushe, fatana dai ka yi mini adalci a zamanmu, don Allah kar ka butulce mini, kar ka kawo wata cikin rayuwarmu ta rage mana farinciki, ba zan iya raba ka da kowace mace ba, kishi ne zai saka zuciyata ta yi bindiga".

Ya ce"Na yi miki alƙawarin hakan ba za ta faru ba My Baby".

Ya kashe ni da daɗin baki sosai har na daina fargaba na amince har zuciyata, washegari kuwa ya ɗauke ni muka je wani private hospital, amma na yi mamakin ƙaryar da ya yi musu, ya ce matarsa ce ni, haihuwata uku duk CS ake yi min ana ciro yaran babu rai, shi ne muke buƙatar na yi planing na samu hutu kafin samun wani cikin, kuma implant yake so a saka min, saboda an yi min allura ta saka ni zubar jini, ƙwaya kuma ba na jurar sha mantawa nake yi, haka na yarda aka saka min tsinke na shekara biyar, da zummar idan ya yi shekara ɗaya za a cire shi, Sadam ya dinga lallaɓa ni, a cikin kwana ukun da aka ce kar na yi aiki da hannun komai shi yake yi, har wanka yi min yake, sannan bai kusance ni ba, ya ce sai na gyara jikina.

Anisa na tambaya inda ake siyan maganin mata, ta haÉ—a ni da wata mata ta ce kayanta suna da kyau sosai, na yi mata magana na ce ni bazawara ce zan yi aure ta yi min haÉ—i mai kyau, ta ce na kawo dubu É—ari za ta haÉ—a min komai har maganin sanyi ingantattu, na turawa Sadam account numberta, nan take ya saka mata kuÉ—in, a ranar kuma aka aiko min da kayan, na hau amfani da su ka'in da na'in.

Kafin na yi rabin kayan ni kaina na ji canji a jikina sosai, ranar kuwa da ya dawo min shi ma ya faɗa ya ce sai yanzu ya san ni amarya ce, wannan gyaran da na yi ma ya ƙarawa zamanmu amarshi, daga nan muka sake sakin jiki da juna, muka cigaba da shimfiɗa rayuwar aurenmu cike da soyayya.

Ƙalubale ɗaya shi ne ba ni da wata alaƙa da danginsa, sau ɗaya ya taɓa ɗaukata muka je gidansu, ai kuwa sai da na yi nadama, saboda yadda Momy ta yayyanka min maganganu ta ce kar ta sake ganin ƙafata a gidanta, ba ta sona, ba ta son aurenmu, ba ta alfahari da kasancewata matar ɗanta, kuma ba za ta taɓa yi min kallon suruka ba, na ma daina sakawa a raina ina da suruka indai ita ce, ina hawaye muka bar gidan, Sadam yana ta kwantar min da hankali, tun da kuma ban sake zuwa gida ta ba shikenan babu wani abu da take yi mini da nufin ƙuntatawa, kowa sabgarsa kawai yake yi, shi dai Sadam kullum sai ya je gidan, ina zuwa gidanmu, ina samun tarba daga wajen Mama, Baba ne dai sai dai kawai ya amsa gaisuwata fuska babu walwala, ban sake fira da Baba ba tun daga ranar da ya san na ɓarar da mutuncina.

Haka rayuwar ta yi ta miƙawa, ko na ji kewar samun ɗa ko 'ya sai Sadam ya wanke min wannan tunanin, da soyayyarsa me tsayawa a zuciya, mun yi zaman lafiya sosai, har na tsayin shekara biyu, duk lokacin da na yi masa maganar cire tsinke sai ya ce mu ɗan ƙara lokaci, muna shiga shekara ta uku mahaifiyarsa ta fara saka mana ido da tambayar ƙalau nake kuwa? Me yasa ban haihu ba har yanzu, sai dai ya ce mata Allah ne bai kawo ba, ni mamaki ma ta dinga ba ni, tun da a ganina tun da ba ta sona ma ai ba za ta so ɗanta ya haihu da ni ba, a hankali ta fara matsawa da zancen rashin haihuwata, na ce masa to a cire mana kawai na samu cikin nan, firr ya ƙi, sai ya zamana ma indai ina so mu yi faɗa to na yi masa batun a ajiye planing ɗin nan, yanzu zai birkice min na kasa gano kansa, shi yasa na rabu da shi don na ga gudun ruwansa, ai kuwa ƙarshe na gani.

A hankali na lura ya fara bawa wayarsa muhimmanci, ko fira muke yi hankalinsa na kan waya, sotari sai na yi bacci na barsa yana danna waya, ko tsakar dare na farka na same shi a falo da waya, da na so yin ƙorafi sai ya taka min burki da faɗin ban isa da na tsara masa rayuwarsa ba, shi ba lusarin namiji ba ne, na ja baki na yi shiru, sau ɗaya na taɓa ɗaukar wayarsa na duba, ai kuwa na ga yadda yake lalata da mata a waya, abun har ya ƙazanta, a ranar saura kaɗan kaina ya fashe, wani ɗan ƙaramin yaƙi aka yi a gidan, don birkice masa na yi na dinga hauka da ihu, shi kuma tun yana kare kansa har ya fara cewa ya yi ɗin na ɗauki mataki, nan fa zagi da gore-gore ya ɓarke a tsakaninmu, yana jifana da kalmar mara tarbiyya ni ma ina faɗa masa shi ne mara tarbiyya, ban taɓa ɗaga masa murya ba sai a ranar, don haka ya faffala min mari, wanda hakan bai kashe bakina ba, tun daga ranar kuma bakina ya buɗe, idan ya faɗa min baƙa ni ma sai na mayar masa, tun da na lura shi bai san halakci ba, na yi zaton irin sadaukarwar da na yi masa tun kafin aurenmu zai saka ya yi mini kara idan halin nasu na maza ya motsa, sai ya nuna min sabo da kaza ba ya hana yankata.

LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 700, KAFIN NA GAMA FREE PAGES MAI SO ZAI SAKA 500, WANNAN DISCOUNT ƊIN NA 'YAN KWANAKI ƘALILAN NE, DON FREE PAGES SUN KUSA ƘAREWA.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

08028966015
[29/09, 6:07 pm] Sadiya Abdulrazak: Ban tashi sanin na yi ganganci ba, sai da na ga da gaske Sadam yanzu ba ya ta ni, kuma aurensa zai yi, duk yadda nake yi masa bambamin sai na cire tsinken jikina ya ƙi, a ganina wannan ai mugunta ce, kenan ni ya mayar matar ado, zai auro wacce za ta dinga haihuwa, shi yasa ƙarshe na ɗauki matakin da na ɗauka.

A sanyaye ya shigo É—akin, na sauke idona a kan shi, sai hawaye suka fara zubo min, ya ce"Ki fito ga likitan nan ya zo zai ga hannun".

Ya juya ya fita, na tashi, na É—auki mayafi na yafa na fita, bayan ya gama dubawa ya yi mini faÉ—an na daina yawan motsa hannun, bayan ya tafi na tashi zan koma É—akin, Sadam ya ce"Sayyada, ki dawo ki zauna mana, ba fita zan yi ba, zan É—an É—auki hutun aikin saboda na kula da hannun naki".

Na ce"Ba na buƙatar kulawarka, ka je ka kula da wanda suka damu da kai".

Na wuce ɗakin, ya biyo ni, na hau gado na kwanta, shi ma ya hau gadon, ya kamo hannuna me lafiyar yana matsawa ya ce"Jikinki akwai ƙwarin da za ki iya karɓa ta? Ina buƙatarki".

Takaici ya sake kama ni, na ce"A'a, sai dai ka yi min fyaÉ—e".

Ya yi murmushi ya ce"Ai babu fyaÉ—e tsakanin mata da miji".

Na yi shiru don magana da shi ma na so nake ba, ballantana na tsaya na shi hujjojin da zai tabbatar akwai fyaÉ—en.

Na yi ƙoƙarin ƙwace hannuna ya riƙe ni tamau ya ce"Tashi ki sha maganinki".

Ya fita ya É—akko maganin da ruwa, yana cewa"Na haÉ—o miki shayi?"

Na ce"Na sha a asibiti".

Ya ɓallo maganin ya ba ni na sha, sannan na koma na kwanta, ya sanyaya murya ya ce"Kin ga Sayyada wannan zaman namu ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba, ba na son rashin kunya da neman fitina, ke kuwa yanzu shi kika saka a gaba".

Na ce"Sadam ni fa indai ba fasa auren nan ka yi ba wallahi ba wani abu da za ka faÉ—a min na saurare ka".

Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce"To shikenan Sayyada, zan saka a ɗaga auren zuwa wata uku, indai kika samu ciki a cikin wata biyu na yi miki alƙawarin zan fasa auren".

Na ce"Da gaske".

Ya ce"Na rantse miki zan fasa indai kin samu ciki nan da wata biyu zan fasa auren nan".

Sai na ji hankalina ya fara kwanciya, na ce"In sha Allah zan samu, Allah Ya ba mu mai albarka".

Ya ce"Amin, amma kin san samun ciki ba zai yiwu kina guduna ba ko?"

Na ce"Na daina, dama ai don ina takaicin za ka yi auren ne shiyasa".

Ya ce"Fine! Yanzu na matso kenan?"

Na ce"Haba don Allah, ba ka ga halin da nake ciki ba ne? Ina laifin ma a bari zuwa sanda ciwon nan zai warke?"

Ya ce"Shikenan, Allah Ya ba ki lafiya".
Chapter 12 · 0% Book details