← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 89

Sashe 18

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka ƙaraso suna tambayata wace ce ni kuma me ya fito da ni titi da daddare? Na ce musu mijina ba ya gari, kuma ni kaɗai ce a gidan na ji ina ciwon mara shiyasa na fito, suka tambaye ni ina ne gidan nawa na kwatanta musu a tsorace, suka tambayi lambar mijin, sai na saka tsohuwar lambata da na daɗe da canzawa, don haka da suka kira ba ta shiga ba, da na ga dai za su tsananta bincike na fasa musu kuka, na ce su kai ni gidan iyayena ba asibiti ba, don kuwa can na dosa.

Ɗaya daga cikinsu ya ce"Asibiti kika fi buƙata, na ga kina zubar da jini".

Sai a lokacin na kalli bayana, na ga yadda rigata ta ɓaci, gabana ya faɗi, amma duk a zatona tashin hankalin da na shiga ne ya matso da al'adata ta zo kafin lokacinta, sai dai ciwon marar ya tsananta, ko zan yi al'ada ba na irin ciwon nan mai tsanani, na ce"Ni dai mu je gidan namu, daga can ma je asibitin".

Wani cikinsu ne ya je ya ɗakko adaidaitasahu muka shiga, ina yi musu kwartance har muka ƙarasa gidan, hankalina a tashe sai karkarwa nake, ina tunanin ya mai gadi ya ƙare da Sadam? Tun da ba lallai ya iya tuƙin mota ba, kar fa ya mutu, idan ya mutu ta tabbata na yi kisan kai kenan.

Ƙwanƙwasa ƙofar gidanmu suka shiga yi, an ɗan daɗe ana bugun kafin Baba ya fito bai buɗe ba ya tambaya wane ne, cikin kuka na ce"Baba ni ce, Sayyada ce".

Baba ya ce"Sayyada? Ke wane irin kunnen ƙashi ne da ke wai? Sau nawa zan faɗa miki na tsame ki daga cikin 'ya'yana? Wallahi Sayyada ki kiyayi ranar da zan sheme ki!".

Na koma da baya na sakin sabon kuka, ɗaya daga cikinsu ya ce"Baba ya kamata ka buɗe, mu ma'aikata ne, mun tsince ta ne a titi, ko ma mene ne a tsakaninku bai kamata ka ƙi fitowa, ya kamata ka saurare mu".

Baba bai buÉ—e ba ya ce"Wannan yarinyar a da ne take 'yata, amma yanzu ba 'yata ba ce, ko mene ne ya same ta Kar a sake nema na".

Na fashe da kuka na ce"Don Allah Baba ka yi haƙuri, kuma ma Sadam ɗin ya sake ni, ina zan je da ya wuce nan ɗin?"

Wallahi shiru ba a ƙara jin motsin Baba ba, da alama ya koma ya kwanta. Suka kalle ni duka da neman ƙarin bayani, na ce"Don Allah kar ku ce komai, ku rabu da ni a nan ɗin, kawai zan kwana a nan, gobe sai na sake roƙonsa".

Fir! Suka ƙi, suka ce ba za su bar ni cikin haɗari ba, ƙarshe sai na ce mu je gidan yayansa wato baban su Anisa, duk da ban manta ba Baba ya ce idan ba sake zuwa gidan wani ɗan'uwansa bai yafe min ba, amma ba ni da wani zaɓi wanda ya wuce na je can ɗin.

Shi ma dai bai buɗe ba sai da na yi bayanin ni ce, ya buɗe suka yi masa ƙarin bayani, cikin kuka na ce"Baba don Allah ka taimake ni ka ba ni wajen zama, ban san inda za ni".

Baba ya fara salati ya ce"Sayyada, sai yaushe wannan abubuwan za su ƙare ne?"

Na kasa cewa komai, suka yi masa bayanin asibiti ya kamata a fara kai ni, da maman Anisa muka tafi asibitin, kafin mu ƙarasa ma har mai afkuwa ta afku, domin kuwa muna zuwa asibitin aka tabbatar mana da ɓarin ciki na yi, gabana ya faɗi da ƙarfi, har hawa da saukar numfashina ya canza, na ce"Da gaske ciki ne da ni? Ina da ciki? Don likita ki ce min bai zube ba".

Ta ce"Ki yi haƙuri, Allah zai ba ki wani in sha Allah, da alama ƙarami ne, shi yasa ba a sha wuya wajen fitar ta shi ba, ki lissafa ki gani yaushe rabonki da al'ada".

Na yi tsam ina hawaye ina tunani, a lissafina sati biyar kenan ban yi al'ada ba, kuma ina zargin a wannan fyaɗen da Saddam ya yi min ya kwashe ni ya zubar a falo na samu cikin nan, na runtse ido ina jin kamar kaina zai yi bindiga, wata nadama ta rufto mini, wallahi inda na san ina da ciki da na bi komai a sannu, idan ban manta ba yau Sadam da ya zo ce mini ya yi matarsa tana period ba zai iya jurewa ba, kenan da burina zai cika zan riga ta haihuwa ma, ashe na yi gajen haƙuri,, tsakani na da Allah har da zafin rashin haihuwa da kuma tunanin wata za ta riga ni haihuwa ya sa na aikata wannan abun, da na san ina da ciki da na rabu da Sadam ya je can ya ƙarata da matarsa, yanzu ma ko a wane hali yake?

SADAM

Azabar da yake ji a ƙafarsa bai sa mamakin Sayyada kashe shi ba, bai taɓa zaton ƙiyayyar da take yi masa ta kai haka ba, tun da ta iya saka wuƙa ta yanka kanta ya san don ta caka masa a cinya ba komai ba ne, amma dalilin da ya sa ta caka masa ɗin ne ya ba shi mamaki, a wannan zamanin da mata suke neman mijin aure ido rufe? Me ta rasa mene ne ba ya yi mata?

Mai gadi ya shigo da sauri yana bin inda yake jiyo kukan shi, ya same shi cikin jini ya fara salati yana cewa"Yanzu ya za a yi? Bari na samo mai adaidaitasahu".

Sadam ya girgiza masa kai ya ce"Je ka bugawa maƙocinmu sai ya kai ni a mota, bari na kira shi".

Da ƙyar ya nemi lambarsa ya faɗa masa, ya kuwa fito da mota da sauri, suka saka shi a ciki suka tafi asibiti, suna ta tambayarsa abin da ya faru, ya ƙi cewa komai, da suka je asibiti ma aka tambaya sai ya ce dare ya yi masu ƙwacen waya suka tare shi a hanya, shi dai mai gadi bai yarda ba, tun da yana kyautata zaton ba haka aka yi ba, aka shiga ba shi taimakon gaggawa.

Allah dai ya taimaka wuƙar ba ta tsinka wata jijiyar ba, don haka matsalar ba mai yawa ba ce, duk yadda Sadam ya so ya ɓoye Sayyada ce ta yi masa wannan abun sai da aka gane ita ce, don da Abbansa ya ritsa mai gadi ya sanar masa lafiya lau ya shiga gidan, kuma sannan Sayyada ce ta zo ta faɗa masa halin da ake ciki, kafin nan kuma dama ta ce ya buɗe mata ta fita ta ƙi, don haka ita yake zargi, tun da ba ta jira aka kai shi asibiti ba ma ta gudu daga gidan.

Shi Sadam bai san me ake ciki ba, sai ji ya yi Momynsa ta zo tana faÉ—a tana cewa sai ta É—aure Sayyada har danginta, gabansa ya faÉ—i ya ce"Momy mene ne ya faru?"

Ta daka masa harara ta ce"Au tambaya ma kake yi? Ko nufinka yara ka mayar da mu da za ka ce masu ƙwacen waya sun tare ka mu ƙu yin bincike? Yanzu dama Saddam da 'yar daba kake zaune? A ce yarinya ƙarama kuma mace har ta san ta cakawa mutum wuƙa? Wallahi kashe ka ma ta so yi, don haka dole sai an hukunta su, ba don Babanku ya hana ni zuwa ba ma da da ni za a tafi gidan nasu".

Sadam hankalinsa ya tashi, ya ji sam ba ya so a taɓa Sayyada, ya ce"Momy don Allah kar ku yi wani yunƙuri, wallahi laifina ne, sai da ta ce na sake ta na ƙi, kuma dama tana da matsalar aljanu, na tabbata su ne suka tashi".

Ta ce"Au! Lallai ka yi nisa, anya wannan yarinyar da iyayenta ba su asirceka ba kuwa? Anya kana cikin hayyacinka Saddam? Mace ta yi yunƙurin kashe ka ka dinga kare ta? Ai kuwa idan wannan so ne, Allah wadaran soyayya wallahi".

Tana haki ta ce"Yanzu an tafi gidansu da hukuma, sai ka tashi ka je ka dakatar da su tun da rayuwarka ce idan an taɓa ka za ta mutu".

Ta fita ta bar shi a É—akin, ya ji sam zuciyarsa babu daÉ—i, tun da ya sake ta a ganinsa ya kamata ko ma me ta yi masa su rabu da ita kawai.

Ya É—auki wayarsa ya kira layin babansa, a raunane ya ce"Abba, da gaske an tafi za a kama Sayyada"

Abba ya ce"E hakane".

Sadam ya ce"Don Allah Abba kar a kama ta, ai ni ta yi wa, kuma na yafe mata, ku bar ta ta ji da sabuwar rayuwar da za ta faÉ—a".

Abba ya ce"Ba zai yiwu ba, wannan yunƙurin kisan kai ne ta yi, kuma hukuma ta riga ta shiga maganar don haka yanzu komai yana hannunsu, sannan ina ba ka umarnin ka saki yarinyar nan, domin idan ba ka san ciwon kanka ba ni na san ciwonka, ba zai yiwu ka zauna da wacce take farautar rayuwarka ba".

A sanyaye ya ce"Ai na sake ta tun a jiyan, amma don Allah Abba a kashe case É—in, wallahi ba ta da me tsaya mata, ni na yafe mata".

Abba ya ce"Sadam kenan, wannan ya nuna har yanzu kana sonta, ƙila ma ba a son ranka ka sake ta ba, to shikenan ta je dan kanta, amma kamar yadda na faɗa maka case ɗin yanzu yana hannun hukuma, idan ka samu lafiya sai ka faɗa musu ka yafe".

Ya ce"To na gode Abba, ko zan samu lambar wanda case É—in ke hannunsa?"

Ya ce"A'a ba za ka samu ba, tana can a kulle, kuma ban amince maka ka sa a yi belinta ba, ko ka yi magana da wani É—an sanda, har sai ka samu lafiya an sallame ka daga asibiti".

A sanyaye ya ce"To".
Chapter 18 · 0% Book details