← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 89

Sashe 73

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka yi sallama cikin aminci, Ustaz ya zarce gidan Umma, cike da farinciki ya zayyana mata yadda suka yi da Rakiya, cewa ta yi ba ta yarda ba, sai da ta je har gidan nasu Rakiya ta sake jaddadawa ba za ta iya auren me mata ba, sannan Umma ta yarda, haka aka haƙura ba don ranta ya so ba.

Da ranar ta zo aka sake ɗaura auren Ustaz da Rauda a karo na biyu, tsirarun 'yan'uwa suka kai ta ɗakinta, Ustaz yana cike da farinciki, ga matarsa mai yarda da shi ga kuma ɗansa a kusa da shi, ai kuwa ranar an ci uwar sabada, don sosai suka nunawa kewar junansu, musamman ma shi Ustaz, tun da Rauda ta bar gidan Ustaz sai yai ta ji wata nutsuwa a zuciya da gangar jikinta, yanzu ta ga ingarman miji, da ta je ta auri lagwani da sunan namiji ne ashe, a ranta ta yanke duk tsanani ba za ta ƙara yin sake da auren Ustaz ba, kishiyar ta zo su buga sai dai ta bar mata mijinta,domin yanzu ta san muhimmancin shi, suka fara zamansu na lafiya, kuma Alhamdulillah Ustaz ya rage mammaƙon nashi, tun da ya zo ya ce mata likita ya ce babu damuwa zai iya cin nama da kayan shayi amma baya-baya, ya ƙara da faɗin ya ce ita ma da take da lafiya a faɗa mata ta guji cin nama sau uku a sati.

SAYYADA

Ranar da ya dawo É—akina, tun da safen kafin ya fita ya tura Abiy É—akinsa ya haÉ—a shi da kayan wasa da kayan ciye-ciye, ya ja hannuna ya nufi É—akinsa da ni, na bi shi babu musu ina gani abun mamaki, ya rufe É—akin da mukulli, na ce"Bawan Allah lafiya dai ko?"

Ya ce"Ina fa lafiya? Muna can muna tunanin ya za ki yi da kewarmu har ta kwana biyu? Shi yasa domin gujewa É—aukar alhaki muka ce bari mu fara da ba ki hakkinki tun yanzu".

Ya yi maganar yana rungume ni, na yi ƙoƙarin janyewa bai ba ni dama ba, na ce"Wallahi ban yi kewarka ba, sai dai kai ne kewar ta dame ka, kuma kai da matarka take sonka take yi maka komai mene ne abun kewata?"

Ya É—an haÉ—e rai ya ce"Wato dai Sayyada ba za ki kiyayemu ba ko? Sai yaushe za ki daina danganta ni da kai?"

Na ce"Sai ranar da na fara ganin mutum dama da É—aya a tare da kai, yanzu tun da kai kaÉ—ai ne ba zan fasa ba gaskiya".

Ya ce"To daga ranar da kika cika sati É—aya a gidan nan indai kika sake yi mana magana babu girmamawa to ba za mu saurare ki ba, ki É—auka kamar kin yi magana da bango ne, babu wannan maganar a lissafi".

Na yi shiru ban ce komai ba, ya ƙarasa da ni gadon yana cewa"Ki cire girman kai ki dinga bayyana kewarki yarinya, don mu dai muna da matar da za ta faranta mana, ke kuwa ba ki da ikon samun kowa sai mu kaɗai".

Na yi ƙoƙarin ƙwacewa ya riƙe ni gam yana cewa"Sai fa na ba ki hakkinki, don ni adalin miji ne a gareki".

Na ce"Na ji ba ni da kowa, amma tun da kai kana da wata don Allah ka daina zuwa wajena, ni na yafe maka hakkin nawa".

Ya ce"Yau ga kishi a inda ake iƙirarin babu soyayya, Sayyada anya kuwa?"

Daga nan bai sake ba ni damar cewa komai ba, ya shiga yin abin da ya kawo shi, yau kam da alama ya damu da wannan kwanciyar da nake yi masa, ya dinga kama hannuna yana yawo da shi a jikinsa, koya min yake wai ga yadda zan dinga yi na ji daɗi, shi saboda tsabar izza nuna min yake ba fa shi zai ji daɗin ba idan na taɓa shi, ni ce zan ji, ni kuwa na ƙi, amma daga baya sai na tsinci kaina da jin tausayin shi, na fara tunanin shin mene ne laifin shi? Laifin tsohon mijina ne ba nashi ba, na ce ba na son shi, kuma da gaske ba na jin zan so shi ɗin, amma ai na yiwa iyayena lƙawarin zan yi masa biyayya, yanzu ina jin biyayyar? Na yi kaina tambayar, wata zuciyar ta ce ina yi daidai gwargwado, matarsa ta riga ta sangarta shi, ba zan iya wannan rayuwar ba kamar a gidan sarauta, kuma idan ma zan yi ɗin sai dai na fito da salona na da ban ba irin nata ba.

Da yamma da ya dawo sai ga shi ya shigo tare da Hajiya Halima, na yi masa sannu da zuwa ita ma na gaishe ta, ta amsa da fara'arta, na ƙarasa na miƙa mata hannu don karɓar jakar hannunta, ta ce"Bar shi ki huta zan kai masa ɗakin". Ta yi hanyar ɗakin

Na kalle shi babu walwala a fuskata na ce"Ka dakatar da ita zan yi tambaya".

Kafin ma ya yi magana ta dakata, ta juyo.

Na ce"Shin wannan ɗakin naka turaka ce ta duka gida da ni da ita namu ne mu biyu ko kuwa ita ma da naka ɗakin a ɓangarenta?"

Ya ce"Akwai namu É—akin mana, kuma da naki da nata kowanne turakarmu ce".

Na ce"To a ƙa'idata turakar mijina daga ni sai shi, saboda haka ban amince wata ta ga ko gadon da muke raya sunna ba, daga sanda matarka ta shiga kuwa ya tashi daga turaka ya koma general bedroom, kuma ni da shiga har abada, sai dai ka dinga biyo ni ɗakina ko kuma mu kwanta a falo".

Hajiya ta juyo da mamaki haɗe da kishi a fuskarta, amma tana ta ƙoƙarin ɓoyewa sai dai a wajen ni mace ba zan kasa ganewa ba ta ce"Au ashe har akwai wani sirri da ya danganci mai martaba wanda ban san shi ba?"

Na ce"Ba kodayaushe ba ne wanda ya riga ka kwana yake riga ka tashi, kar ki yi mamakin na san abin da ba ki sani ba a game da shi, mijinki ne ba mahaifi ko malaminki ne, wannan abin da kike yi yana kawo naƙasu a soyayyarku, kuma ni wannan kissar taki idan kina yi ne don ki ga ƙarshena ya kamata ki dakata haka, kome za ki yi ki tsaya a iya sashenki, kar ki sake zuwa sashena ban gayyace ki ba".

Mai martaba ya ce"Ya isa haka Sayyada, mu muka gayyace ta, kuma mun yi ne dama da niyyar a ƙarfafa zumunci, duk wacce take da girki za mu haɗu a ɗakinta tun daga iyanzu har zuwa lokacin da za mu kwanta bacci, sai mu raka wacce ba ta girki, a cikin wannan zaman za a samu tattaunawa da kuma shaƙuwa, tun da mun riga mun zama ɗaya, Sayyada ba na son fitina".

Na ce"Na ji ta zauna amma wallahi indai ta shiga É—akinka to sai dai mu koma raya sunna a falo".

Hajiya ta fara taku don zuwa É—akin nashi, ya ce"Hajiya, kawo jakar mu za mu kai da kanmu, tun da husuma ba ta da daÉ—i".

Ya karɓa ya shiga ɗakin, Hajiya ta zauna a kujera, ni kuma bisa shawarar zuciyata na bi bayansa, na rufe ƙofar na murza key.

Ya juyo ya kalle ni, ya ce"Sayyada me yasa kike da fitina ne?"

Na ce"Don Allah ba na son ganin matarka a É—akina, ka je ka sallame ta".

Ya ce"Duk kishin ne?"

Na ce"A kan me zan yi kishinka? Kawai saboda na san ba zuwan Allah ta yi ba, ba na so".

Ya ce"Gaskiya ba za mu iya korarta ba, don haka dole a bi dokarmu, yunwa nake ji me kika dafa?"

Na ce"Ban dafa komai ba, amma ban sani ba ko ni kaɗai zan iya ƙosar da kai ba tare da abinci ba?"

Ya ce"Me kike nufi?"

"Ina so ka ba ni haƙƙina ne". Na yi maganar a raina kuma haushin kaina nake ji, saboda na yi ne ba don ina buƙatar ba sai don na ƙuntatawa Hajiya Halima.

Ya yi murmushi ya ce"Da gaske wai?"

Na ce"Ƙwarai kuwa ranku ya daɗe mai martaba".

Ai kuwa ina rufe baki ya janyo ni ya rungume, ya ce"Sayyada da gaske ke ce".

Na ce"To me zan yi muku ku gane ni ce?"

Ya ce"To ai gani na yi lokaci É—aya kin canza ne".

Na ce"Ka yi haƙuri, zan canza halina ne daga yau in sha Allah"

Sai kuwa ya ɓarke da zance"Na gode sosai Sayyadata, ni fa dama ina sonki wallahi, kawai wannan rainin naki ne ba na so, shi yasa kika ga ina basar da ke, i love You, Please yau dai zan yi zama kamar rayayyiya ba gawa ba ko?"

Na yi murmushi na ce"Ran mai martaba ya daÉ—e kun manta kun daina saka jam'u a maganarku".

Ya ce"Ina sane, rabu da sarautar nan, ai a daidai wannan lokacin ke ce sarauniyar ke dai bisimillah Sayyadata".

Ai kuwa na zage na dinga faranta masa, yana yi min godiya kamar ba shi ba, da gayya na yi, na yi ne don na ƙuntatawa kishiya, amma wani abun mamaki, sai ga shi a ranar na gane Ustaz fa sumar da sha'awata ya yi ba kashe ta ya yi ba, domin kuwa ta farfaɗo a yau, muka samu gamsuwa sosai, kiran sallar magriba ne yasa muka katse, sai murmushin yake yi yana cewa"Ana yin sallar isha'i za mu ɗora kin ji?"

Na ce"To Mai martaba".

A tare muka yi wanka, don haka tare muka fita daga É—akin, na É—aura zanina sai towel da na yafa shi daga kaina zuwa lafaÉ—a, shi ma yana sanye da jallabiya kana ganin shi za ka gane ya yi wanka, na ji daÉ—in ganin Hajiya Halima ba ta yi zuciya ta tafi ba, Ya ce"A, Gimbiya har yanzu kina nan ashe".

Ta haɗiye malolon da ya tokare mata maƙoshi ta ce"Ina nan mai martaba, sannunku da fitowa".

Ya ce"Yawwa, bari mu je masallaci mu dawo, idan zaman ya ishe ki za ki iya komawa sashenki kawai ma, tun da ai an gaisa".

Ta ce"A'a zan zauna".

Ni kuwa a raina na ce ashe ba ki gama ganin takaici ba kenan.
Chapter 73 · 0% Book details