Sashe 34
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaina ya kulle na shiga tunanin wanda yake son wasa da hankalina, na kira lambar na ji layin sam ba ya tafiya ma, na yi tsuru-tsuru, wata zuciyar tana ce min tun da ina cikin buƙatar kuɗi na ci kuɗin nan kawai Allah ne Ya ba ni, wata zuciyar kuma tana hana ni, ba ni da wata mafita, don haka na saka hijjabi na ɗauki ATM ɗina na fita, jikina babu ƙwari Sam nake yin komai, ga yunwa da ta addabe ni, ga mara da cikina sam babu daɗi, kafata sai ciwo take, kada ma cinyata ta ji labari, don na fara tunanin ƙasusuwan ƙugun Ustaz ko bayan mun rabu sai sun nakasa min cinyata.
Dubu ashirin na cira, na hau adaidaitasahun na tafi asibiti, ina tafe a harabar asibitin da ƙyar nake ɗaga ƙafata, ban yi aune ba jiri ya kwashe ni, na faɗi, na dai ji lokacin da na tafi luuuu zan kai ƙasa, sannan na ji salatin mutanen dake wajen, daga nan kuma ban sake jin komai ba.
(Saboda na mutuðŸ˜)
Prank ne kar ku tsire niðŸ¤
[14/10, 5:44 pm] Sadiya Abdulrazak: 21
Allah Ya taimaka akwai ma'aikatan asibitin a kusa, don haka ba a samu wanda ya sace wayarta ba, aka kwashe ta aka ba ta gado aka fara ba ta taimakon gaggawa, sannan aka ciro wayarta daga jaka, aka ɗora hannunta, fingerprint ya fita, ba a gane lambar mijinta ba, don da Malam ta yi saving, sai aka kira ta Baba, aka sanar masa asibitin da take, Baba duk ya ruɗe ga shi ba ya kusa ya je can ƙauyensu zai yi kwana biyu, da sauri ya kira Mama ya sanar da ita asibitin ya ce ta je ta ga jikin, sannan ya kira Ustaz. Ustaz yana kasuwa aiki yake amma hankalinsa yana can wajen Sayyada, tunanin wannan minus one ɗin da ya yi kawai yake yi, ji yake ya cuci kansa kamar ba zai iya jurewa ba, sai ga kiran Baba ya shigo, ya san Baban ba ya garin tun da ya faɗa masa zai yi tafiya, ya ɗaga ya gaishe shi, Baba bai ja gaisuwar ba ya ce"Malam Ashiru kana ina ne? Me yake damun Sayyada aka bar ta ta tafi asibiti ita kaɗai babu ɗan rakiya?"
Ustaz ya rikice ya ce"Subhanallah! Ita Assayyadar ce ta fita daga gidan ba tare da izinina ba? To a iya sanina dai na ba ta kuɗin siyan kayan miya, ƙila ta fita za ta siyo ne".
Baba ya ce"Duka fa ba wannan ba, ni hukumar asibiti ne suka kira ni, suna kyautata zaton Sayyada ganin likita ta je, shi ne ta faÉ—i a harabar asibitin kafin ta kai ga ganin likitan, Allah Ya taimaka ta fita da wayarta shi ne aka kira ni".
Ustaz ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ita kuwa Assayyada me ta je yi asibiti? Wallahi Baba ban san ba ta da lafiya ba, kuma ba ta ce min za ta je asibiti ba, kaico! Ni ban san me take nufi ba, ban san me ta É—auki lamarin aure ba, amma babu komai na yafe mata, sai dai Baba ku dinga tuna mata haÉ—uwarta da Allah, idan ni na yafe mata Allah fa?"
Baba da ransa ya fara ɓaci da wannan surutun nasa ya ce"Yanzu za ka je asibitin ne ko kuwa? Ni ma gani nan xan hau mota na taho".
Ya faɗa masa asibitin da take, ya kashe wayar, a ransa yana tunanin me yake damun Sayyada da ba ta sanarwa mijinta ba? Nan take ya gasgata lallai Sayyada ba zaman lafiya take yi da mijinta ba, tun da har za ta iya fita ba ta tambaye shi ba, sannan ban da baƙin hali da ɗaukar miji ba a bakin komai ba, a ce ba ka da lafiya ba za ka faɗawa wanda kuke kwana tare ku tashi tare ba? Nan take ransa ya ɓaci, duk da ya damu da rashin lafiyar nata.
Mama da ta ƙarasa asibitin ta ga halin da Sayyada take ciki ta dinga share hawaye, musamman bayan farfaɗowarta da ta faɗi cewar ɓarin ciki ta yi, ta ji tausayinta sosai, sannan ta ga ta sake rama a kan ranar da ta je gida, Mama ce take ta ɗawainiyar asibitin, da kuɗin da aka samu a jakar Sayyadar, a tunaninta ma mijinta ne ya ba ta, yanzu halin da ake ciki an ce ana so a ƙara mata jini ko leda ɗaya ne, don haka Mama ta sake kiran Baba, ya ɗaga yana tambaya ya mai jikin, ta ce"Da sauki za a ce, amma yanzu sun ce dole sai an ƙara mata jini ko leda ɗaya ne".
Ya ce"Subhanallah! Mijin nata ya ƙaraso?"
Ta ce"A'a, bai zo ba".
Suna gama waya sai ga Ustaz ya kira wayar Sayyada, Mama ta ɗauka ya ce mata ya ƙaraso ina zai yi? Ta faɗa masa ɓangaren da suke, sai ga shi ya taho yana ta zuba saurayi, tun a adaidaitasahu yake ta jera subhanallah, har ya ƙaraso inda Mama take, ya duƙa ya gaishe ta ta amsa, cike da jimami ya ce"Ya mai jikin namu kuma? Me ya same ta ne?"
Mama ta ce"Ai na zata ka san ta yi ɓarin ciki ko? To bayan ɓarin ne ta taho ganin likita shi ne jiri ya kwashe ta ta faɗi, tsakani da Allah bai kamata a ce ka bar ta da ɗanyen jiki ta taho asibiti ita kaɗai ba, idan ma ba ka da lokacin kai ta ai ya kamata ka sanar min, ni sai na kai ta, ko na turo wata ta raka ta".
Ya ce"Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wato Mama haƙiƙa na kula kamar Sayyada ba ta da lafiya kafin na fita, amma da na ga ba ta faɗa min ba ta jin daɗi ba, sai na yi zaton kawai kasala ce, bi ma'ana dai irin larurin nan na masu juna biyu, a halin yanzu ban san an rasa cikin ba sai yanzu da kike faɗa min, haƙiƙa sai bayan na fita komai ya afku, subhanallah!".
Mama sam ba ya burge ta, haushin shi take ji tun da ta san hariji ne mai cutar 'yarta, don haka ta ce"Yanzu dai tana ciki, kuka jini ake buƙata za a ƙara mata ko leda ɗaya ne".
Ya ce"Subhanallah, abun har ya kai haka?"
Mama ta ce"Zai iya fin haka ba, don wannan ramar da take yi ba ta lafiya ba ce, daga gani ba ta cin abinci mai gina jiki".
Ya ce"A yi haƙuri Mama, in sha Allahu za a fara siyo mata abubuwa masu gina jiki, akwai me zogale da kullum take zuwa kasuwarmu, in sha Allah zan daure na dinga siyo mata tana kwaɗawa, tun da a bisa bincike na masana kiwon lafiya an ce zogale ya fi kaza amfani a jikin ɗan'adam, yanzu ya jikin nata?"
Ta ce"Da sauƙi za a ce, duk abin da aka buƙata na siya da kuɗin da na gani a jakarta, yanzu jinin ne dai ban san yadda za a yi ba, ai sai dai a siya".
Ya ce"To ai dama ba a riga an siya ba, da sai na siya, tun da hakkina ne, bai kamata a É—auke min nauyina ba, amma tun da an riga an siya la ba'asa, na gode".
Mama ta ce"To ai ga siyan jini nan a gaba".
Ustaz ya sauke numfashi, shi fa fitar da kuɗin siyan jinin ne yake jinjinawa, shiyasa ma ya ga kawai gara a ɗibi nashi a saka mata, kuɗinsa ya huta, idan ya siya zogale na ɗari biyu maltina guda ɗaya ya san zai mayar da jininsa ai, don haka ya ce"Subhanallah! Mama da raina da lafiyata ai ba zai yiwu na zuba ido a ce wai a siya jinin da za a ƙarawa matata ba, nawa za a ɗiba a ƙara mata in sha Allah".
Mama ta kalli yadda yake a bushe sai tsayi kamar daren mutuwa, gani take jinin jikinsa bai kai ma leda É—aya ba, amma shi ne yake cewa a É—ibi na shi".
Kafin ta ba shi amsa likita ya ƙaraso inda suke, ya ce da Mama wai kun gama yanke zancen jinin kuwa? Yana da kyau a saka mata".
Mama ta ce"Ga mijinta nan, ya ce a É—ibi nashi".
Likitan ya yi masa kallon sama da ƙasa, ustaz ya jinjina kai ya ce"Na'am in sha Allah!"
Likita ya miƙa masa hannu suka yi musabaha, sannan ya ce"Amma Malam anya za a samu a jikinka kuwa?"
Ustaz ya yi murmushi ya ce"In sha Allah, ai ko ba za a samu yadda ake so ba, indai an samu ledar da za a sakawa ita Assayyadar to a ɗiba a saka mata, domin ni fa ba zan ɓoye muku ba, kishina ba zai bari a ce an ɗauki jinin wani ƙato an sakawa matata, ya dinga gudana a jikinta ba, don haka dole nawa za a ɗiba".
Likitan ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To babu damuwa, mu je lap sai a É—iba a gwada, idan zai yi ba matsala sai a É—iba É—in".
Ya ce"In sha Allahu zai yi, lafiya ƙalau ne".
Suka je aka gwada gabansa sai faɗuwa yake yi, aka ga zai yi daidai da na Sayyada, sai dai shi kansa jinin jikinsa ya yi ƙaranci, inda za a ƙara masa yana buƙata, don haka likitan ya ce"Malam sai dai fa ka yi haƙuri, level ɗin jininka bai kai wanda za ka iya ba wa wani gudunmawa ba, domin kai ma kana buƙata".
Ustaz kamar zai yi kuka ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kun dai rantse sai kun gurɓata jinin matata da na wani gardin da ban san ma wane ne ba, likita ka dubi girman Allah ka ɗibi jinin nan nawa, a saka wa matata halattaccen jinin mijinta, wallahi idan aka saka mata jinin da ba nawa ba zan iya haɗiyar zuciya na mutu don kishi".
Ya ce"Idan aka diba fa za a iya samun matsala".
Ya ce"Haba likita, kar fa ka manta fankam-fankam ba ta kilishi, ba wai don ka gan ni babu ƙiba bane zai tabbatar maka ni ba namijin duniya ba ne, wallahi ko zan mutu na yarda na sadaukar, ka ɗiba kawai".
Aka ja leda É—aya, aka bar shi kwance yana hutawa, aka je aka sakawa Sayyada.