← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 89

Sashe 57

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tsaya yana kallona, fuskar shi babu yabo babu fallasa, kallon ya kashe min jiki, irin wanda na yi kewa ne, sai na sunkuyar da kai hawaye ya fara sakko min, wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ina farinciki da zuwan shi amma ya zama dole na nuna ban yi ba saboda iyayena su yarda da ni.

Ya ce"Ki dakata da wannan pretending ɗin haka, kin san ina sonki, kin san ina tare da ke, sannan kina farinciki da zuwana yanzu ma, ban taɓa ganin ƙiyayyata a Idonki ba tun da na fara ganinki, ko a baya daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarki ce ta ƙi ni ba ke da zuciyarki ba".

Na ce"Na ji, ka tashi ka tafi, kar ka sake yi min irin wannan zuwan".

Ya ce"Dama barka na zo, na kuma ga yanayin jikin naki, kin sauka lafiya?"

Na ce"Lafiya lau".

Ya ce"Allah Ya raya shi bisa sunna, hmm da ciwo a ce kin sakarwa wani jiki har kin haihu da shi, kin haifa masa ɗa ba nawa ba, kuma kina sane idan mace ta haihu jikinta canzawa yake yi, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa na ƙi ki haihu a farko, kike ganin hakan kamar ƙiyayya ko mugunta, ga shi kuma yanzu zan biya sabon sadaki na aure ki a duk yadda jikin naki ya zama".

Na ce"Kana da raunin tunani ta wannan fannin kuwa, a tunaninka idan mace ba ta haihu ba shikenan jikinta ba zai taɓa canzawa ba?"

A bazata na ji Mama ta ƙwala min kira"Sayyada!" Gabana ya faɗi, sai yanzu na gane ma na yi wauta da na zauna ina sauraron shi, ya miƙo min ledar da ya ajiye a kusa da shi ya ce"Ga wannan ba yawa, zan yi miki transfer wani abu, sannan duk abin da kike buƙata ki tambaye ni, sai mun yi waya".

Ya fice daga É—akin bai jira amsata ba, ina jiyo shi yana cewa Mama"Sai da safe, Allah Ya raya".

Na yi zaton ma za ta dakatar da shi ta yi masa gargaɗi sai na ga saɓanin haka, ta shigo ɗakin ta rufe ni da faɗa kamar za ta dake ni, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta rantse sai na fito mata da wayar hannuna, na fara kuka na ce"Wallahi Mama ba ni da wata wayar bayan wacce kika karɓa, na rantse da Allah ba ni da wani connection da shi, ban san wanda ya faɗa masa na haihu ba, ban gayyace shi ba".

Mama ta yi hau bincike kayana, tana watso su ƙasa, ni kuma sai kukan baƙinciki nake yi, a ce mahaifiyata tana zargina? Na shafawa kaina baƙin fenti, ta gama bincikenta tsaf ba ta samu komai ba, ta juyo tana yi min mugun kallo ta ce"Sayyada!"

Na tsananta kuka na ce"Don Allah Mama ki yarda da ni".

Ta ce"Ta ya zan yarda da ke? Me yasa zan yarda ba kwa waya alhalin jiya kika haihu yau ya ji labari har ya zo barka?"

Na ce"Wallahi ba a wajena ya ji ba".

Ta ce"Ina fatan dai ba ki manta alƙawarina a kan alaƙarki da shi ba ko? Babu ke babu auren shi har abada".

Na kasa cewa komai, sai bugun zuciyata da ya canza, ta ce"Ki faÉ—a masa kar ya sake dawowa cikin gidan nan, idan kuma ya dawo laifinki ne, da ni kike zancen!".

Na ce"Amma Mama ban san ta inda zan faÉ—a masa ba wallahi".

Ta ce"Za ki sani ne idan ya sake dawowa".

Ta fita daga É—akin ta bar ni cikin zulumi, na rasa ya ma zan yi, haka na dinga fargabar kar ta faÉ—awa Baba, kuma na yi sa'a ba ta faÉ—a masa É—in ba, can wajen goma na dare na janyo ledar da ya bar ta, Mama ta ganta amma ba ta bi ta kanta ba, na buÉ—e, da waya a kwali na fara cin karo gabana ya faÉ—i, na yi saurin rufe ledar, sai da na je banÉ—aki na yi fitsari na gyara jikina sannan na dawo na yi shirin bacci na rufe É—akin na saka sakata, na buÉ—e ledar, na ciro wayar, na buÉ—e ta, na kunna, sai na ga da sim card a ciki, massage ya faÉ—o, na buÉ—e na ga an yi saving lambar da Mijina, "Idan kin kunna wayar ki kira ni".

Abin da yake cikin saƙon kenan, na sauke numfashi, na ajiye ta a gefe na fara ciro kayan ciki, leses ne masu kyau da tsada guda uku sai takalmi da jaka, da wani box ɗin sarƙa mai shegen kyau, sai kuma kayan jariri kala uku masu kyau, jikina duk ya yi sanyi, har zuciyata ba na son kowa sai Sadam, da shi nake hasasho rayuwata ta gaba, ga kuma ƙudurin iyayena, ina tsoron fushinsu, tun da na san namiji ba shi da tabbas, na ga illar barin iyaye na zaɓi namiji, ba na fatan na maimaita, na kashe wayar na ɓoye ta, na gyara kayan da Mama ta watso min na kwanta, abunka da jikin jego sai bacci ya kwashe ni Ni mai nauyi, sai da yaron ya motsa sannan na farka na tashi zaune na shayar da shi, na fara tunanin Saddam yana can yana jiran kirana, amma ban yi nisa da tunanin ba bacci ya kwashe ni.

Da safe Mama tana can tana kokawar dafa mana ruwan wanka na kunna wayar na kira shi, tun da ya zama dole na yi hakan saboda gudun kar ya dawo, ba ta daÉ—e tana ringing ba ya É—auka da sallama, na amsa na gaishe shi, ya ce"Shi ne jiya kika bar ni da tunaninki ko? Me yasa ba ki kira ni ba?"

Na ce"Sadam don girman kar ka sake zuwa gidanmu".

Ya ce"Me yasa?"

Na ce"Matsala za ka ja min a wajen iyayena, zargi suke ma ni ne na ce ka zo, don Allah kar ka sake zuwa".

Ya ce"To yanzu dai dama ba zan zo ba sai bayan suna idan an yi arba'in haka, amma daina zuwa gabaÉ—aya kin san ba zai yiwu ba".

Na ce"Zai yiwu".

Ya ce"Ok kina nufin gidan shi harijin za ki koma kenan?"

Na ce"Ba wanda zan aura, ai auren ba dole ba ne".

Ya ce"Dole ne a gare ki, musamman da kika auri hariji kika sakar masa jiki har da haihuwa, yanzu sai jarumi ne ma zai iya zama da ke, ni É—in ma zan gwada ne kawai".

Na ce"Sai anjima, kar ka sake zuwa don Allah".

Ya ce"Sayyada".

Na ce"Na'am".

Ya ce"Kina sona?"

Na ce"Ba wannan maganar ce a gabana baz ka san dai ko zan yi aure sai na yaye É—ana ko? Ban tsara yin zance da wani ina shayarwa ba, don haka kar ka sake zuwa, kuma batun soyayya a ajiye shi a gefe, kafin ka hasala iyayena, su raba mu har abada tun kafin lokacin da ya kamata a fara batun auren ya yi".

Ya sauke numfashi ya ce"Idan na fahimce ki dai kina sona, amma iyayenki ba sa sona kuma kina gudun fushinsu ko?"

Na ce"Ina sonka Sadam, amma a wannan karon ba zan saɓa umarnin iyayena ba, duk yadda suka tsara min haka zan yi".

Ya ce"Ko da ba su amince da aurenmu ba? Za ki zaɓi sake rayuwa da wanina a karo na biyu?"

Na ce"Ba ni ce zan zaɓa ba, ƙaddara ce za ta zaɓar min".

Ya ce"Shikanan, gara da kika faÉ—a min tun yanzu na janye jikina, na gode Sayyada ina yi miki fatan alkhairi".

Na ce"Ba fa haka nake nufi ba".

Ya ce"To faÉ—a min nufinki".

Na ce"Kawai dai na san dole za a samu matsala ta wajen iyayena shiyasa nake faÉ—a maka haka".

Ya ce"Tun da ba za ki iya fuskantar matsalar ba ki magance ta ai kin ga babu amfanin mu fara rayuwar da ba ta da ma'ana, tun da za mu ɓatawa juna lokaci ne kawai".

Na ce"Ka dai tsaya mu ga abin da hali zai yi, amma kar ka dinga zuwa don Allah".

Ya ce"Za mu dinga waya da chatting?"

Na ce"E".

Ya ce"Duk ranar da ban ji ki ba zan zo kin yarda?"

Na ce"Na yarda, amma kar ka dinga kira saboda tsaro, idan na samu space zan dinga taɓo ka".

Ya ce"Ok, I love you, you are mine".

Na ce"Love you too".

Na kashe wayar na ajiye, na lumshe ido ina tuna lokacin da nake gidan shi kafin al'amura su fara lalacewa. A haka Mama ta shigo ta same ni, ta É—auki É—an tana ce min"Ki je na kai miki ruwan ki shiga".

Na gama komai na shirya ina karyawa sai ga sallamar Ustaz, ina jin Mama tana ba shi izinin shigowa na fizgo mayafi na lulluɓe jikina, na ɓata rai sosai, na ji alamar dai ya shiga ɗakin Mama, ba jimawa kuma ya yi sallama a ɗakin da nake, na sake haɗe fuska, sannan na amsa, ya ce"Zan iya shigowa?"

Na ƙi amsawa.

Ya ɗan yi sakanni sannan ya shigo yana ƙara sallama, hannunsa riƙe da jaririn ya ce"Haba ya ke Assayyada ya ina neman kuma kin ƙu amsawa? Kin san yanzu ke ba matata ba ce, iddar ma da nake tunawa kina ciki na ji daɗi yanzu an ƙare ta, don haka dole na nemi izininki yayinda zan shigo inda kike, don gudun saɓawa shari'a, bi ma'ana kar na yi tozali da abin da bai halatta na gani ba".

'Hali yana nan' Na faÉ—a a zuciyata.

A fili kuwa na kau da kai na ce"Ina kwana".

Ya ce"Lafiya lau Assayyada, Alhamdulillah, ya ƙarfin jiki, ya kwanan Abiy? Bi ma'ana takwaran mahaifina".

Na ce"Ƙalau".

Ya ce"Ma sha Allah, dama na zo ne na gan shi ke ma na ga jikin naki".

Na ce"Ka tsaya a iya ɗan naka, don ni dai ba Ni da wata alaƙa da kai".

Ya ce"Hakane, amma ni na yi zaton zuwa yanzu kin huce za mu sasanta amma fa ba wai na damu ba ne, dama makomar wannan yaron nake dubawa".

Na ce"Kar ka saka ran za mu sasanta har abada, da ma can ban so ka ba, kuma ba zan taɓa sonka ba har abada".
Chapter 57 · 0% Book details