Sashe 70
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ya nufi ɗakin Abiy ya ɗauke shi ya yi masa wasa, ya bar ɗakin, na dinga tunanin ta yadda zan je wa wannan makirar matar da batun ta ara min mai aikinta, dai ga shi ma baƙin sun zo da wuri, don ƙarfe goma a nan ta yi musu, har na yi musu tayin karyawa suka ce sun karyawa su goma sha biyu ne, manyan mata da 'yan mata, suka faɗa min yara sai ranar Juma'a za su zo, tass suka yi min bayanin wannan wance ce, ga yadda suke da mijina wannan ma haka, kuma aka yi sa'a sun yi min, don haka na saki jiki da su muka dinga fira, sai dai na ji suna ta kushe Hajiya Halima, har ma suka tambaye ni yanayin zaman namu, na ce ƙalau muke zauna, suka dinga ba ni shawarar to na yi hankali da ita, kar na sake na sakar mata fuskar da za ta raina ni, a bakinsu nake jin mahaifarta ta lalace har ma an cire, don haka babu batun haihuwa, amma ta mallake shi tun tuni ta hana shi aure, sai yanzu da Allah ya yi, ni dai jinsu kawai nake ban faɗi wata magana mai zafi ba ko me sanyi wacce za a kai ni gaba, don mutum mai surutu ba abokin sirri ba ne, kuma ba a cika yin gulma da shi ba.
Da lokacin ɗora girki ya yi ina shiga kitchen 'yan mata biyu suka biyo ni, ƙannesa ne uwa ɗaya uba ɗaya, suka karɓe aikin suna taya ni, ɗaya mai suna Mansura ta yi wa ɗayar raɗa a kunne, sai suka fara dariya, Zuhra ta ce min "Anti akwai CCTV camera a kitchen ɗin nan kuwa?"
Na ce"Gaskiya ko akwai ban sani ba".
Mansura ta ce"Wallahi ko akwai dai na faÉ—a".
Ta ce"Wai kika yi da sarautar Yaya? Kin san fa sarki ne shi a gidan nan nashi, ji yake kamar wata shahararriyar masarauta ce, ko ba ki ji idan zai yi magana yana jam'u ba?"
A raina na ce Alhamdulillah, tun da an sosa min inda yake yi min ƙaiƙayi, na ce"Ni dama ina so na tambaye ku, wai ku jinin sarauta ne?"
Suka fara dariya duka ce"Wallahi babu É—aya, matar tashi ce da shegen iyayi tun farkon auren take ce masa sarki, ita ta É—ora shi a wannan tsarin ta ce shi sarki ne, girmamawa kamar ta tsugunna masa, yanzu ai ta rage sosai, shi ne fa shi kuma ya hau kai ya zauna, yake ta famkama, ba ki ga har kayan sarauta yake sakawa ba? To da har doki ma zai siya, Mama ce ta hana shi".
Mamaki ya kama ni na ce"Allah mai iko, to ita matar tashi jinin sarauta ce kenan?"
Suka ce "Wallahi babu ɗaya, ko akwai sarauta to ta nesa ce, kin san yar Nijar ce ya je ya kwaso ta, ai ni na ji daɗi da ya ƙara auren nan, yanzu za mu dinga zuwa gidan nan a daɗin rai".
Haka dai suka dinga surutu, muna yin girki, cikin ƙanƙanin lokaci muka gama, aka yi drink aka saka a firji, kafin a yi sallah, kuma na ji daɗin yadda ba su nuna rashin jin daɗin ganin ɗana ba, duk da ban sani ba ko a gaban idona ne suka nuna haka, mun baje muna cin abinci sai ga Hajiya Halima ta aiko mai taya ta aiki da abinci kula biyu, babbar cikinsu ta ce a mayar ba za su ci ba, wasu kuma suka ce a ci tun da ai kuɗin ɗan'uwansu ba na ta ba, suka dinga sa'insa suna zaginta da yi mata gore-gore, ƙarshe dai aka ƙi karɓa aka koma da shi.
Haka muka wuni tare da su, sai yamma lis suka tafi, don har tuwon dare na Sarki su suka yi min, ba ni da kuɗi, don sadakina har Baba zai ba ni na ce ya ajiye min, ga shi account ɗina na babu komai, na kwashe duka a hidimar bikin, sai ƙanwata na kira na roƙi ta ara min dubu ashirin, na yi sa'a aka samu, na aiki yarinya ɗaya ta ciro min kuɗin, da za su tafina tarkato musu kayan kwalliyata da kuma kuɗin na ba su, ai kuwa sai shi min albarka suke, duk mun yi musayar lambar waya da su.
Zuwa su ya yi min daÉ—i sosai, na gyara gidan, na yi wanka na yi sallar magriba, dab da kiran sallar isha'i ya dawo gidan, ina kallon fuskar shi na gane babu walwala a tare da shi, na ce"Sannu da zuwa".
Bai amsa na sai É—aukar Abiy da ya yi yana É—aga shi sama, ya zauna yana ba shi ledar tsarabar da ya yi masa, na tashi don kawo masa ruwa ya ce"Ke koma ki zauna".
Na tsaya ni ban tafi ba ni ban zauna ba, don gaskiya idan ya cigaba da nuna min ikon nan wataran zai sha mamaki.
Ya ce"Ko ba za ki zauna ba?"
Na zauna ina haÉ—e gira, ya ce"Ba jiya muka yi muku magana a kan Hajiya ba?"
Na ce"To wani abun ta ce maka na sake yi?"
Ya ce"Ai kin fi kowa sani, mene ne huruminki a sabgar danginmu da har za ta kawo musu abinci ki rantse ba za a karɓa ba?"
Mamaki ya kama ni, don wallahi lokacin da ake maganar ko saka baki ban yi ba. Na ce"Ban ce komai a maganar ba, su ne suka yanke wannan hukuncin".
Ya ce"Hajiya za ta yi miki ƙarya ne, ko kuwa mu ne muke ƙaryar?"
Na ce"Allah shi yana kallona".
Ya ce"Sayyada! Sayyada!"
Na ce"Na'am".
Ya ce"Tashi ki wuce mu je ki ba ta haƙuri, kuma wannan shi ne karo na biyu da kika mata laifi, idan kika yi na uku za mu ba ta dama ta ɗauki mataki da kanta".
Na ce"Na rantse da Allah ban yi mata komai ba, ko jiyan ma rashin sanin halinta ne ya sa na yarda ka saka ni a gaba muka je, amma gaskiya ba zai yiwu na dinga bawa wata zindiƙiya mara tsoron Allah haƙuri a kan laifin da ba nawa ba".
Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Sayyada, a lallai za a samu matsala babba da ke, dole sai an saita ki, kin wuce mun tafi ko sai na ba ki mamaki".
Na ce"Ni fa babu wani mamakin gidan aure da ban gani ba".
Ya ce"Tashi mu je ki ba ta haƙuri".
Da na tashi sai na yi ɗakina na yi kwanciyata, ina jira na ji me zai biyo baya, don na ƙudure ko dukana zai yi ba zan ba ta haƙuri ba.
08028966015
[11/11, 7:13 pm] Sadiya Abdulrazak: 42
Jim kaɗan ya biyo ni ɗakin da sallama kamar abun arziƙi, na amsa ina ɓata rai, ya ce"Ke Sayyada ba ma son raini fa, ki tashi ku je ki ba ta haƙuri".
Na ce"Ni fa ban yi mata komai ba, 'yan'uwanka ne suka yi mata, kuma ka kira su ka tambaye su".
Ya jinjina kai ya ce"To mun ji ba ki yi komai ba, amma duk da hakan muna ba ki umarnin da ki tashi mu je ki ba ta haƙuri, ai mun isa ko?"
Na ce"Ka isa, inda kai zan bawa haƙuri na zan ji ƙyashi ba, ko ban yi maka laifi ba, amma ita dai wallahi ba za ta juya ni ba, tun da ba zamanta nake yi ba, ni ka faɗa mata ma tun da dai abun babu mutunci kawai babu ni babu ita, ta daina zuwa ɓangarena ta daina kula baƙina, duk da 'yan'uwanka ne to ta bari sai sun shiga ɗakinta ta ba su abinci, ka ga ban isa na ce a ce mata ba za su ci ba, sannan kai ma ban yarda ta sake kawo maka wani abinci ba, ba na buƙatar haka, idan kuma nata kake da ra'ayin ci don Allah ka dinga zama a ɓangarenta kana ci".
Ya ƙanƙance ido da alamun ɓacin rai yana kallona, da ƙarfi ya kira sunana "Sayyada!"
Gabana ya ɗan faɗi ganin ya tsare ni da ido, na tura baki na yi juyi na juya masa baya, babu zato na ji ya damƙo ni, har sai da na ƙwalla ƙara don firgici, ya juyo da ni yana riƙe da ni kuna fuskantar juna ido cikin ido, sai na ga ya yi min kwarjini, na ce"To ka yi haƙuri, ka ce mata na ce ta yi haƙuri".
Ya sake ni, ya ce"Wucewa za ki yi mu je tun da mu ba 'yan aikenki ba ne ba ko?"
Na ce"Ka yi haƙuri, na riga na rantse ba zan ba ta haƙuri ba".
Ya ce"To shikenan, ba za mu karya miki rantsuwa ba, amma za mu yi namu hukuncin, to hukuncinki shi ne yau ba za mu ci abincinki ba, za mu saka ta kawo mana nata shi za mu ci".
A raina na ce'Na samu na É—umame'.
Ya fice daga ɗakin, na taɓe baki ina jin ashe ma hukuncin ba mai tsauri ba ne, ko da ya ji na ce kar ta sake kawo masa abinci ya yi zaton kishinsa nake yi da har zan ji haushi don ya ƙi cin abincina? Abiy ya shigo ɗakin nawa, na dinga yi masa wasa har ya yi bacci, na kwantar da shi a ɗakin na tashi na yi sallar isha'i, na koma falo, sai wajen ƙarfe tara ya dawo ɓangaren nawa, na yi masa sannu da zuwa ya amsa, ya zauna, sai ya yi gyaran murya, ni kuwa ko kallon shi ban yi ba, ya ce"Amm... Sayyada, idan kin ji mun yi gyaran murya to muna buƙatar ruwa ne ko lemo ko kuma shi haka".
Na ce"To gyaran muryar kala uku ne kenan? Yanzu sai a banbamce min, ka yi min kalar na ruwa, ka yi kalar na lemo da kalar na shayin".
Ya ce"Duka kala É—aya ne, idan mun yi mun sanar, ke ce za ki tambaya me muke nufi".
Na yi dariya na ce"To yanzu me kake nufi?"
Ya ce"Shayi za ki kawo min, sannan uzurin da zan yi miki na wannan rainin na tsayin sati É—aya ne kawai, daga nan zan fara nuna miki da gaske ni sarki ne a fadata".