← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 89

Sashe 68

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nisa ya ce"Akwai kaza da ake shigowa da ita ta amarci, mun sha'afa saboda yadda Hajiya ta matsu mu dawo gidan, ba mu siyo miki ba, sai ki yafe, ko kuma ki shiga kitchen akwai komai, sai ki gasa ki ci".

A raina na ce'Tun da ga ni mayya ba'

A fili kuma na ce"Na yafe".

Ya ce"To ki je ki yi baccinki, saboda yau mun gaji, ba za mu yi amfani da ke ba, sai dai ko zuwa gobe, ko kuma da asuba ki tashe mu idan kina buƙata".

DaÉ—i ya kama ni, a raina na ce'Allah Ya dawwamar da kai a cikin gajiyar nan' saboda gabaÉ—aya ba na so a ce wani namiji zai sake kusantata, hakan zai tuna min da abubuwa masu yawa cikin cutarwar da Ustaz ya yi min, na tsani wannan abun da ya kasance samun nutsuwa ga wasu. A fili kuma na ce"To, sai da safe".

Na tashi ya ce"Idan kin so ki kwana a É—akinmu, idan kin so kuma ki dinga kwana a naki É—akin, kawai dai damuwarmu ya zamana duk lokacin da muka so yin amfani da ke za ki ba mu haÉ—in kai".

Ban amsa ba, na dai tsaya na gama sauraron shi, na wuce É—akina na kwanta, na daÉ—e ina tunane-tunane kafin bacci ya É—auke ni, mai nauyi kuwa.

Washegari da na yi sallar asuba ban koma bacci ba, zama na yi ina ta azkar tare da saƙa da warwara, da gari ya waye na tashi na shiga kitchen, na fara kiciniya, na gama komai na gyara gidan tsaf, na yi wanka, na ci abinci, na bar masa na shi a dining, na koma ɗakina na zauna, na ji ana sallama, Hajiya ce don na gane muryarta, ina ji na ƙi fitowa, saboda na ɗauki alƙawarin nesa da ita, kar na fita ta ce na harare ta, gara dai shi ɗin ya riga ni fitowa, da na ji muryarsa alamar ya fito falon, sai na kwanta kamar me bacci, ya shigo ɗakin nawa yana kiran sunana, na buɗe ido ina amsawa, ya ce"Kin yi baƙuwa, ga Hajiya ta kawo mana abun karyawa".

Na ce"Ni ai na karya, kai ma ga naka can a dining".

Ya tsaya yana kallona na 'yan sakanni kafin ya ce"Sayyada, mun lura ba ki san kan dokar gidan nan ba, ko kuma don ba mu faÉ—a miki ba ne?"

A raina na ce'Wata sabuwa'.

Ya ce"To ni sarki ne a gidana, wannan gidan fadata ce, don haka dole ne ki girmama ni kamar yadda za matata take yi, dole ne ki dinga yi min magana da girmamawa, wannan raini ki ce min kai ma, sai dai ki ce ku ma, ni ba sa'anki ba ne, ni shugabanki ne, don haka komai za ki faÉ—a min sai kin canza harshenki da kalamai masu taushi".

Sai yanzu na samo amsar tambayar da na rasa wanda zan yi wa, tun da na zo gidan nan na ji yana yiwa kansa jam'u, kamar wani sarki ko me tare da aljanu, ashe sarauta ce, na ce"To Allah Ya ba ni iko".

Ya ce"Ki wuce ki je tana jiranki".

Na ce"Na riga na ƙoshi".

Ya ce"To ki je ki gaishe ta".

Na wuce ba tare da na sake musawa ba, ba don raina ya so ba, na je na zauna na kalle ta, har ta fi ni cin ado kamar ita ce amaryar, na ce"Ina kwana, mun tashin lafiya?"

Ta yi murmushi ta ce"Lafiya lau Alhamdulillah, ya kwanan baƙinta?"

Na ce"Mun gode Allah".

Ta ce"Ga abinci nan na yi muku".

Na ce"Mun gode, amma kuma na riga na yi sai dai shi idan zai ci".

Sai na ga ya kalle ni da sauri, na kau da kai gafe, Hajiya Halima ta ce"A yi haƙuri ranka ya daɗe tuba take, rashin sani ne".

Na yi musu kallon rashin fahimta, kafin na kai ga magana ta ce"Ƙanwata ki gyara kalamanki, kin ce shi, wannan kalma babu girmamawa a cikinta".

Nan fa ake yinta, ni ko karatu da kallon fina-finai na gidan saurauta ba na jurewa, saboda girmamawar da suke nunawa idan ta yi yawa abun haushi yake ba ni, ni ko Sarkin gaske na aura matuƙar zai tuɓe a gabana gani nake zai sassauta min mulkin nasa, ballantana wannan da na ya ari sarautar ya yafawa kansa, ko na ce ya ɗorawa kansa wahala, na yi mirsisi ban ce komai ba.

Ya ce"Zuba min abincin ni zan ci naki".

Ta ce"An gama ranka ya daÉ—e".

Ta shiga kitchen É—ina ta É—akko plate, ni kuwa na tashi na koma É—aki, ina jiyo dariyarsu da fira sama-sama, ni kuwa na koma bacci ma.

Sai da ya yi shirin tafiya aiki ya tashe ni ya ce min"Za mu fita, idan akwai abin da kike buƙata sai ki faɗa mana ko mu aiko da shi, ko idan za mu dawo mu taho da shi".

Na ce"Ba na buƙatar komai".

Ya ce"To za ki yi mana abinci kamar na mutum biyar haka, wanda za mu aiko a kai mana kai mana wajen aiki, ya kamata a ce ƙarfe ɗaya kin kammala komai kin ajiye, ki dafa duk abin da kika ga dama amma kullum da daddare tuwo nake buƙata".

Na ce"To a dawo lafiya".

Ya fita yana cewa"Ki yi magana a kawo yaron nan, ko kuma idan muka dawo daga aiki za mu biya mu É—auke shi".

Na ce"Hakan ma zai fi, ka É—akko shi kawai".

Ya juyo ya yi min wani bahagon kallon da ya saka na tuna da na saɓa dokar shi, na ɗan ɓata rai na juya daga kallon shi".

Na fito na wanke kwanukanta, na kai mata, ta karɓa fuskarta babu walwala, na juya na koma ɗaki, kafin karfe ɗaya na kammala girki tsaf, har bakin ƙofar ɗakina mai karɓar ya zo, ya faɗa min shi ne, na ba shi ya tafi, ni ma na ci na zauna na fara kiran 'yan'uwa a waya, can da yamma na tashi na ɗora tuwon, a dole na yi miyar wake saboda babu kayan yin wata miyar, na kammala komai na yi wanka na zauna na kunna kallo.

USTAZ

Haka nan yau ya ji kewar ganin É—an shi na wajen Sayyada, yana gujewa zuwa ganin na wajen Rauda don kar ya motsa kishin mijinta, to ita Sayyada tun da bazawara ce ai ba wani abu ba ne idan ya je, ya shirya ya tafi cike da fatan ma Allah Ya sa ta ga ya burge ta, ta sakko su sasanta. A hanya ta tsaya ya cikawa Abiy leda da kayan ciye-ciye irin na yara, ya karasa gidan, ya aika yaro ya ce a ce Malam Ashiru ne ya zo, Baba ya ce a ce masa ya shigo.

Ya shigo da sallama aka ba shi wajen zama, ya zauna suka gaisa, Baba ya janyo Abiy dake zaune a cinyar Mama yana cewa"Ga babanka nan ku gaisa mana".

Ustaz ya fara yi masa zance irin nasu na yara, ya bashi ledar hannunsa.

Baba ya ce"Dama ina son yin magana da kai, ban sani ba ko ka san Sayyada ta yi aure?"

Wani abu ya caki zuciyar Ustaz, ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, aure kuma? Wallahi ban sani ba, subhanallah".

Mama ta galla masa harara a fakaice, takaicinsa ya sa ta tashi ta shige ɗaki, har yanzu tana ganin baƙinshi idan ta tuna azabar da ya ganawa Sayyada.

Baba ya ce"Jiya ta yi aure, kuma mijin nata ya roƙi ta tafi da yaron nan naku, domin yana son yara, kuma ana kyautata zaton zai riƙe mata shi da amana".

Ustaz ya yi jimm kafin ya ce"Allah mai iko, yanzu Shikanan ni haka yarean za su ƙare a gidajen wasu ba ubansu ba?"

Baba ya ce"To idan ba ka amince ba ai babu dole, kana iya É—aukarsa ko yau ka tafi da shi".

Ya ce"Lala-lala, la ba'asa wallahi, a gaskiya ba ni da mata a halin yanzu, idan ma akwai ban san irin riƙon da za ta yi wa yaron nan ba, saboda haka idan na raba shi da mahaifiyarsa na cutar da shi, Allah ba zai bar ni ba, su ɗauke shi ɗin, amma idan na buƙaci ganin shi zan yi maka waya sai a kawo shi gidan nan na zo na gan shi, tun da dai ai ba za a raba hanta da jini ba".

Baba ya ce"Babu damuwa in sha Allah!".

Ustaz ya yi musu sallama ya tafi yana cewa"Allah Ya ba su zaman lafiya".

A ran shi kuwa cewa yake Allah Ya sa mijin rago ne ta kasa zama da shi ta ji kewar shi ta buwaye ta, a ga ta tsiya.

Ustaz bai daÉ—e da tafiya ba mijin Sayyada ya zo, ya É—auki yaron ya tafi da shi, da yake yana son mutane sai ya saba da shi bai yi masa kuka ba, a hanya ya tsaya ya yi masa siyayya, duk da ya ga an haÉ—o shi da ta wajen Ustaz, sannan ya siya kazar amarci ya kama hanyar gidan, a ransa yana rayawa yau zai ji kalar test É—in mara kunyar yarinyar nan.

08028966015
[10/11, 8:09 pm] Sadiya Abdulrazak: 41

Kafin ya ƙaraso gida sai da Mama ta kira ni a waya muka gaisa ta ce"Sayyada ga mijinki nan ya zo ya karɓi ɗanki, don Allah ku zauna lafiya da mutumin nan, me sonka shi yake son naka, kuma don Allah kar ki tauye masa kulawarki saboda yaron nan, Allah Ya ba ku zaman lafiya".

Na ce"In sha Allah Mama".

Ina nan zaune na ji me gadi ya buɗe masa gate, ya daɗe kafin ya ƙaraso, hakan ya sa na gane ɓangaren Hajiya Halima ya fara sauka, ya shigo da sallama, na amsa ina kallon ɗana, da yake ƙoƙarin zamewa daga hannunsa zai taho wajena, ya sauke shi yana cewa"Au kenan wariya za ka nuna mana ko Dauda?"

Na É—ora Abiy a cinyata ina ce masa "Sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa" Yana zama a kujera.

Na tashi na É—akko masa ruwa da lemo na ajiye, zan bar wajen ya ce"Dawo ki zuba mana".

Na dawo na zuba masa a kofi, sannan na koma kitchen na kwaso tuwon shi na kai dining, na dawo na ce"Ga tuwonka can a dining".
Chapter 68 · 0% Book details