← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 89

Sashe 65

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce"Amma za ki ce wannan sangamemen mutumin ba shi da aure, ko kuwa kishiyar ta gidana ce ba za ki iya zama da ita ba?"

Ta ce"Ƙwarai kuwa ba shi da aure, ya yi aure amma yanzu sun rabu da matar, don haka zan aure shi in sha Allah, nan da sati uku".

Wani abu ya daki zuciyar Ustaz ya ce"Ban gane sati uku ba, me kike nufi kenan? Kina nufin za ki tsige yarona daga nono ba tare da kin yaye shi ba saboda za ki yi aure?"

Ta ce"Babu dalilin yaye shi lokaci bai yi ba".

Ya ce"Kina nufin da ɗana za ki tafi gidan wani zindiƙi alhalin kina shayarwa? Ɗana ya sha abun nan, shi ma ya sha? To haram, muddin kika tafi ɗana wallahi na haramta miki ki ba shi abin nan ya sha, har sai kin yaye ɗana, wannan wane irin kwaɗo ne? Saurin me kuke yi da ba za ki bari ki yaye shi ba?"

Ta ce"To idan kana da iko ka yanke abun ka haÉ—a da É—an ka tafi da shi, tun da dai ka fi ni iko da jikina, aure babu fashi, nan da sati uku in sha Allah".

Hankalin Ustaz ya tashi sosai, ya ce"Kin ga Rauda mu bar wanann sa'insar, ni fa yanzu bazawari ne, na saki ita amaryar saboda ke, bi ma'ana na gano ke nake so na ke ba, na gaji fa kewarki, don haka a yi haƙuri ki dakatar da wannan aure mara fa'ida, mu mayar da aurenmu a gobe ma, ina da sadakin da zan ba ki in sha Allah!".

Rauda ta ce"Ai ka riga ka makara, ka ɓarar da damarka, na gama aurenka in sha Allah, sai sabon miji, sabuwar rayuwa".

Daga haka ta shige gidan ta bar shi tsaye yana salati.

08028966015
[08/11, 7:15 pm] Sadiya Abdulrazak: 39

Ustaz fa ya shiga tashin hankali, sai yanzu ya gane ma ashe sosai yake son Rauda, kuma idan ya rabu da ita ya tafka babbar asara, tun da har ta iya zaman da ta saba da shi da larurar shi ai ba ta cancanci haka daga gare shi ba, da a ce ya san wacce zai aura ba za ta iya sabawa da shi ba, da zai zaɓi ya fasa auren a kan dai ya kashe kuɗinsa kuma ya saki wacce take iyawa da shi, ya so ya tunkari mahaifinta da maganar amma kunya ta hana shi, da ya tuna duk irin halakcin da mutumin ya yi masa amma ya shafawa idanunsa toka ya sakar masa 'ya, ya matsawa Rauda da waya yana roƙonta ƙarshe ma sai ta yi blocking ɗinsa, tun daga ranar kullum sai ya je, duk da ba fita take ba, wataran Daddy ya rufe ido ya taka masa burki da cewar tun da ta ce ba za ta koma ba ya rabu da ita, daga nan ya haƙura ya saddaƙar, ya rungumi ibada da kasuwancin shi.

Allah Ya taimake shi ranar ɗaurin Rauda ba ya garin, Daddy ya aike shi wata tafiya ta sati ɗaya, amma da ya zai ji a ce ya je ɗaurin aurenta? Kuma ba zai iya ƙin zuwa ba saboda yi wa Daddyn kara, kuma yana takaicin wai a ce an rasa me tsawatar mata, da ɗan shi za ta tafi gidan wani ƙato ko yaye shi ba ta yi ba.

Rauda amarya ana ta rawar kai da ta jiki an yi sabon aure, tabbas tana son Ustaz, amma tun da ya iya zaɓar rabuwa da ita a kan ƙarin aure ya fita daga ranta, ta dinga ƙoƙarin mantawa da shi, za a iya cewa ta yi nasarar cire son shi daga zuciyarta da kaso tamanin cikin ɗari, amma fa tun kafin wata ɗaya da mutuwar auren gangar jikinta ta fara kewar shi, dama can ya lafiyar kura ballantana ta yi hauka? Tun tana buduruwa take fama da yawan jin sha'awa ballantana yanzu da ta yi auren, kuma ta gamu da miji irin Ustaz, kuma a ce yanzu za ta yi sabuwar rayuwar da babu namiji? Haka ta dinga daurewa, shi yasa tana gama idda ta fara kula mazan da suka samu labarin mutuwar aurenta, a ciki kuma ta zaɓi tsohon saurayinta Habibu, domin ta yarda da soyayyar da yake yi mata.

Tana kewar kashe arna, don haka ta yi gyara sosai, ta kashe kuÉ—i kamar za ta koma buduruwa, bayan 'yan kai amarya sun watse tana zaune a falo da É—anta, wanda bai kai ga yin bacci ba, saboda ya yi na yamma, tana ta yi masa wasa, ango ya shigo cike da zumuÉ—i, amma sai ta ga karsashin na shi ya ragu, ya nemi waje ya zauna a kusa da ita yana faÉ—in"Ranki ya daÉ—e amaryata".

Ta ce"Sannu da zuwa".

Ya kalli yaron, sai haushin shi ya kama shi, saboda ya rage masa jin daɗi, ba don da shi ba da yanzu ya rungume ta, ko ita ta zo ta tare shi tun kafin ma ya zauna, ƙila ma da a rufe zai zo ya tarar da fuskarta, ya buɗe mata kamar buduruwar amarya, amma wannan yaro ya canza lissafin, dama har ran shi ba wai son yaron ne ya sa shi cewa ya yarda a yi auren ba, kawai ita yake so, kuma ya gaji da zaman gwauranci shi ma yana so ya yi aure, da ma tsoron ya bari ya huce lokacin da za ta yaye ɗan kuma wani ya canza mata tunani, amma a gaskiya zai rage masa jin daɗi.

Ya sauke numfashi ya ce"ÆŠan naki bai yi bacci ba ne?"

Ta ji kalmar É—an naki babu daÉ—i, ko babu komai ai ya kamata ya yi mata kara, ta maze ta ce"E tukuna dai".

Ya ce"To ai shikenan, amma dai da kin ajiye shi mun yi sallah, mun yi abin da yake gabanmu ko?"

Ta É—an yi jim kafin ta ce"Bari na goya shi".

Ya ce"A haba wane irin goyo? Ajiye shi don Allah".

Ta ce"Da na goya shi É—in ai bacci zai yi".

Ya tashi ya yi gaba zuwa ɗakinsa yana cewa"To shikenan idan ya yi baccin kya ƙaraso, ina jiranki".

Duk sai jikinta ya yi sanyi, don ta saka ran nuna soyayya da rawar ƙafa sosai a daren farkonta da Habibu, sai ta ga saɓanin haka. Ba ta gama tsinkewa ba sai da ya yi baccin ta je ta kwantar da shi a nata ɗakin, ta sake yin wanka ta yi alwala ta ɗora hijjabi a kan rigar baccin, ta kwashi kayan ciye-ciye da ya dawo da su ta juye ta nufi ɗakin nashi, yana zaune yana danna waya, ta shiga da sallama, ya amsa yana murmushi ya ce"Masoyiya ya yi baccin?"

Ta ce"Ya yi".

Ya ce"To Allah Ya sa dai ba ya farkawar dare, don gaskiya ba zan so a ce ki dinga katse mana jin faÉ—i ba idan ya farka".

Ta yi murmushin yaƙe ta ce"Ai kuwa yaro mai shan nono ba a raba shi da farkawar dare".

Ya ce"To a gaskiya ina ga za a ɗaukar masa mai raino ta dinga kwana da shi, idan ya farka ta ba shi madara, wannan duka zan ɗauki nauyi, kawai saboda na samu kasancewa da ke tun daga farkon dare har ƙarshe".

Rauda ta yi jimm, sannan ta ce"Amma kuma ga ni da raina da lafiyata, sannan hidimar gidan ba yawa ta yi min a ce a É—aukarwa yarona mai raino kuma a na ba shi madara?"

Ya ce"To ya kike so a yi kenan idan ba haka ba Rauda? Ai na faÉ—a miki uzurina".

Ta ce"Na ji uzurinka, amma a matsayina na uwa, uwar ma me haihuwar farko zan ɗauki uzurinka a matsayin mai rauni, na yi maka alƙawarin za mu dinga kwana tare, amma zan dinga zuwa ina duba halin da ɗana yake ciki dole, kuma ba na bukatar sirka masa shayawar da madara, ka yi min wannan alfarmar".

Ba don ya so ba ya ce"To shikenan".

Suka yi sallah, suka yi ciye-ciyensu, har alla-alla yake a gama su kwanta, yana ta nuna zalamarsa, wanda hakan yake farantawa Rauda, tana jin yau za ta sauke nauyin dake tare da ita tun mutuwar aurenta. Da fari kamar za a yi abun arziƙi, amma sai dai me? Ana shiga fagen dagar komai ya kuncewa Rauda, wannan abu da ya faru a daren yau ta iya cewa an lasa mata zuma ne a baki an janye, saboda sanda ta fara ɗaukar saiti shi kuma lokacin ya samu cikakkiyar gamsuwar shi, ya matsa gefe, gabanta ya faɗi, sosai ta shiga damuwa, don ita ko ɗakko hanya ma ba ta yi ba, ta so ta kalli agogo kafin farawar, amma duk da ba ta kalla ba ta san a ƙiyasi ba zai wuce minti goma ba, tana ta wannan saƙa da warwara har ya yi wanka, ya dawo ya rungume ta yana tambayarta ba za ta yi wanka ba sai da asuba?

Kamar ta ce masa bai ishe ta ya taimake ta ya ɗan ƙara, amma ta zame a sanyaye ta sauka daga gadon, ta shiga wankan, bayan ta gama kafin ta kwanta sai da ta je ta duba ɗanta, ta dawo ta kwanta, ya rungume ta yana yi mata firar soyayya, hakan ya sa ta ji kamar susa yake yi mata a saboda halin da take ciki, tana jin lokacin da ya yi bacci, ita kuwa ta kasa yi da ƙyar ta samu ta ɗauke ta.

Tana jiyo kukan ɗanta ta zame ta tafi, a nan ta ƙarasa baccinta. Washegari da asuba ta yi zaton zai ƙara yi mata ko minti goman ne, amma sai ta ga babu alama, haka da rana a gidan ya wuni amma sai dai ya yi ta taɓa ta, wancen babban lamarin dai babu shi, duk da yana ta yi masa sambatun daren jiyan, sai dare, yau kam da wuri yaro ya yi bacci, don haka tun farkon dare aka fara kashe arnan, wata zuciyar tana ta faɗa mata jiya gajiyar ɗaurin aure ce ta sa shi rashin nisan zango, yau zai ba ta mamaki, amma me? Sai ga shi irin na jiyan dai, a ranta ta ce'Na shiga uku ni Rauda, a haka rayuwar za ta tafi?'
Chapter 65 · 0% Book details