← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 89

Sashe 5

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na yi zaton tun asuba Sadam zai zo, na ji shiru har gari ya waye, ga yunwa ina ji, ina cikin jerin mutanen da ɓacin rai ko jinya ba ya hana su cin abinci, ko macaroni da ban ci ba jiya kishi ne, na ƙara haɗa shayi na sha, na ci kazar, don da na duba ta na fahimci gashin bakin titi ne ba ita ce ta gasa ba, ina ci ina hawaye, idan na tuna Sadam yau ya kwana da wata a gadonmu na sunna sai na ji kamar rayuwata ta zo ƙarshe, fitar numfashina har canzawa ya yi.

Wajen ƙarfe tara da rabi na gaji da jiran shi, na daure zuciyata na ɗauki waya ba kira shi, kira biyar bai ɗauka ba, zuciya tana ta raya min yana can tare da mace sun ɗora daga inda tsaya daren jiya, sai na ji ba zan iya cigaba da zaman asibitin ba, duk da da safen nan da likitan ya duba ni ya sake ba ni haƙuri ya ce na bari Sadam ɗin ya zo sai a ji yadda za a yi, sai ya dinga zuwa gida yana duba ni kullum, amma na kasa haƙuri na tashi na ɗauki wayata na saka hijjabi na fice, Allah Ya taimake ni har na bar cikin asibitin ba wanda ya gane ba ni da gaskiya.

Na tari adaidaitasahu na hau, a hanya ma sai hawaye nake yi, ina kuma fargabar abin da zan je na tarar, wallahi Indai ya tabbata da wata a gidan dole ya sake ni duk taurin kansa.

08028966015
[24/09, 9:26 am] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1

*KU YI MANA ADALCI*

NA
Sadiya Abdulrazak

Page 4

Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima'ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500 💃 munamaraba damasu siyan Daya ko sari

Page 4

Muna dab da ƙarasawa gidan na hangi wata mace ta fito daga gidan tare da Sadam, ƙirjina ya doka da ƙarfi, sai dai kafin adaidaitasahun mu ya ƙarasa tuni ta hau adaidaitasahun da ya zo wucewa an ja sun tafi.

"Tsaya! Sauke ni haka!" Na faɗa da ƙarfi don ganin Sadam ya juya da sauri zai koma cikin gidan, ko gama tsayawa bai yi ba na fito hakan ya sa na faɗi a ƙasa tim, ban damu ba na miƙe da sauri na cim ma Sadam da yake shirin shiga gidan, shi kuwa wata kunya ce da fargaba ta kama shi, saboda ya san dole ta fa Safna, kuma sai yake ji kamar za ta gane ya rungume Safna har ma ya yi kissing ɗinta a cikin gidansu.

Da sauri na fizgo jallabiyar jikinsa cikin ƙaraji na ce"Wace ce wannan!? Sadam da wa ka kwana a cikin gidana?"

Yana juyowa ya sharara mini mari, rai a haɗe ya ce"Ashe ba ki da hankali! Ni za ki yi ƙazafi a titi a bainan nasi?"

Na ci kwalarsa na fashe da kuka ina cewa"Ni za ka mara a kan hakkina? Ba zan sake yarda ka ci zarafina a kan gaskiya ta ba wallahi, wace ce wannan ka rako ta? Uban me ya kawo ta gidana da sassafe? Kuma uwar wace ta yi maka girki juya a cikin gidan nan?"

Da ƙarfe ya ƙara min marin, sannan ya fizge rigarsa, takaici da zafin zuciya suka saka ni zubewa a wajen na rushe da kuka, ga shi ƙofar gidanmu titi ne, masu ababen hawa har sun fara fakawa suna kallonmu, cak ya ɗauke ni ya yi cikin gidan da ni, ina ta zillewa ina zagin shi ina faɗin"Ka ajiye ni, wallahi yau sai ka sake ni, kuma ba zan taɓa yafe maka ba, ɗan iska, fasiƙi, mazinaci".

"Kar fa ki fama hannunki, ba ki da hankali ne?" Ya faÉ—a kamar bai damu da zagin da nake yi masa ba.

Bai ajiye ni ba sai da ya sada ni da ɗakina, ya kulle ƙofar, duk da ba a hayyacina nake ba, amma idona tarr ya sauka a kan gadona, inda na ga pant yashe a gadon, an buɗe shi kamar wanda aka shanya shi, tashin hankali bai sa na tsaya na yi wa wandon kallon tsanaki ba, da tabbas zan gane nawa ne, na zauna a jikin ƙofar na ɗora hannu a kai na rushe da kuka ina cewa"Na shiga uku, Sadam ka cuce ni ba zan taɓa yafe maka ba".

Duk wannan ihun da nake yi yana falo yana jiyo ni, shi ma kuma abun duniya ya ishe shi, ya yi nadamar gayyato Safna, Allah ne shaidarsa bai taɓa kusantar wata mace ba bayan Sayyada, duk 'yan tsalle-tsallensa a iya waya yake ƙarewa, wannan ta san yana yi, yana yin sex chart har ya samawa kansa nutsuwa, amma ya sani a yadda soyayyarsa da Sayyada ta kasance kafin aure dole za ta iya zarginsa a yanzu, ai shi ne ya zubar da garinsa a wajenta, amma idan za ta yi masa adalci tun da bai zarge ta ba, bai kamata ita ma ta zarge shi ba, dalili kuwa shi ne ita da shi ɗin ƙwaryar sama ce ta daki ta ƙasa.

"Sayyada aurenki fa zan yi, an saka ranar aurenmu, ɗaurawa ne kawai ya rage, idan ba ki yarda da ni ba a yanzu sai yaushe? Ashe ba ni da wata alfarma a wajenki? Ba ni da matsayin da zan nemi abu ki ba ni? Please just romance, ki amince da ni, ba za ki taɓa danasani ba". Na rintse ido tunawa da irin kalaman yaudarar da ya dinga yi mini, nuna mini yake duk matan duniya ma shi ƙyamar su yake, da ni kaɗai zai iya sex, ashe zai iya maimaitawa wata macen wannan kalaman da ya yi mini amfani da su har na amince? Kuma idan ta amince har ya aikata? Lallai duk wacce ta yarda da daɗin bakin namiji za ta sha giyar mamaki ta yi mankas har ta yi tuɓumle, ni Sayyada kura-kuran da na yi a kan Saddam sai dai na roƙi Allah Ya yafe mini kawai, amma na tabbata shugabar daƙiƙan matan duniya, a gaba za ku ji labarin kalar tawa soyayyar.

Na ci kuka na gode Allah, a nan ƙasan ɗakin bacci ya kwashe ni ban shirya ba.

Sai da ya daina jin kukana sannan ya buɗe ni, a zatonsa na yi haƙuri ne, sai ya same ni ina bacci, ɗaukata da ya yi don mayar da ni kan gado ne ya farkar da ni, na sauke idona a cikin nashi, na zabura zan dire sai na fama ciwona, na saki kukan azaba ina jin dama kawai na mutu na huta, don ganin Sadam yana azabtar da ni ba kaɗan ba.

"Sorry Sweetheart". Ya kira ni da sunan da yake yi min daÉ—i a da, amma yanzu haushi na ji maimakon daÉ—in.

"Ka ajiye ni". Na faÉ—a ina hawaye

Ya ce"Ok" Ya É—ora ni a gadon.

Na ce"Na tsane ka!".

Ya ce"Ki dakata da wannan shirmen please, ya jikin naki?"

Na haɗiyi yawun baƙin ciki, ban da raini ni zai tambaya ta jiki? Na rufe ido kawai hawaye yana sake kwaranya daga idona.

Ya ce"Ki tashi ki ci abinci ki yi wanka ko za ki daÉ—in jikinki".

Na yi shiru ban kuma buɗe idona ba, tabbas Allah Ya taimaki Sadam da ya ƙaddara wannan ciwon na hannuna, da yau ban san adadin haukan da zan nuna masa a cikin gidan nan ba, ganin na lumshe ido ya yi zaton bacci nake yi, sai ya tashi ya bar ɗakin, yana fita na tashi leƙa shi ta window, na hangen shi a falo yana waya, ba dai na jiyo abin da yake cewa, yana shiga ɗakinsa na saka hijjabi da takalmi da sauri ko wayata ban tsaya ɗauka ba, na fito cikin sanɗa na bar falon, Allah Ya taimake ni mai gadi yana cikin ɗakinsa, don haka na buɗe gidan na fita, Allah Ya sake taimakona na fita daidai adaidaitasahu ta ajiye maƙocinmu, na faɗa ina faɗa masa ya yi sauri ya ja mu tafi, ai kuwa ya bi umarnina ya fafake mu a guje yana tambayar lafiya? Na ce"Mahaukaci ne ta biyo ni, kuma gudu gare shi kamar babur".

Ya ce"Subhanallah! Gaskiya to ba ki kyauta mini ba, salon ya yi jifa ya fasa kin glass?" Ya ƙara gudu sosai, cikin sakanni muka bar unguwar.

Na yi iya ƙoƙarina na ganin na saita kaina kafin na shiga cikin gidanmu, na shiga ɗaki na gaishe da Mama na ce ta ba ni ɗari biyu zan bawa mai adaidaitasahun, ta ba ni, na fita na kai masa, sannan na dawo ɗakin, na zauna na sunkuyar da kai.

Ta kalle ni ta ce"Sayyada lafiya kuwa? Na gan ki a hargitse me ya faru?"

Sai na fara kuka na ce"Babu komai".

Ta ce"Babu komai za ki zo haka ba shiri ki saka ni a gaba da kuka? Ba za ki faÉ—a ba? Ko ke da Sadam É—in ne?"

Na gyaÉ—a mata kai alamar e, don na shirya sanar da ita abin da yake faruwa, saboda a yadda nake ji a raina kawai na gama zama da Sadam, damuwa ta bayyana a fuskarta ta ce"Mene ne ya faru? Wani abun ya yi miki?"

Daidai nan kuma Baba ya yi sallama a É—akin, na gaishe shi, bai amsa ba ya ce"Sayyada, kukan ne kike yi?".

Mama ta ce"Ita da mijinta ne, yanzu nake son jin mene ne ya haÉ—a su".
Chapter 5 · 0% Book details