← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 89

Sashe 54

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya kwana a wahale, washegari da safe ya gyara gida ya dafa shayi, ya soya dankali, ya ci rabi ya goge bakinsa, ya ajiye mata rabi, zama ya yi a falon, ba shi da shirin zuwa kasuwa, don ya ma daina zuwa, sai dai ya je ya yi musu sallama kawai, Rauda tana ta jira ta ji fitarsa ta fito, amma ta shi shiru, sai da ta fara jin yunwa ta daure ta fito tana ta ɓata rai.

Kallonta kawai ya yi wani yawu ya tsinke ya silala maƙoshinsa, saboda jiya ya kwana da kewarta ba kaɗan ba, ya ce"Sannu da fitowa, kin tashi lafiya?"

Ta ce"Lafiya lau".

Ta wuce kitchen, ya tashi ya bi ta, yana ƙarasawa ya rungume ta ta baya, ta ce"Don Allah sake ni".

Ya ce"Wannan matata ce kuwa? Gaskiya masoyiyata Rauda ba za ta yi mini haka cikin hayyacinta ba, me na yi miki don Allah, ki faÉ—a min na gyara kuskurena".

Ta ce"Ba kuskure ba ne, ba kuma laifinka ba ne, kawai kasancewarka hariji ya sa na gane ba mu dace da juna ba, kamata ya yi ka nemi harija ni kuma na nemi mai lafiya, don cigaba da zamanmu akwai cutarwa".

Ta fizge ta fara ƙoƙarin kunna gas, ya ja baya yana cewa"Ga abincin can fa a dining na yi miki dankali da shayi, kuma akwai biredi ma".

Ta fita ba ta kula shi ba, ya bi bayanta, ya riga ta ƙarasawa ya haɗa mata shayin, ya zuba mata dankalin a faranti ya tura gabanta, ya zauna ya ce"Ko na ba ki a baki?"

Sai ta ji tausayin shi kaɗan, Allah Ya sani tana son Malam Ashir, kuma kyautatawar da yake yi mata da haƙurinsa ta san ba duk wani namiji ne zai yi ba, yanzu jiya duk abin da ta yi masa amma yau ya tashi ya mata girki bai fasa ba, har ma yana so ta ba shi dama ya ba ta a baki, yana da kyakkyawar zuciya, amma hakan ba zai sa ta zauna ya kashe ta ba ko ya nakasa ta.

Ya ce"Me na yi miki don Allah, indai wannan ne za a yi minus one, yanzu zan dinga haƙuri idan za ki ba ni sau ɗaya kullum, kin ga sai ya zama da daddare kawai za a dinga yi ko?"

Ta ce"Ni fa ba zan iya ba, ai ko sau É—ayan ma cutata za ka yi, tun da mutane normal ba haka suke yi ba, an ce min na a fin awa É—aya ko minti talatin".

Ustaz ya ce"Subhanallah! Allah Ya yi min tsari da minti talatin, Rauda kin san wane ne mai irin larurata kuwa? Jina nake ko kwana uku zan yi ban guda daga gare ki ba ba zan gamsu ba, ana bari kawai don ba shi aka turo mu duniya ba, a yi dai zancen da zai yiwu, amma maganar minti talatin ko awa É—aya ba ta taso ba, me aka yi da maza?"

Ta ce"To ai shikenan, ka sake ni ka auri wacce za ta iya kawai".

Ya ce"A haba wannan ai zance ne, Rauda ni da ke mutu-ka-raba in sha Allah".

Ta ce"Wallahi ba zan iya ba, zan sanarwa iyayena tun wuri su san halin da nake ciki".

Ustaz ya ce"A'a Rauda don Allah kar ki zama matan da suke bankaɗa sirrin shimfiɗar aurensu, idan na yafe miki ya za ki yi da hukuncin da Allah Ya tanadawa waɗan nan mata? Ina son rayuwa da ke har aljanna, don Allah ki riƙe min sirrina, kar ki zama Sayyada da Maraƙisiyya".

Ba ta sake magana ba, ta gama karyawa ta tashi ta tafi ɗaki, ya tattare wajen, ya bi ta, ya tarar ta rufe ƙofa, ya ce"Innalillahi wa ilaihi raji'un, ashe dai wahala ba ta ƙare min ba ni Ashir".

Ya koma falo ya zauna yana ta tasbihi, tunanin Sayyada ya faɗo masa, ita tana jin wa'azi ta amince ko ba ta so, amma wannan kamar 'yar Fir'auna? Sannan ba zai iya yi mata ta ƙarfi ba kamar yadda ya sha yi wa Maraƙisiyya, ita wannan lallaɓa ta zai yi tun da ya ga aurenta zai zame masa jari, ga shi daga aure wata ɗaya ya samu canjin wajen aiki, dole zai haƙura da wasu abubuwan su yi komai cikin lumana da sasanci.

Ta ɗauki waya ta ba wa Zainab labarin abin da yake faruwa ta whatsApp, ba ta online ma, ta kira ta ta faɗa mata ta yi mata magana ta hau online, ai kuwa tana hawa ta saurara ta yi mata voice ta zuge ta tass, ta ce"Wallahi ke ma Rauda son shi kike, na lura ba kya tsoron mutuwa, indai kina zauna a gidan ai wallahi sai ya yi miki kwanta-kwanta ya haike miki, ko lafiyayyen miji ne kuka kwana biyu ba kwa tare ranar da kuka haɗu ya take kasancewa? Ballantana kuma hariji, Rauda Allah Ya ji ƙanki kawai".

Rauda ta rikice ta ce"Don Allah ki daina tsorata ni, ki faÉ—a min ya zan yi?"

Ta ce"Ki tattara kayanki ki bar gidan, ki je gida ki faÉ—i halin da ake ciki, Wallahi idan ba haka ba za ki tsinci talatarki a Laraba".

Rauda ta ce"To bari na tafi".

Ta tashi ta hau haÉ—a kayanta, kuma a cikin zuciyarta ba ta som tafiyar, tana son shi, sannan ba ta so a ce aurenta zai mutu a yanzu ba, tana ma jin kunyar bayanin da za ta yi idan ta je gida, haka ta fito tana jan akwati, Ustaz yana kwance yana karatun Qur'ani a wayarsa ya ga fitowarta tana jan akwati, ya kai aya ya ajiye wayar, ya tashi da sauri ya nufe ta hankali tashe, ya ce"Rauda, Raudata me zan gani haka?"

Ta ce"Gidanmu zan tafi, ai na faÉ—a maka ba zan iya ba".

Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Haba Rauda me ya yi zafi? Mene ne damuwar wai? Kin ga zauna don Allah, ki rufa min asiri na ga samu kuma na ga rashi?"

Ya ce"Ba abin da za ka faÉ—a min na yarda da kai, don haka ka ba ni hanya".

Ya zube a gabanta ya fashe da kuka amma babu hawaye ya ce"Don darajar Allah da Manzonsa ki yafe min Rauda, soyayya ce ta haɗa mu ba ƙiyayya ba, ba dai a kan raya sunna ba ne? To daga yau na yarda a rabu da arnan nan su yi ta rayuwarsu, ba sai an kashe su ba, sai dai kuma su arna suna iya yaɗa ɓarna a bayan ƙasa, dama shi ne amfanin auren don a kashe su a kauda ita ɓarnar, amma tun da kin ce haka ni na haƙura wallahi, na yi miki alƙawarin ba zan sake nemanki ba, sai dai idan kin ji marmarina sai ki faɗa min, kina da dama tun da ai hakkinki ne ko?"

Jikinta ya yi sanyi, kuma ta ji tausayin shi, kuma ta ji a ranta indai da gaske yake za su rayu a haka ba zai neme ta ba za ta haƙura su zauna, ta ce"Ka yi alƙawarin da gaske ba za ka sake nema na ba?"

Ya ce"Ƙwarai kuwa, in sha Allah ko gado ɗaya muka kwana sai dai mu kalli juna, zan daure in sha Allah, ai kowane bawa da kalar ƙaddarar shi, amma don Allah ki dinga yi min adalci" Ya ƙarasa maganar muryarsa tana rawa.

Ta ce"To na ji, amma daga ranar da ka saɓa alƙawari zan tafi gidanmu".

Ya ce"In sha Allah ma ba zan saɓa ba".

Ya karɓe akwatin ya mayar ɗakin, ya buɗe ya jera kayan duka a sif ɗin, tana zauna a gefen gado tana kallon shi, ya gama zai fita ya kalle ta ya ce"To shikenan Rauda Allah Ya ba ni ikon jurewa, kuma ni fa na yafe miki".

Ya fita daga É—akin, ta bi shi da kallon tausayi, ta É—auki waya ta faÉ—awa Zainab yadda suka yi da shi, Zainab ta ce mata wannan fa ba dabara ba ce, saboda ba lallai abun ya É—ore ba, Rauda ta ce ta ga alamar zai É—ore, saboda ta ga nadama a fuskar shi.

Suka wuni a falo suna fira kamar komai bai faru ba, suka yi girki tare suka ci abinci, da yamma ya fita ya je kasuwa ya sanar da su zai fara wani aikin, bai dawo ba sai dare, bayan ya ci abinci yake tambayarta"To Rauda ya batun makwanci fa? Za mu raba ne ko kuma a É—aki É—aya za mu cigaba da kwana?"

Ta ɗan yi jim kafin ta ce"Ba matsala za mu iya kwana tare, kai dai ai ka san alƙawarin da ka yi ko, sai ka yi ƙoƙarin kiyayewa".

Ya ce"In sha Allah zan kiyaye".

Da aka zo kwanciya sai ta saka filo guda biyu a tsakaninsu, ta kuma juya masa baya, Ustaz ya rasa ta ina zai fara wannan sabuwar rayuwa mai cike da sammatsi.

Haka suka kwana ya daure bai ko gwada taɓa ta ba, amma yana ji a jikinsa fa.

Haka aka fara sabon zama, Ustaz yana ta ƙoƙarin daurewa, ita kuma ko a jikinta, kuma haka za ta dinga shiga ta ɗaukar hankali, sai dai ya kalla ya haɗiyi yawu. Cikin satin ya fara zuwa aiki, shago ne babba wanda ake siyar da electronics, aka fara nunawa Ustaz yadda kasuwar take, kuma yana fahimta, yana gudanar da komai cike da ɗaukin abun.

Tun yana daurewa har abun ya fara fin ƙarfin shi, sai ya tsiri wani abu, sai Rauda ta yi bacci sai ya tashi ya kunna fitilar wayarsa ya dinga haskata, yana kallonta yana haɗiyar yawu, kuma hakan ƙara masa wahala kawai yake yi, idan ya kunnu da yawa sai ya bar ɗakin ya koma falo ya biyawa kansa buƙata.
Chapter 54 · 0% Book details