← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 89

Sashe 75

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce"To ka fara ba ni goron albishir É—in, wayarka nake so kuma".

Ya ce"Kin san kuÉ—in wayar nan kuwa?"

Na ce"Ni dai ita nake so, idan ba haka ba na koma da albishir É—ina".

Ya ce"Ki fara yi min jam'u zan iya siya miki irin wayata".

Na ce"Yanzu nake so, don wannan albishir É—in ya fi jam'u a wajenka".

Sai kuwa ya sha jinin jikinsa, ya fara kallona da zaƙuwa ya ce"Sayyada, mene ne? Wane albishir ne?"

Na ajiye masa takardar a cinyarsa, ya kalle ni ya ce"Ta mene ne?"

Sai kuma ya duba ya gani, ai kuwa ya yi kabbara, ya yi hamdala, ya yi sujjadar godiya ga Allah, ya É—ago ya É—aga hannunsa sama ya dinga kwararowa Allah godiya, sannan ni ma ya fara yi min addu'a yana faÉ—in Allah Ya sauke ni lafiya Ya ba ni duk abin da nake nema, indai aljanna ce ya É—aga min na shiga, jam'u kuma ya yafe min ba sai na yi ba, har na fara tunanin anya wannan matar ba ta haukata shi ba kuwa? A ce ka É—aga hannu kana yi wa Allah godiya har da zancen jam'u?

Sai da na ga ya fara hawaye, sannan na É—aga shi, na zaunar da shi a kujera ina share masa, sai ya rungume ni yana cewa"Na gode Sayyada, don Allah ko bar cikin nan ki haihu lafiya kin ji?"

Na ce"Allah za ka godewa, kuma shi za ka roƙa ya bar mana shi na haife shi lafiya".

Ya ce"Alhamdulillah, yanzu iya wayar tawa kike so ko da wani abun? Na cire layukan na ba ki ko za ki jira na sayi wata gobe na kwashe abubuwa daga ciki?"

Ya fara kiciniyar cire cover wayar, na lura nema yake ya zaune fa, ya karɓi wayar na ajiye, na kwanta a jikinsa, na ce"Ka samu nutsuwa, kar ka sa na fara tunanin ranar da na haihu aka damƙa maka yaro ko yarinya a hannu sumewa za ka".

Ya ce"Na ji daɗi ne sosai, Alhamdulillah! Ina son haihuwa sosai Sayyada, da kika yi wata ɗaya ban ga alamar ciki ba na fara fargaba, kawai ina ta ɓoyewa ne, ashe abun yana tafe, Allah Ya sauke ki lafiya".

Na amsa da amin, da ya ba ni wayar na ce da wasa nake yi, washegari sai ga shi ya siyo min irinta sak a kwali, a cikin satin ya samo min mai taya ni aiki, ya ce bai yarda na sake yin aikin komai ba, tun da ranar da ya san ina da ciki yake ta kaffa-kaffa da ni, ya ƙi kusantata wai tsoro yake kar wani abu ya samu cikin, kuma ina lura da shi yana buƙatata, na fahimtar da shi babu komai ya ƙi fahimta, sai da na tausaya masa na nuna masa ni ce nake buƙatar ya ba ni hakkina sannan ya saki jiki da ni.

Kulawa nake samu ba ga shi ba, ba ga 'yan'uwanshi ba, duk sati sai an canza girki daga gidansu an aiko min, ƙarshe na ce ni zan dinga zuwa, don haka duk ranar Juma'a idan zai fita tare muke fita, ya kai ni gidansu, da daddare sai ya ɗakko ni, to a ranar sai abin da na zaɓa zan ci.

Tun cikin yana ƙarami muke siyayyar kayan haihuwa, tun da aka samu cikin nan ban sake ganin murmushin Hajiya Halima ko da kuwa na yaƙe ne, don mun sha ma haɗuwa a tsakar gida na gaishe ta ta yi banza da ni, ƙarara take nuna rashin jin daɗinta a kan cikina, ba wai saboda kishiyata ba ce, na saka ta a sahun matan da ba su da adalci, duk mutumin da zai san ba ka haihuwa kuma ba za ma ka haihu ba saboda an cire maka mahaifa, amma ya cigaba da zama da kai da kyautatawa tabbas mai sonka ne, kuma rashin adalci ne zai sa ka yi adawa da samun haihuwar shi, kuma abun mamaki shi sam ba ta nuna masa, tun da yana yawan faɗa min yadda Hajiya ta ƙagauta na haihu, take nuna tana son cikin, har ma ya taɓa ce min idan na haifi wannan a haihuwa ta biyu tun yana jariri za a ba ta ta shayar da shi ya zama nata, ai kuwa nan take na ce ba zan bayar ba, da ya tambayi ba'asi na ce kawai ba zan iya kyautar ɗa ba ne, ban faɗa masa na san ba za ta so ɗan ba, tun da mata masu kissa irin matar nan idan ka fiya nunawa miji ga halinsu gani yake yi kawai kai ne ba ka son zaman lafiya ba su ba.

Haka na yi ta rainon cikina har zuwa lokacin da ya girma, hidimar sarki ta ƙara linkuwa a gare ni, indai muna zaune to ya ta matsa min ƙafafuna kenan, da na motsa sai ya yi min sannu, a wannan rainon cikin ne na daina yaudarar kaina, na yarda da gaske Isma'il ya samo wannan mukullin kuma tuni ya daɗe a zuciyata, wallahi son shi na fara yi da gaske, duk da ban furta masa ba shi ma ya gane, wata irin soyayya muka fara yi mara hayaniya a nutse, kuma na ɗaura ɗamarar faranta masa iya iyawata bayan na haihuwa lafiya. Lallai mace tana da rauni, kuma kyautatawa tana kawo soyayya, yawanci matan da suke yin aure ba sa son miji kuma su dawwama da wannan ƙiyayyar to idan ka bincika har da laifin mazan, yau dai ga mijina wanda nake tunanin babu abin da zai yi na so shi yanzu ya yi kane-kane a zuciyata.

A kwana a tashi har lokacin haihuwa ya yi, naƙuda ta kama ni watarana, da safe ne ya tafi wajen aiki, misalin ƙarfe goma, mahaifiyarsa ta faɗa min idan na fara naƙuda ita zan faɗawa ba shi ba, saboda ba ta so ya rikice sosai, ai kuwa na kira ta na sanar mata, ta zo da motar gidansu muka tafi asibiti, duk yadda aka so ɓoye masa sai da ya gane, tun da idan yana wajen aiki kafin ya dawo yana kirana a ƙalla sau biyar, tun da aka ce masa zan iya haihuwa a cikin satin, zai ta tambayata ƙalau nake? Ba na jin ciwon komai? To yau kuma da ya kira sai ya ji ƙanwarsa ta ɗaga, ko ta ce ina bacci ko ta ce ina wanka, har la'asar bai same Ni a waya ba, don haka ya zargi ba ƙalau ba, ya taho gida, yana zuwa kuwa Hajiya ta ce ba ta san ma na fita ba, ya tafi gidansu, a can ya ji muna asibiti, dayake ya san asibitin da nake yin awo sai ya tafi kai tsaye, yana zuwa ina haihuwa, ɗana namiji sankacece, don sai da aka yi min ƙari, Isma'il ya dinga murna kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, da za a yi min ɗinki na ce a ɗinke ni tsaf, dama ina son gyara jikina, tun da yanzu na yarda Ustaz bai kashe ni ba, don sosai nake jin daɗin wannan mu'malar.

Na kwana a asibiti tare da ƙanwarsa bazawara, washegari aka sallame ni muka koma gida cike da farinciki, Mama ta roƙi na dawo gida a yi min wanka, Isma'il ya cire kunya ya ce a yi haƙuri na zauna a ɗakina za a kula da ni kamar ina gidan, Mama ta turo wata 'yar'uwarmu dattijuwa, ita ce take yi min wanka da jaririn da ya ci sunan mahaifin shi Sa'eed, ya ce Baffa za a dinga ce masa, kamar yadda suke faɗawa mahaifin nasu.

Ranar da muka dawo Hajiya ta shigo barka fuska cike da yaƙe, ni ce nake gane yaƙe take yi, amma sauran mutane murmushi suke gani, ta zauna a falona ana ta barka da ita, kuma haka kullum take zuwa ta ɗauki ɗan a yi ta fira da ita, sai da ta fara karɓar gashin cibiyarsa ne na ce da me yi mana wankan kar ta sake ba ta ba na so, amma hakan bai saka ta yi zuciya ba.

Idan muna zaune da Isma'il ya yi ta faÉ—a min yadda yake jin tausayinta kenan, ni kuwa hakan bai sa na ji wai zan iya haihuwa na bar mata É—an ba.

Daga kowanne ɓangaren Daddy ya ga gata, kayan barka daga gidansu akwati biyu da nawa da nashi, haka daga gidanmu ma aka ka yi kaya daidai ƙarfinmu, ban da wanda Islma'il ɗin ya ƙaro masa, babu abin da yaron nan ya nema ya rasa.

Ana jibi suna sai na wayi gari da alert ɗin kuɗi dubu ɗari uku, wannan karon ba ta POS ma ya tura min ba, da sunan shi ɓaro-ɓaro, tare da gajeren saƙon cewa"Sayyada ina ya garin? Ina yi miki barka Allah Ya raya shi bisa sunna, ga kuɗin gidanki nan".

Na sauke numfashi ina ayyana idan an gama taron suna zan mayar masa da kuɗinsa, domin na daina son duk wani abu da ya dangance shi, ba zai yaudare ni da kuɗin haya ba, ya guje ni a lokacin da nake buƙatar shi, yanzu kuwa Allah Ya azurta ni da mijin da zai iya ba ni wannan kuɗin, to me zan yi da na shi? Dama gidan ban yarda ya ba ni shi ba, idan ma da gaske yake na fasa karɓa ya riƙe abun shi.

Sai dai kash! Ƙaddara ta riga fata, ana gobe suna an yi min ƙunshi ina zaune sai ga Isma'il ya shigo, hakan ya sa mutanen falon suka watse, zaman shi ke da wuya kiran Sadam ya faɗo wayata, ya ɗauka ya miƙo min, da yake babu saving a lambar, kuma ma ba asalin lambar shi ba ne, tun da na saka shi a blacklist, sai na ce masa ya ɗaga ya saka min a hands free, ya bi umarnina, sallama ta bayyana cikin wayar da muryar Saddam, gabana ya faɗi, yayinda shi kuma ya cewa"Hello Sayyadata, ko har yanzu ba ki huce ba? Ai kya amsawa min tun da barka zan yi miki ko?"
Chapter 75 · 0% Book details