Sashe 17
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban amsa ba, ban ma kalle shi ba, ya ce"In sha Allah daga yanzu ba zan sake takura miki ba, amma ba zan sake ki ba, sai dai kuma ba za ki sake fita daga cikin gidan nan ba har sai na gamsu da yadda kika karɓi zaman aurenmu, komai kike so ki faɗa min zan kawo miki, sabga kuma idan ta tashi ki dinga Allah Ya sanya alkhairi a waya, ba zan gajiya wajen yi miki addu'ar nema miki shiriyar Allah ba, sannan zan fara yi miki ta gujewa fushin Allah, ni mijinki na yafe miki".
Daga haka ya tashi ya fita daga gidan, ina nan zaune a falon ya dawo can bayan sallar isha'i, ya wuce ni yana waya ya shiga ɗakinsa ya rufe, har sha ɗaya ina nan a zaune, bacci da yunwa sun addabe ni, haka dai na buɗe kular na ga faten doya ne da kifi, na tashi na je kitchen na ɗakko faranti na zuba na ci, ni ce har da ƙari, kamar na manta daga hannun kishiya ya fito, na shiga ɗakina na yi wanka na canza kaya ka kwanta, nan take bacci ya yi gaba da ni.
Washegari ya dafa shayi ya karya, ya yi tafiyarsa aiki, ni ma guntun shayi da biredin na ci, wajen sha biyu ya aiko da cefane mai yawa, a raina na ayyana wato dai shi ya dage ni da shi zama daram ko? Na yi girki iya cikina, na ci, na kai wanda zan ci da daddare É—akina, na wanke komai kamar ban yi ba, don ba na so ya san na yi É—in, so nake ya gane da gaske ba na zaman auren nan, ko zai sake ni na huta.
Bai dawo ba sai bayan sallar isha'i, ina É—akina ya turo ya shigo, ya ce"Sayyada na ki yi girki ba ne?"
Na ce"Ban yi ba, ai ni da girki a gidan na. Har abada!".
Ya ce"To Allah Ya raba ki da cutar yunwa".
Ya fita, ina jin sanda ya fice da mota daga gidan, ya dawo ya shigo ya ajiye min takeaway na ƙi kula shi, a nan ya zauna ya ci na shi, ya sha ruwa, sai na ga yana rage kayan jikinsa, ya gama ya hau gadon, da sauri na tashi zaune ina cewa"Ka fitar min daga ɗaki".
Ya ce"Ba zan samu hakkina ba? Gobe fa zan bar gidanki, wai kar na barki da kewata".
Na ce"Allah Ya kiyaye, wacce ta damu da kai ita ce za ta yi kewarka, har abada ba zan sake baka haÉ—in kai, sai dai idan fyaÉ—en da ka saba za ka yi".
Ya sauka gadon ya ce"Ai na daina yi miki har abada, sai da safe".
Ya fice daga É—akin.
Washegari duk da yana É—akin Safna sai da ya zo gidana da safe, ganina kawai ya yi bai ce komai ba ya tafi, washegari ma haka. Ranar dawo É—akina ma haka ba ya shiga harkata, kuma ranar da zai bar É—akina ya sake zuwa ya ce zan ba shi hakkinsa? Na ce a'a, sai ya ce Shikenan duk ranar da na ji ina bukatarsa na sanar da shi, shi dai ba zai sake nema na ba, daga ranar kuwa bai sake nema na ba, har tsawon wata É—aya haka muke zaman kowa ya yi ta kansa, ya riga ya saba ba na ba shi abinci, iya cikina nake girkawa.
Wata ranar Lahadi da ba zan taɓa mantawa da ita ba, ranar ba ma ni ce da kwana ba, a gidan Safna yake, ina ta bacci wajen sha biyu, na ji shigowar mutum ɗakina, ya kunna hasken ɗakin, Sadam ne tsaye daga shi sai ɗan wando, ya yi min murmushi, na ɓata rai, ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon ya ce"Yau fa Safna ba ta nan, aikin kwana take yi, kuma dama tana period, ni kuma na kasa jurewa, shi ne ta ce ta amince na zo gare ki".
A harzuƙe na ce"Ni ban amince ba, kenan ma ba ka faɗa mata na bar mata kai ba har abada?"
Ya ce"Don Allah Sayyada mene ne matsalarki? Kin san fa ba daidai kike aikatawa ba, ya kamata a ce zuwa yanzu mun wuce wajen".
Na yi banza da shi.
Ya ce"To ya za ki yi da ni yanzu? Za ki ba ni ne?"
Na ce"Ka ƙwata mana! Ko dama da ka ce ka daina yi min fyaɗe kana zaton na yarda ne?"
Ya ce"Yanzu idan za a ba ki zaɓi za ki zaɓi na je wata a titi ta ba ni?"
Na ce"Ai dama ka saba!"
Ya ce"Na yafe miki duka ƙazafin da kike yi min".
Ya janyo ni jikinsa, duk duka da yaƙushin da nake yi masa bai rabu da ni ba, sai da ya cim ma muradinsa, zuciyata ta dinga zafi, ya shiga ya yi wanka a banɗakina, ya kwanta bacci ya kwashe shi.
Na tashi zaune ina fashewa da kuka, kallonsa da nake yi ne ya dinga ta'azzara ƙiyayyarsa a zuciyata, shikenan haka zan cigaba da rayuwa cikin rashin 'yanci? Sam ban san inda na dosa ba fa, ba zai yiwu ba, Saddam ya yi kaɗan na kashe rayuwata saboda shi. Ina wanka ina kuka, na gama na saka doguwar rigar atamfa, na haɗa kaya a jaka, na fice daga ɗakin, ga mamakina ƙofar dai a kulle take ta ciki, na shiga ƙwanƙwasawa mai gadi, ya buɗe ya fito daga ɗakin nasa, na durƙushe a ƙasa ina kuka na ce"Baba indai kai uba ne ka yi tunanin yadda za ka ji idan 'yarka ta kasance a halin da nake ciki, don girman Allah ka buɗe min ƙofar nan na tafi gidanmu don Allah".
Baba ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ki yi haƙuri 'yata, komai ya yi zafi maganinsa Allah, ki yi ta faɗawa Allah, idan yana cutarki shi zai yi miki kyakkyawar sakayya, ba zan iya buɗe miki ƙofar nan ba, amma na lura kina cikin tsanani, yanzu dare ne, gobe da safe na yi miki alƙawarin zan buɗe miki ki tafi 'yata".
Na ce"Don Allah Baba ka buÉ—e min yanzu, zan iya mutuwa idan na kwana a gidan nan".
Ya ce"Ki yi haƙuri, yadda ba zan iya bari 'yar da na haifa ta fita daga gidan cikin daren nan ba, haka ke ma ba zan bar ki ba, da yau da gobe duk ɗaya ne, awa ne ma ya rage mu ga wayewar garin? Ki yi haƙuri kin ji? Ki je ki ɗaura alwala ki yi sallah, Allah zai kawo miki sassauci".
Na gyaɗa masa kai, na ja jakar kayana na koma ciki, amma sai dai kash, ƙaddara ta riga fata, inda na yarda na ɗauki shawarar Baba mai gadi ƙila da abubuwa da yawa ba su faru ba cikin rayuwata, cikin ɗakin na koma na zauna a falo na fashe da kuka sosai, zuciya ta dinga yi mini ayyane-ayyane, a haka ne ta ayyana min me zai hana na kashe Sadam? Ai dai ba wanda zai min tilas ɗin zama da gawa ko? Ba tare da tsayawa tantance shawarar zuciyata ba, na yi kitchen na ɗakko wuƙa na tafi ɗakin nawa.
Yana kwance ya baje sai sharar bacci yake yi hankali kwance, na tsaya ina kallon shi da wuƙar riƙe a hannuna, wallahi na kasa tuna kyautatawa ko guda ɗaya da ya yi min, sai tarin ƙuntatawa da cutarwa ne suke ta zuwa kaina, zuciyata tana ta faɗa min shi ne matsalata, kuma ina da maganin matsalar, na kashe shi kawai na huta.
Duk taku ɗaya da nake yi na matsawa kusa da shi, ƙara bugun zuciyata ake yi, gabana sai faɗuwa yake, haka har ya zamana na matsa dab da shi, babu wani sauran taku, na ɗaga wuƙar cike da zugar zuciya da ta shaiɗan, sai dai na kasa daɓa masa ita a ciki kamar yadda na san zan fi kashe shi cikin sauƙi, sai kuma na sauke, sai da na ɗaga wuƙar sau biyu ina fasawa, a na uku da na ɗaga na daddage na caka masa a santaleliyar cinyarsa, na finciko ta da sauri, ya zabura ya saki wani gigitaccen ƙara sannan ya fara salati, tuni jini ya fara malala a gadon, na sake ɗagawa kamar zan caka masa na ce"Sadam za ka sake ni ko sai na kashe ka?"
Zare ido yake cikin azabar ciwo da mamaki, ya ce"Sayyada? Kashe ni za ki yi?"
Na ce"Za ka sake ni ko na ƙarasa ka?"
Yana fizgar numfashi ya ce"Na...na...na sake ki, Na sake ki Sayyada". Ya fara kwarara ihu yana riƙe ƙafar.
Jikina ya hau rawa, na fita da gudu ina ƙwalla kiran mai gadi, "Baba! Baba ka zo ka taimake ni, zai mutu".
Ya fito da sauri, ya yi cikin gidan ni kuwa cikin farincin yau gidan a buɗe yake na buɗe na fice da gudu, ina ta haki, na yi nisa da gidan rigata ta harɗe ni na faɗi, daidai lokacin kuma na ji marata ta murɗa, na saki kukan azaba da nadama, da ƙyar na tashi ina jin ruwa mai yauƙi yana bin ƙafata amma ban fasa sauri ba, don na kasa yin gudu.
Yau dai Sadam ya sake ni, amma tun a ranar na kasa jin farincikin da na yi tsammani, a tunanina rabuwa da Sadam ita ce hanyar buɗe shafin farincikina, ashe shafin ƙunci ne zai buɗe min, ku biyo ni don jin yadda rayuwata ta kasance.
LAST FREE PAGES! DAGA WANNAN SHAFIN FREE PAGES SUN ƘARE, LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN 700, IDAN YA ZAMA COMPLETE 1K NE
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
[04/10, 8:26 am] Sadiya Abdulrazak: 12
Na yi tafiya mai nisa, na ji ciwon ya turnuƙe ni, na nemi waje gefen titi na zauna ina riƙe marata ina ta kuka, kalmar Na sake ki Sayyada ce take amsa kuwwa a kunnena, na fashe da kuka sosai ina cewa"Allah na tuba, ba ni da wani zaɓi ne da ya wuce wannan, Allah ka sani wannan bawa naka Sadam ya fi tsohon maye naci, Allah ka yafe min".
Ina nan zaune a wajen cikin wani hali, sai ga 'yan bijilanti suna zagaye, suka haske ni da fitila, na kare fuskata ina cigaba da kuka.