Sashe 22
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ce"Ƙaddara ce wallahi, kuma na yi nadama, ko da wasa ba zan sake gwada aikatawa ba".
Ya ce"Ki yi haƙuri Sayyada, mahaifiyata ce ta yi mini umarnin na fasa aurenki, kuma ba na jayayya da maganarta, ta ce har gida aka je aka faɗa mata, don haka ko da zarginki ake yi ba ki aikata ba sai na fasa auren, ballantana ma ga shi kin tabbatar min ba zargi ba ne".
Na fara kuka mara sauti, na ce"Don Allah ka yi mini adalci, wallahi tsautsayi ne, mu je na roƙi Umman, don Allah kar ka fasa aurena ka tona min asiri, yanzu ido da hankali zai dawo kaina a fara tunanin mene ne dalilin da yasa ake fasa aurena".
Ya ce"To a shawarce kawai duk wanda ya zo miki da batun aure ki dinga faÉ—a masa tun kafin tafiya ta yi nisa, idan ya ji zai iya shikenan, idan ba zai iya ba kin ga sai ya tafi tun ba a gane ki da shi ba".
Na ce"Kenan ni da kaina zan dinga yamaÉ—iÉ—i da labarina? Ba zan iya haka ba".
Ya ce"To Allah Ya kyauta, sai ki sanarwa da iyayenki zuwa wani satin su dawo min da kuɗin aurena tun da ban sani ba ko an taɓa shi, na bar ki lafiya".
Ya wuce ya bar ni tsaye da ƙunar rai, sai na ji kamar na ɗora hannu a ka na rushe da kuka, ya ce har gida aka je aka faɗawa babarsa, hakan yana nufin mace ce ta je ta kai zancen kenan? Idan har haka ne to kuwa tabbas Anisa ce, nan take na ƙara jin tsanarta ta linku a zuciyata.
A ranar birkicewa na yi, na dinga kuka mai sauti kamar mai aljanu, don Baba tofa min addu'a ya dinga yi, yadda na ga rana haka na ga dare, sassafe ko karyawa ban yi ba na tafi gidanmu, durƙusawa na yi a ƙofar ɗakin Baba ina ta kuka sosai, duk yadda Mama ta yi da ni na tashi ƙi na yi, har dai kukan ya ishi Baba, ya fito fuskarsa a haɗe ya ce"Ke uban wa kika zo kika saka a gaba da kuka haka?"
Cikin kuka na ce"Baba shi ma ya fasa".
Ya ce"Idan ya fasa sai me? Laifin wa? Dama duk me hankali ai dole ya ji shakkun aurenki".
Na ce"Don Allah Baba ka yafe min, ƙila hakan zai saka na samu sassaucin wannan abu da yake bibiyata".
Ya yi tsaki ya koma ɗaki, na ƙi tashi daga wajen, sai da ya na kusa awa ɗaya a wajen, sannan da ƙyar Mama ta zo ta ja ni zuwa ɗaki, duk yadda ta so na ci abinci na kasa ci.
Baba sammakon zuwa kasuwa ya yi niyya yau É—in, amma sai ya kasa, yau dai ya ji tausayin Sayyada, ya gane da gaske ta yi nadama, amma ba zai nuna mata ya yafe mata ba har sai wani lokaci, a fili ya furta"Astagfirullah, Allah na tuba Ka yafe ni, idan saboda fushina dake kan Sayyada ne ta kasa auruwa Allah ka shaida na yafewa É—iyata Sayyada, Allah ka shiga lamarinta ka ba ta miji na gari".
Tun daga wannan ranar na sake zama silent, na daina kula samarin da a kullum dai wani ya doko na sallama, na yi alƙawarin ba zan sake saka wani a raina ba, ya zo ya azabtar da ni ya ce ya fasa daga ƙarshe, sai na kama sallaya, Qur'ani da kuma carbi suka zama abokan rayuwata, da dare na yi sallah, da rana na yi karatun Qur'ani da istigfari, cikin lokaci ƙanƙani na fara jin sanyi a zuciyata, ga kuma nutsuwar gangan jiki.
Wata É—aya da faruwar haka, wataranar Juma'a ina gidanmu a kwance ina istigfari sai ga Baba ya dawo daga masallaci, na yi mamakin jin yana tambayar Mama dake tsakar gida ni, ya ce"Ina Sayyada, ta zo?"
Mama ta ce"Ta zo, tana ciki ina ga bacci take".
Na taso da sauri na fito ina cewa"Mama idona biyu".
Baba ya ce"To ma sha Allah!"
Ya zauna a tabarmar da Mama ke zaune ni kuma na tsugunna daga gefe, ya ce"Sayyada a yau na yanke wani hukunci a kanki ba tare da saninki ba, sai dai ban sani ba ko za ki amince da hukuncina?"
Gabana ya faÉ—i rass, na ce"Baba kana da cikakken iko da ni, na amince ko ma mene ne".
Ya fito da kuɗi daga aljihunsa, sannan ya ciro wata leda, ya miƙo min kuɗin ya ce"Ƙirga su, dubu ɗari ne".
Na karɓa hannuna sai rawa yake na fara kirgawa, ban yi nisa ba na ce"Baba ba sai na ƙirga ba, tun da ka ce ɗari ne haka ɗin ne".
Ya turawa Mama ledar ya ce"Wannan goro ne da alawa a ciki, a yau na aurawa wani bayan Allah Sayyada, wanda na yaba da halinsa, kuma na faɗa masa tabon da yake bibiyarta, amma ya ce ya ji ya gani, sai ku yi haƙuri idan na yi muku laifi ke da ita bakiɗaya".
Tun da ya ce ya aura min wani na ji kamar zuciyata ta tsinke, fargaba ta shige ni, na fara tunanin shin wane ne wannan da ya ce ya ji ya gani tun bai gan ni ba? Wane ne wannan da Baba ya yaba da shi ya ga dacewar aura mini shi ba tare da amincewata ba?"
Mama ta ce"Ikon Allah, amma wane ne shi?"
Baba ya ce"Zai fi kyau ki sakawa abun albarka kawai kamar yadda na saka, tun da aka yi auren ai dole za ki san wane ne shi, anjima zai zo ya gaishe ki, kuma su gana da ita Sayyadar".
Ya kalle ni ya ce"Sayyada kin karɓi auren nan ko na warware shi?"
Na sunkuyar da kai na ce"Baba na karɓi zaɓinka da godiya mai tarin yawa, kuma in sha Allah zan yi masa biyayya iya ƙarfina".
Baba Ya ce"Idan kika yi haka ni kuma na yafe miki, Allah ka shaida indai Sayyada ta zauna ta da mijinta lafiya ta zama mai biyayya a gare shi na yafe mata duniya da lahira, kuma zan dawwama ina yi mata addu'ar gamawa lafiya da nema mata yafirka, idan ta bijirewa mijinta Allah ka shaida na..."
Da sauri na ce"A'a Baba, don Allah kar ka ƙarasa, wallahi na yi alƙarin zan so shi zan yi masa biyayya, ko kuturu ne, ko da bai zo a jinsin ɗan'adam ba na karɓi aurensa, kuma zan zauna da shi lafiya, in sha Allah Baba za ka gamsu da zaman mu, har ka furta ka yafe min".
Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To Alhamdulillah! Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi, kuma mijinki yana sonki, ina kyautata zaton zai yi miki adalci a zamanku har ma ki fara son shi, Allah Ya yi miki albarka".
Daga haka ya tashi ya shiga ɗaki, Mama ta bi shi da abinci, ni kuma na shiga ɗaki, na hau gado na fara kuka mara sauti, ko waye wanda Baba ya aura min? Ko zan so shi? Na dai yi alƙawarin zama da shi a duk yadda yake, kuma zan yi masa biyayya da dukkannin zuciyata, sai na ji na ƙagauta daren ya yi ya zo na gan shi.
Ana idar da sallar isha'i Baba ya shigo yana ƙwala min kira, na fito, ya ce"Maza kintsa ɗakinku ga mijinki nan zai shigo ku gana, don Allah kar ki ba ni kunya, yana matuƙar ganin girmana".
Na ce"In sha Allah Baba ka daina kuka da ni, ba zan ba ka kunya ba, kuma ya shigo kawai É—aki a gyare yake".
Baba Ya ce"Ma sha Allah".
Na faɗawa Mama, ta miƙo min babbar sallaya ta ce na je na shimfiɗa masa, na saka hijjabi, na ɗauki sallar na shiga ɗakin na shimfiɗa ta na nemi waje na zauna a takure gabana sai faɗuwa yake yi, ina jiran ganin wane ne mijina?
Wata zazzaƙar murya na jiyo tana sallama a tsakar gidan, irin ta cikakkun 'yan ahalus sunna, na zaro ido a raina ina cewa wannan na samu kenan?
Ina ji suka gama gaisawa da Mama ta faɗa masa ya shiga ɗakin can, wato inda nake, na sunkuyar da kai sanda ya yi sallama a ƙofar dakin, na amsa ba tare da na ɗago ba, ya shigo ya zauna yana cewa"Ma sha Allah, Alhamdulillah".
Fargabar É—agowa na kalle shi ma na dinga yi, da muryarsa mai kama da ta iyayi ya ce"Assalamu alaiki Ya Sayyada".
Na ce"Amin wa'alakassalam, ina wuni?"
Ya ce"Lafiya Alhamdulillah, Ya Sayyada yana da kyau ki É—ago ki kalli mijinki, ni ma kuma na kalli matata".
Na tsinci kaina da bin umarninsa, na ɗago na kalle shi, sai na ga mutum sanye da jallabiya da hirami, duk da a zaune yake amma na gane yana da tsayi sosai, sannan ba shi da ƙiba siriri ne, fari ne, amma ba kyakkyawa ba, yana ta sakar min murmushi ya ce"Yana da fa'ida ki kalle ni da kyau, kamar yadda ni ma zan so a ce kin cire hijjabin nan, domin na samu damar kallonki da kyau ya ke Assayada".
Gabana ya faÉ—i da jin wai na cire hijjabi, na kau da kai daga kallonsa,ba tare da na cire hijjabin ba.
Ya ce"La ba'asa, to Assayada kamar yadda na san mahaifinki ya sanar da ke, ni ma zan sake sanar da ke, ni ce wanda aka É—aura mana aure a yau, hakan yana nufin a yanzu dai ni ne mijinki bi ma'ana mun zama mallakin juna, Alhamdulillah ina farin ciki da hakan, kuma ina tafa ke ma haka".
Na ce"Ina farinciki, Allah Ya ba mu zaman lafiya".
Ya ce"Alhamdulillah! Baba ya faÉ—a min komai game da ke, ni ma kuma akwai abubuwan da ya kamata ki sani game da ni".
Ya ɗan yi shiru kafin ya ce"Wato Assayada ni ba cikakken saurayi ba ne, na taɓa yin aure, sai dai watanni uku da auren aka samu matsala ɗalaƙi ya shigo cikin lamarin, bi ma'ana muka rabu da juna, daga nan ban sake aure ba sai kuma yanzu da Allah Ya ƙaddara ke ce matata, Alhamdulillah ina farinciki da hakan".